Tana cikin tunani kawai sai horn da ta gama ji daga waje kamar kyaftawa da bismillah.. sai ta ji gaban ta ya fadi tasan ba kowa bane illan angon na ta hmm, ta wuce bedroom ta dauko gyalen ta me shegen kyau ta yafa ta kara fesa turare duk da kayan da ke jikin ta ba karamin kyau yayi da gyalen ba, ta zo ta zauna kan sifa ta lullube fuskantar jin kara bude dadi tayi hade da sallama, gaban ta ya kara fadi daurewa tayi ta amsa cikin siririyyar murya wadda su kansu angwayen basu ji komai ba amma ita duk a tunanin ta ai sun ji, jin tayi sadeeq na cewa amarya ba kya laifi ga angon ki na kawo maki shi kyauta.. hmm kawai tace sai sadeeq yace ai namanta amarya bata magana fa sai an saye baki gashi kuma ita na kawaye anan kusa da ita anan ne ma Dr fahad ya bude baki yayi magana yace shikenan ai ba sai an saye bakin ba tunda na biya sadaki ai na saye komai..
****
Haka dai suka cigaba da dariya suna zolayar ta babu abunda tace masu sai hmm da motsi da take yi da jikin ta.. sadeeq ne yayi ma su nasiha iya nashi kuma yace shi zai tafi ya bar su lafiya Allah ya basu zaman lafiya ameen Dr fahad yace sai ya bi bayan shi bayan ya tashi ya raka shi har kofar fita parlour suka yi musabaha yayi mashi godiya ya rufe dakin ya juya ya dawo ga matar shi.Yana isa wajen ta ya mta sallama ta amsa ciki ciki sai ya bude gyalen ta "fatabarakallahu ahsanul haliqeen" kawai yake fada a fili hade da "Allahumma barik" Ameen ta fada sai yaji muryan ta ya kara zaki ta kara mashi kyau kamar wata saurayin Makkah Alhamdulillah yace Allah nagode maka da irin wannan kyakkyawan halittar da ka bani ita kyauta a matsayin kyauta.. sai tayi murmushi zauna wa yayi kusa da ita ya rike mata hannu ya mike ya da ita tsaye ya mata wani kyakkyawar hug yake wajen 5minutes bai sake ta ba sai da yaji motsin nata yayi yawa sannan ya dawo daga duniyar da ya shiga shima ma manta da duniyar da yake ita kanta jadwa ba karamin dadi taji da sanyi a lokacin da suke wannan hug in tama manta da duk wani damuwa da take ciki..
Koda ya sake ta yace mata my queen ya kamata muyi sallah mu kara gode ma Allah da ya nuna mana wannan ranar koh? Daga kai tayi yace yawwa sai ya rike mata hannu yace ko na dauke ki? Dariya tayi tace A'a Dr sweet yace yayi idan na tashi ai bazan tambaye ki ba kuma baki isa ki hanani ba sai tayi murmushi tace toh..
Janta yayi suka wuce bedroom, manyan kayan da ke jikin shi ya rage sai ya dawo gare ta ya cire gyalen yace ta zauna, taba zama ya cire mata earring da jewelry harda bangles in da ke hannu ta kare ma lallen ta kallon yayi sai ya manna mata kiss wani yarrrr taji a jikin ta sai ta lumshe ido, kallon yadda tayi sai abun ya burge shi ya rike hannu gam bai sake ba 😂 shiru yayi yawa sai ta bude idon ai ko suka hada ido sai tayi murmushi sai ta kwace hannun ta da sauri sai yayi dariya yace oyahh let's go to toilet sai ya kashe mata ido daya murmushi tayi ta mike, ta mike ya sake riƙe mata hannu suka wuce toilet alwalla suka yi shi da ita bayan sun gama suka fito shi da kanshi ya bude wardrobe ya fito mata da hijab ya mika mata sannan ya ciro prayer mat ya shimfida masu, daganan ya ja su sallah ya bayan sun idar ya jima yana masu addu'a, ya mata tambayoyin da duk ya dace ango yayi ma matar shi a daren su farko kuma ta amsa su duka babu kuskure MashaAllah yake fada don daman yasan matar tashi gwarzuwa ce ba baya ba wajen karatun addinin ta..
