JADWA 36

123 12 0
                                        

Suna isa ningi suka kama kuka kamar ran zai fita, parking yayi kofar gidan yace ku fitowa saboda yaga babu alamun fitar su.. sauka suka yi suka fita Fatima ce ta fara shiga gidan yanayin da ta ga umman ta fadi sai kuka don umma an daure ta da hannu da ƙafafu, mama ta fito tana fadin lafiya zaki shigo gida da ihu? Fatima tace haba mama sai kin tambaye ni lafiya wannan halin da umma take cikin ya dole nayi ihu, tace toh shi ihun me zai kara mana ? Lokacin har A'isha ta shigo tana zubar da hawaye wani na bin wani.

Mama sai hakuri take ba su duk ta rude ta ma rasa ta ina zata fara ga jikin tsufa.

Haka suka wuni ko cin abinci basu ci ba sai A'isha da ta kira wani sugar daddyn ta, tana fada mashi abunda ke faruwa dasu hakuri ya bata yace zai kira amma shiru bai kira ta ba har dare. Haka suka tashi suka je suka ci abinci suka kai ma umma sai fiz fiz ke take kuka suke yi sosai abunda yafi basu mamaki wai ace radiya har yanzu baza iya kiran numbern su don taje musabaqa na Alqur'ani gashi suna kiran numbern ta baya zuwa.

Haka rayuwa ta cigaba tana tafiya duk sunyi baki sun lalace umma ta rame sosai abun tausayi mutane sai zuwa kallon ta suke yi, mama tayi dasu su koma school amma suki duk samarin su sun juya masu baya abun na daure masu kai suna fadi a ransu ko dai ansa masu hannu ne lokaci daya abubuwa zai rikici masu haka.

A bangaren su jadwa da Dr fahad shirye shirye yayi nisa sosai ana ta shirin biki duk da irin kudin amma ba suyi wani shiri bidi'a ba don Dr fahad baya so ita kanta amaryan jadwa bata so duk ustazai ne..

Waliman da za'ayi Abba ne yace zai yi a ranar da aka daura aure, su kuma amarya da ango suka ce sai Abuja bayan sun tare zai gayyato abokanan arziki da aikin sa aci a sha ayi masu addu'a.

Yau Sunday radiya suka kammala musabaqar su tayi nasara sosai don ita ce tazo ta biyu a garin bauchi anan wani ya bata kyauta mota corolla LE bayan kuɗaɗen da ta samu koda malamin su ya bata wayan ta da rawar jiki ta karba don dama ta matsu ta kira gida kwanan nan duk hankali na gida..

Tama rasa wa zata fara kira, tunani take yi sai ta duba numbern jadwa ta kira bata dauka ba sai ta kira Abba shima kamar baza a dauka ba sai da kira ya kusa kai karshe sai ya dauka sallama yayi ta amsa tana dauƙin magana da shi yace yan musabaqa Masha Allahu diya naji labarin nasarar ki Alhamdulillah ina alfahari da ke radiya yau sai gida ko? Tace Alhamdulillah Abba Nagode da kokari hakika bani da abun da zan saka maka dashi sai dai na tayi maka addu'a Allah ya baka Aljanna ya kare da sharrin makiya yace "Ameen" yasu umma na kira jadwa bata dauka ba ? Nan ya rasa ma me zai ce mata can tace Abba kana jina na yace Eh suna lafiya, tare da mallaman ku zaku dawo ? Tace "Eh Abba muna ta shiri ma yanzu za mu taso" yace toh Allah ya dawo daku lafiya. Ameen ta fadi kai tsaye suka yi sallama ta kashe waya. Yana aje wayan ya kama tunanin toh yanzu idan yarinyar nan ta dawo me za'a fada mata lallai yasan idan har aka fada mata wannan labarin ba zai mata dadi amma shi kam zai cigaba da rikon ta har ya mata aure kamar yadda ya fada da wannan tunanin ya wuce dakin hidaya yace ya same ta da maganar.

Ganin kamar ya tada hankalin shi yasa ta kwantar mashi da hankali tace mashi ai In'sha'Allah radiya tunda tasan halin mahaifiyar ta ta baza tace za taki zama da mu ba Allah yasa ta samu miji mu mata aure amma ta samu uwa mai bakin halin da yan uwa ta gode tunda bata yi halin su ba kuma tana da hankali. Yace hakane Allah yasa mu dace Aameen ta fadi ta kara matsa wa kusa dashi.. ina Jadwa ? Ya tambaya yana taba wayar shi amswa tayi tace "su jadwa amarya wlh tana can gidan auntyn ta zainab ana ta shirye shirye biki". Dariya yayi yace toh MashaAllah, Allah ya kai mu lokaci dai tace "Ameen"

Parlourn yayi shiru babu mai ce ma wani ƙala can tace wai Abban jadwa kasan me nake tunani ni? Yace a'a sai kin fada. Wai yau mune zamu aurar da yar cikin mu gaskiya rayuwa yana tafiya ina kara gode ma Allah da ya bani lafiya ya fitar da Ni cikin mawuyacin halin da na shiga gashi zan ga biki yata da idona da hankali na In'sha'Allah.

