JADWA 41

119 11 0
                                    

Yana isa ya bude sallama tayi ya amsa yace yi hakuri yaya muna sonn ganin auntyn mune mun kosa. Yace kai!! Jidda har yanzu kinyi aure baki daina rigima ba ko? Waye yace baza ki ganta ba? Fada mun nace ba yau aka kawo ta ? Shiru tayi tana kallon jadwa daga nisa fuskar ta dai a rufe yace wai zo ku gaisa ta sauri ta shiga na sallama ita dai jadwa a hankali ta amsa ta tace Aunty jadwa barka da shigowa family inmu tace thank you sis, sai jidda tace "pls can I see your face"? Murmushi jadwa tayi sai ta bude mata fuskan sai ta rufe da sauri ita ko cewa tayi wow beautiful sis wlh ke mai kyau ce gaskiya yaya ya iya zaɓe.. Thank ta fada tana wasa da hannu ta, shiko duk abunda ake yi Dr fahad na tsaye yana kallon su abun ganin shi yake yi kamar a mafarki wlh sai hamdallah yake yi ma ubangiji..

Yana koma ya zauna kusa da su zai yi magana kenan sai ga Aunty da su radiya watau yan Bauchi kenan sun shigo dakin da sallama dr fahad ba ƙaramin kunya ya ji gaishe su yayi kanshi a kasa sai ya hawa sama binen da ke dakin. Nan aka kara yi ma amarya nasiha aka ce za'a kai ta part inta, tashi tayi radiya da jidda suka rike mata hannu guda na dama guda hagu, sai guɗa ake yi aka fita da amarya abun da ya bani mamaki ace part inta ma'ana cikin gidan kenan amma kuma sai naga manya manya motoci sun tsaya irin wanda suka dauko su daga airport nan aka bude da taimakon radiya da jidda amarya ta shiga cikin motar yan bauchi ma suka shiga motar, suna shiga ba'ayin wani tafiya mai nisa ba tunda cikin gidan ne naga an isa part in, sai gashi motar ta tsaya haka suka kara tai maka mata ta fito suka tsaya suma sayar motar duk suka fito, gida cikin gida kenan don har da gate part in jadwa yanda kuka san wani gida haka part in yake duk acikin gidan su Dr fahad kenan.

Suna fito wa Aunty tazo da ganta ta ja hannu jadwa tace jadwa Barka da iso wa ga gidan ki nan zaki zauna nan za kuyi 1 week kafin mijin ya dauke ki ku koma Abuja wajen aikin shi, kai jadwa kawai ta ɗaya sai Aunty tace toh MashaAllah. Aunty Zainab ta zo tace gidan zaki shiga ki tsaye kiyi addu'a kafin ki sa kafar ki ciki tace toh In'sha'Allah.

Sai suka ja ta sai bakin gate in Dan ko ta tsaya tayi addu'a sosai ta kai 6 minutes tana addu'a sannan tayi bismillah ta shiga suka bita baya masha Allah kowa ke fada auren shi ganin kyawon wajen portable building akayi shi ba wani mai girma sosai ba amma ya tsaru, Aunty ta ciro keys daga bag in ta ta bude parlourn wow abunda kowa ke fadi kenan yadda tsarin parlourn yake shima abun kallo ne ya manya sofa masu kyau, kowa nata fadi wuri yayi kyau Masha Allah.

Basu fi 15 minutes ba aka ce za'a wuce nan jadwa ta fara hawaye ganin kawai akayi na shassheƙa nan Aunty ta zo tana fada hakuri tace ai su radiya da jidda da sultana zasu tsaya nan su kwanta da ita gobe da safe sai su shirya tunda jirgin su 8:00am zai tashi, haka dai ta hakura Aunty zainab suna waya da mommyn jadwa sai ta ba ma jadwa wayen suna gama wayan sai ta fashe da kuka kowa yaji tausayin ta haka suka tashi suka bar part in suka koma nasu part in ma wanna time in ba motocin sun wuce har da su Aunty zainab tafiya suka yi sai bai wuce 7 minutes ba suka isa part insu

Ita ko a bangaren su jadwa kuwa taje toilet ta rage kayan jikin ta, radiya ta taimaka mata ta fita mata da wata silk material ash color da perfumes masu dadi ko da ta fita lafayar da ta fito toilet su ta sa ta mata godiya ita radiyar wanka tayi ta sa abaya jidda da sultana dai suna ta kallon su, gashin jadwa ke basu mamaki duk da suma fulani ne kuma suna da nasu gashin amma na jadwa daban ne yafi kama da na larabawa ko indiyawa cikin shawara da son juna suka taya jadwa da radiya linke kayar da suka cire suka sa a wardrobe.

Sun shirya tsaf, sai kamshi dakin ke yi nan aka kowa masu wasu kalolin abinci masu dadi da kamshi gaske, haka radiya taci kadan su jidda ma kadan suka ci amma jadwa ne ma taki ci tace bata jin yunwa da kyar da amince tace su hada mata team, Sultana ce ta je kitchen ta hada tean ta kawo mata ta karba tace ta gode.

