ƘARA'IN INNA DELU

53 1 0
                                    

https://chat.whatsapp.com/C7Bm5rzpp10K96WEUGHPE0

ƘARA'IN INNA DELU
           💄💄💄💄
        
                   NA

          MAMAN AFRAH

FCW💛

PROMO! PROMO! PROMO💃💃💃

  *ƳAR ZAMAN WANKA COMPLETE  500 NE DAGA YAU 6/9/2023 ZUWA 10/9/2023 ZA KU SAME SHI A KAN 300 MAZA HANZARTA KAR A YI BA KE NISHAƊI ZALLAH😂😂😂*
*IDAN 10 GA WATAN YA WUCE ZAI KOMA YADDA YAKE 500*
 
   MAI ZAMAN WANKA TA TAFI MAI ƘARA'I TA ZO
😂😂😂😂😂

_Wannan shafin sadaukarwa ne ga masoyan littafin ƘARA'IN INNA DELU a duk inda suke ina matuƙar ƙaunarku tare da jin daɗin yadda kuke nuna mini ƙauna_ 😍😍😍😍

             Page 1⃣3⃣➡1⃣4⃣

      Da yake ba wani tsaro aka saka a wurin ba duk mutanen gari sun shigo kallo musamman samari, yadda wurin ya tsaru kowa ya ɗauka zai ga amarya budurwa ango saurayi amma suna fitowa aka fara tozali da wata uwar furfura da ta yiwa Jauro ƙawanya a fuska ga wani aski da aka masa na zamani aka aske wani wurin wani wurin aka bar masa gashi sai ya zama kamar irin fataken nan wanda suka daɗe suna yawo basu samu gari a kusa ba. Inna na fitowa daga motar da yake rigar tata doguwa ce ta mata yawa ko ƙafar baka hangowa da takalminta mai tudu gashi kuma yadin satin ne aka yi ɗinkin da shi sai aka ɗora net aka sosai rigar  ta mata yawa, tana fitowa kowa ya saki baki yana kallonsu banda ƴan ƙauyensu da dama sun san su waye amarya da angon.

   Shattu ce riƙe da wani bokiti da aka zuba ganyen maina irin wanda ya yi yellow ɗin nan tana watsa musu a matsayin furanni dan Inna ta ce babu wani abu da ba za a musu ba sai dai ko idan mantawa suka yi da shi.

  Tana watsa musu tana carara guda duk da mc ya ƙure kiɗa baka jin komai amma bata daina guɗar ba, Jauro ne ya riƙe hannunta irin yadda amarya da ango suke yi, matakala ce a wurin suna zuwa sun hau ɗaya biyu suna shirin hawa ta ukun rigar Inna ta taɗe ta aikuwa ta zame ta tafi za ta faɗi, da sauri Jauro ya tareta ashe shi ma rigar ta maƙalo da ƙafarsa aikuwa suka tafi a tare suka tiƙu da ƙasa ji kake tim sun faɗi ai gabaɗaya samarin nan da suka ziyarci wurin ba gayyata suka ɗauki wani uban ihu kamar an ci ball a gidan kallon ƙwallo. Gabaɗaya wurin ya kaure da ihu wasu har fito suke, da yake da suka faɗin Jauro ne a ƙasa ita kuma sai ta faɗa da rubda ciki a kansa, duk sai kunya ta rufe su, Shattu bokitin ganyen mainar da take watsawa a matsayin furanni ta ajiye tana sakin wani salati ta nufe su cikin azama tana faɗin.

"Ya subhanallahi, amarya da ango an sha ƙasa, yo dama ku da za ku shigo cikin mutane ai bakwa fito ba tare da kun sha lahaula ba,  ko maganin baki saboda kallo, yadda kuka yi kyan nan ai sai ido ya kama ku kar fa ku manta duk taron nan saboda ku aka yi kuma kowa ƙoƙarinsa ya ganku wasu har ɗaɗɗage suke dan su hangi amarya da ango" Ta faɗa tana ƙarasawa wurinsu ta ce

"Sannu Delu sannu Jauro ai sai ku tashi ku karkaɗe jikinku domin ƙasa ba sirikar kowa bace da za ku ji kunyarta"Cewar Shattu tana miƙa hannu za ta ɗaga Delu dan yanzu ta gangara ƙasa daga kan Jauron, gashi taƙi tashi sai Shattun ta ce

"Ki tashi mana ku ƙarasa kan kujerunku na amare"

"Haba Shattu kin ji ƙirjina kuwa...

"Wane irin na ji ƙirjinki kuwa ke da kika faɗi ai ke za ki ji a jikinki dama" Shattu ta faɗa rai ɓace dan ta fi so Innar ta tashi saboda yadda idanu suka musu caaa

"Haba ina dalili dama ai laifin Lantana ne da bata saka an rage mini tsawon rigar nan ba ta barni ina yawo a ciki zulum-zulum kamar limamin masallacin juma'a zai yi kuɗuba...

"Wai Delu ki tashi mana banda ma ɗan adam ke da Allah ya taimake ki kika faɗa a kan Jauro da kan dakalin nan kika faɗa ai da kin ji a jikin ki" Cewar Shattu tana kama tsantsa ganin Delu ta ƙi tashi.

ƘARA'IN INNA DELUWhere stories live. Discover now