***
Ya mike da ita tsaye ya jata suka je kan bed suka zauna bayan su zauna ta dafa kanta ya mata addu'a sosai, sannan ya ce ta cire hijab ta cire ya je ya mayar da prayer mat da hijab in a wardrobe sannan ya mike yace ma yana zuwa zai fita waje ne tayi mamaki da taji ya ambaci waje ba ko parlour ba.. zata tambaye shi har ya wuce, sai ta koma tana tambayen kanta... Kafin duk ta gama tunani sai ga angon nata yafi shigo da sallama babban foodwarmer ne a rike a hannun shi, tana ganin shi tace muke taje taimaka mashi tace Dr sweet Ina ka fito da warmer haka ? Dariya tayi tace cikin mota na je na dauko daga waje hmm ta ce sai yace Bara naje kitchen na dauko plate tace "A'a ka bari naje" ki huta kawai abunda ya fada je nan bai jira mezata ya fita, sai gashi ya dawo da plate da folk da bottle water..Haka ya zauna kan rug carpet in da ke dakin yace bude warmer in watau musulumin pepper chicken ke ciki hade da gas meat, kamshi ya garwaye dakin ga suracin na fita daga warmer in...
Yace kinsan aikin Aunty ne nan ko? Cewa tayi babu wani kazar da zan je saya waje ita zata mana kazar daren farko 🙈😂 kulle ido tayi saboda kunya tace gaskiya Dr sweet kazan nan tayi dadi sosai yace kin ci yana kallon ta dariya tayi tace ai ko iya kamshin nan ya isa ya nuna cewa da girkin Aunty yayi dadi yace haka ne yar gidan Aunty..
Fara zuba masu yayi a cikin plate ganin sai zuba yake yi tace wallahi Dr sweet a koshe nake fa sai dai in nakai ba murmushi yayi yace toh nima a koshe nake bari na bar shi haka...
Bayan ya gama yace bismillah ya fara yagar kaza, ganin sai kallon shi yake sai ya mika mata tana ya sa cikin baki, yana sa wa babu gardama sai ta ciza yadda ta yi sai abun ya burge shi, shi komai na ta yana burge shi ne wlh, taka yata feeding inta daga karshe ne ta karba cikin kunya ta mika mashi sai yaji dadin hakan. Sun kusa gama wa tace ta koshi, shima ya koshin saboda ita ne yake kokarin ci don kar ta barshi, haka ta taya shi kwashe kayan suka dawo suka shiga toilet suka wanke baki yace suyi alwalla kwanciya bacci.
Sun dawo ta kama jin kunya yadda zata cire kaya sa sa kayan bacci ya lura da haka sai da ya bari ya gama cire kayan jikin shi daga shi sai boxer kallon daya ta mashi ganin gashin kirjin sai sai taji wani iri jikin ta bata kara kallo ba ya lura da haka sai yayi murmushi. Bude wardrobe yayi ya ciro mata kayan bacci masu kyau maroon color, rigar kara ma ce kamar vest iya cibiya sai bum short.
Kallon su tayi ta mamaki wai ita ce zata sa kayan nan ta kwana da namiji? Hmm take fada cewa yayi ko sai na sa maki ne ? Zato ido tayi tace A'a ka fita zan sa da kai na sai yayi dariya yace ba inda zan je Ni fa mijin ki ne..
Kara zaro ido tayi tace don Allah Dr sweet ka je toilet yace wlh ba inda zan je toh Ni dai mijin ki ne, tashi tayi har da buga kafa yadda tayi shagwabar sai ta kara birge shi..
Yace toh zan fita amma fa na yau ne kawai gaskiya don gobe ma ni zan sa maki sai tace toh.. sai ya fita yace parlour, 5 minutes yayi sai ya dawo cikin dakin da sallama.. tana zaune a bed ta rufe jikin ta da blanket..
Dariya yayi sosai yace amarya kenan, sai ya hau kan gado da bismillah, yaja blanket in ya shiga.. jawo ta yayi duk jikin ta yayi sanyi sai yayi hugging inta tight daganan sai ya fara romancing inta nan ta ke hankalin ta yi fita jikin ta wasu zafafan kisses ya fara zazzage mata ta wuya ta baki.. ganin haka nayi sauri na bar dakin tace sai gobe bari naje Bauchi na dauko labari ko ningi zanje ne don ganin yadda jikin umma yake ? Oho dai Allah ya kai mu gobe bari naje na huta nima mai kawo labarin sai wani jiƙon In'sha'Allah
Ma'assalama ❤️🦋
Unedited chapter, pls ignore mistakes
Love you all readers
Pls comments, vote, and share
Next chapter coming soon In'sha'Allah
YOU ARE READING
JADWA (Completed)
AventuraHe make love stories for a niqabi girl and pious heart but step mum, sisters and fake friends that back stabbed and betrayed her. After all they go like this.. Completed but editing.... Find out in the novel Note: A Hausa novel