Karfe 9pm na dare bayan sun yi shirin bacci saboda gajiyan da ke dauke da dukkan su can sai ga kiran wayan jadwa, habibinta ke kiran ta murmushi tayi ta dauka tace Salam alaikum, ya amsa yace my queen yakike ya gajiya ya kuka ? Sai tayi murmushi tace duka Ni kade? Yace eh mana nasan duk kina yin su tace hakane fa yace toh ya kika ji kan ki a sabon wuri kuma gidan mijin ki ? Tace dadin baya milsatuwa Dr sweet kamar mafarki nake yi? Yace toh ki farka idan ma mafarki ne ta ce toh sweet yace yawwa honeyy yace kince abinci tace tasha tea da yaso yayi korafi sai ya kyale don shi komai ma bai ci ba kuma baya jin yunwa lalle murna yana haka cin abinci ya fada a ran shi. Can yace  wlh my queen na matsu gobe tayi a rako ni dakin ki na karar tabbatar da cewa lallai nayi babban dace alhamdulillah. Dariya jadwa tayi tace lallai ma watau sai ma gobe zaka kara tabbatar wa? Yace ban ma san me na fada ba duk murya na ya lullube Ni. Cikin raha da wasa suka ta waya radiya tayi bacci ita da Sultana ita ko jidda abun ba ƙaramin burge ta yayi bayansa suke wayan su cikin so da kaunar juna, ana cikin haka taji zuciyar na tashi jidda tayi sauri ta tashi ta shiga toilet sai amai nan jadwa ta katse wayan suka yi sallama ta shiga toilet tana ma jidda sannu da kayar ta samu amain ya tsaya duk abincin da taci sai da ta amaye shi duka nan jadwa ke cewa ko ta sake kiran Dr ne azo a duba ta sai jidda tace karki damu kwana biyu da suka wuce na saba da hakan kuma ina shan magani toh jadwa tace mata bata kawo komai a ranta ba sai ta taimaka mata ta fito dakin daga nan ta koma kan gado ita ma jadwa ta yi shirin kwanciya ta duka su kayi addu'a suka kwanta..

Washe gari da safe alarm ya ta dasu na sallah asuba karfe 5:21am suka farka duka domin yin sallahn asuba ita ko jadwa suku suku take don da ta tuna yau family inta zasu koma bauchi sai taji babu dadi yanzu ita ce za zauna nan babu wani na ta can tayi tunani tace ko ta roki abban ta da ya bar mata radiya su tsaya tare don ita wlh ba ƙaramin kewar gida zata yi ba da wannan tunanin taji sanyi a ranta ( Ni ko a rai lallai jadwa yarinya ne har yanzu ko ta manta aure take yi yanzu, kuma ko ta manta yanzu radiya tana jinyar mahaifiyar ta can ningi ).

Ko da suka tashi suka yi sallah asuba Aunty zainab ta kira radiya a waya tace kar ta koma bacci ta fara shiri kar suyi missing Flight, jin hakan sai da gaban jadwa ya fadi tayi mirimiri da ido tana kallon radiya. Tana kashe waya ta shiga toilet zata yi wanka. Jadwa kasa komawa bacci tayi 7am nayi fit ta kira Abba a waya, Abba yana cikin masallaci yana lazumi yaji kiran waya ganin sunan jadwa yayi mamaki, sai ya dauki wayan, sallama yayi yace jadwa lafiya sai ta fashe da kuka yana zaune ya mike ya fita Masallacin ya na fadin lafiya ? SubhanAllah jadwa me ya faru lafiya ? Me aka yi maki? Duk ya rude Yana San sanin abun da ya faru da yarsa tilo guda daya. Nan ta ce mashi ita wlh baza iya zama gidan babu kowa dan ya barta da radiya su zauna tare, murmushi yayi yace jadwa kenan.. yasan halin abun shi nan ya fara bata hakuri yana lallashin ta kun ce yan shekara goma ce yake lallashi ya ce mata radiya na jinyar mahaifiyar ta amma idan ta gama ta dawo Bauchi zata rika zuwa ko da sun koma Abuja ne sannan suma za su rika zuwa ziyar ta haka yata lallashin ta yana kwantar mata da hankali har ta sake suka yi sallama yace anjima zata kira mommy yace toh. Ko da ya gama abunda yake yi ya shiga gida ya samu mommy na karatun Alqur'ani gaishe shi tayi ya amsa yana bata labari, dariya suka yi sosai shi da ita suka ai zata daina..

Koda 7:30am yayi aka zo daukan radiya aunty zainab da yan Bauchi duka don zo suka yi sallama da jadwa, nasihar da lallashin da Abba ya mata ne yasa bata yi kuka sosai ba, daga nan suka shiga motar sai airport, haka suka shiga da Aunty da jadwa da su sultana, suka ta fira sama sama ita dai jidda ba lafiya kuma su san Matsalar ta wani jika za su kara samu gidan 😂 ko da suka gama fira su ka bar ta daga ita sai jidda

Yan Bauchi sun isa gida lafiya lau alhamdulillah ita ko radiya hankali ta duk ya koma ningi cewa tayi yau zata koma anyi anyi da ita ta bari gobe tace wlh ita kam yau zata koma ningi babu yanda suka ita da ita dole Abba ya bada mota aka wuce da ita ningi..

Karfe 8pm jidda ta kira waya aka zo da mota aka dauke ta, babu jima ma shima ango ya kira amaryan shi yace ga shi nan zuwa shi da babban abokin shi sadeeq.. toh tace sai ta kama wasu tunani..

Ma'assalama ❤️🦋
Unedited chapter
Pls vote and comment
Share also, my delaying for not updating this book, so is because of you guys are not commenting.. pls do comment and like it cost you nothing to do so.. Ina so sanin yadda kuke ji idan kuna karanta book in shin yana maku dadi ?

Next chapter coming soon In'sha'Allah but a daure a yi vote da comments harda like plss Kar ku ga laifi na idan banyi updating da wuri ba laifin ku ne.. idan kunyi yadda kuke nike ko yau za ku iya kara ganin wani update In'sha'Allah

I love you all readers ❤️❤️

JADWA (Completed)Where stories live. Discover now