Yace tsarki ya tabbata ga Allah swt lallai Allah abun godiya ne mun gode masa sosai da yasa muka yi witnessing wanna lokacin Allah ya nuna mana ranar auren lafiya tace Ameen.

Ce mata yayi bari ya fita yaje masallanci kofar gida ya gana da ma'aikatar shi ko fira suyi tace toh sai ya dawo.. ya mike ya bar parlourn.

Dr fahad da jadwa sun gama hada lefe duk abunda jadwa ta gani Instagram ko wani media da ta nuna mashi za'ayi order a kawo har a bauchi sai da sha gama sayan komai da komai ya kwashi kayan ya wuce da su adawama za'aje can da wanda Aunty zata kara a zuba a boxes a fara shirin kawo lefe..

Koda radiya ta iso gida haka aka hada mata abinci iri iri kamar wanda za tarbi bakin biyar kuma mommy tasa akayi hakan sosai radiya ta ji dadi amma abunda ya fi daga mata hankali yadda take kiran numbern umma a kashe ta kira na Fatima akashe A'ishah kuma bata dauki waya ba..

Ta kasa daure tana sauka gidan ta fara tambaye masu aiki da taci karo dasu, tace sun je ningi nan hankalin ta ya fara kwantawa da kuma ƙyayatancen abinci da mommy tasa ayi mata ya fara shagalar da ita amma ma suna ranar da, tafito daga wanka kenan ta ci karo da jadwa tace Barka da dawowa sis Ina taya ki murna duk kyaututtukan da kika samu Allah yasa suyi maki amfani Allah ya kara ma ilimin albarka tace Amin Nagode Aunty jadwa..

Shiryawa ta fara yi tana sa kaya suna yi suna fira nan jadwa ke bata labarin auren ta take ansa rana kuma nextweek zava kawo lefe sosai radiya taji dadi harda tsalle..

Sallama mommy tayi nan radiya ta tsaya cak! Tace mommyyyyyyyyyy yaushe kika da.... Sai ta kasa karasa abunda zata fada ta sheka da gudu ta rungume ta, tana murna tace aunty jadwa wanna surprise in fa mommy wlh naji dadin ganin ki haka Alhamdulillah Alhamdulillah Alhamdulillah murna radiya take yi sosai. Ita ko jadwa a ranta tana tausayin radiya idan tasan cewa umman ta ne ta koma cikin halin da mommy ta shiga da zuciyar ta ya raunana.

Duk abunda suke yi Abba yana dakin yana kallon shi, jima jikin shi yayi sanyi sosai yana tunani ta ina za'a fara fada mata kuma abunda ya zama dole a fada mata saukin abun daya ma ita kanta yarinyar tasan halin umman nata da yan uwanta.

Sallama abba yayi nan suka juyo suna kace Abba yashe kazo ? Yayi dariya yace yanzu dai su ke parlour dukkan su. Toh suka amsa suka bi bayan shi ita dai radiya dadi fal a ranta tana jin dadin yadda mommy ta samu lafiya ta dawo cikin su..

Koda suka je parlourn sun ci sun sha anyi wasa dariya can radiya tace mommy abba Ashe su umma ningi ? Ta tambaya kai tsaye can kuma tace Abba hakane koh! Uhmm umm sai yace eh hakane sai mommy tace radiya akwai maganar da zamuyi da ke yanzu, sai tayi shiru tace toh mommy Ina ji Allah yasa lafiya sai Abba yace radiya sai dai kiyi hakuri maganar da masu aiki suka fada maki na cewa umman da su Fatima sun na ningi tabbas hakane amma sai dai basu yi maku karin bayani ba lalurar ce yasa suka koma can ningi kuma sun tafi kenan don abubuwan da umman ki tayi a gidan nan suyi muni.. mikewa tsaye tayi tace innalillahi wa'inna ilaihi raju'un me umma tayi Abba ?? Sai idon ta ya can za kala, Abba yace ki zauna kiji radiya kuma bance ki tada hankalin ki sosai ba kinji...

Ma'assalama
Yours khadsss ❤️❤️
Let's meet in the next chapter
Not edited chapter, ignore mistakes plss

JADWA (Completed)Where stories live. Discover now