Suna fara tsayawa parking space suka fara fitowa abun ka na manya mutane harda kuma yan siyasa. Senator Ibrahim Rashid da shi ciki a wannan tafiya, tare aka zo neman auren dan shi don yace baza'a barshi ba shi ma zai tafi, ba ƙaramin farin ciki yake yi ba saboda ɗan shi da ya dade yana burin yayi aure kuma ya samu matar auren toh ai dole yaje, ƙanin shi da abokan shi sun yi ya tsaya yace a'a suje dashi kawai... Yana farin ciki da hakan
Koda suka iso gida shima Abba ya kira manyan abokansa kuma harda yan uwan Hajiya babba da sauran yaran ta kuma sun halarci gayyatar...
Anyi masu tarɓo irin wanda ake so har cikin babban parlour aka kai su suka fara shiga da sallama.. mutanen Abba da suka gansu hakan sunyi farin ciki suka tashi suna musabawa da juna suna masu Barka da zuwa da sannu da hanya, suna dariya suna murmushi kamar ansan juna..
Suko su lantana da rabi tuni suka gama hade komai na tarbon baki aka ajiye tun kafin su zo..
Ruwan bottle abokin Abba ya fara basu wasu daga cikin sun karba wasu kuma sunyi godiya. Da ganan aka bude masu snacks in da aka masu da local one dana zamani.. Senator ibrahim Rashid shi dai sai dariya yake tayi yana fara'a don yaji dadin yadda su Abba suka tarɓe su sai Alhamdulillah ya ke ta fada...Umma kuwa koma cikin tayi kamar mahaukaciya tana ihu, so A'isha basu nan sun wuce yawon su, radiya kawai ke gida, zuwa tayi don jin abunda ya samu umma, nan umma take ce "shikenan radiya, shegiyar yarinyar zata aure mai kudi ta barku, gashi ubanta ya fara chanza hali wai me ke shirin faruwa da Ni ne"?
Abun bai ba ma radiya mamaki ba saboda ta san halin umman ta, cewa tayi "umma ai aure lokaci ne muma idan lokacin mu yayi zamuyi" tsawa ta daga mata tace uban mai ya kawo ki nan ma, shegiya mai bakin hali, da yan uwan ki nan nasan baza su fada mun irin wannan maganar mai ɗaci ba wuce ki bara kallona wawuya kawai.. wuce tayi tana mai ma umma ta addu'a a cikin zuciya akan Allah ya shirye yasa ta daina wannan halin sannan ta ci gaba da taya jadwa murna akan baiwar da Allah ya mata..Da harara ta bita, tana mata mugun baki sai waya ta je ta dauko ta fara kiran wayoyin su A'isha duka a kashe, duk ta rasa sukuni sai kira numbern tabawa bata dauka ba.. sai zufa take yi hankalin ta a tashe tace ta rasa duk inda zata sa kanta..
Su Abba kuwa sai fira ake tayi daga nan sai wakilan Senator ibrahim Rashid suka fara bayani akan abunda ya kawo su, nan take ƙanin Abba yace (daya daga cikin yaron Hajiya babba) yace ai tunda yarinya da yaro sun amince da junan su har an kai ga wannan matakin kuma kuma manya mutane Alhamdulillah munji dadi sosai sai ayi abunda Allah ya ce sai asa rana. Kowa yayi mafarki ciki da maganar da yayi saboda ya jero maganganu cikin hikima..
Nan ko aka bada kudin auren jadwa masu yawa har abba sai da yace a rage albarka ake nema da kyar suka amince suka rage 15% cikin kudin ba don sun so ba..
Maganar sa rana Abba yace su dakata zai yi shawara da mahaifiyar ta.. sai da ƙanin Abba ya juya ya kalle shi don yasan qaunar da ake soya wa yau Abba da kanshi ne yake maganar mahaifiyar jadwa wanda baya don maganar ta.. hmm lallai
Cewa suka yi ba matsala dama ya dace bangaren mahaifiyar su sani saboda suma suna da hakkin.. shi ko abba duk ahankali ya koma kan hidaya wai a yau yake tunata toh ina take meyafaru da ita, ina taje duk yana da tambayen kan shi duk ya matsu su wuce ya kira jadwa ya tambaye ta labarin hidaya wai meke faruwa da shi ne...
Kowa aka yi sallama suka fara fita daga parlourn Senator ibrahim Rashid sun yi musabaha da Abba amma ya lura yanayin shi ya chanza akan na dazu sai yake tunanin toh Allah yasa lafiya dai ya fada a ransa.. suka wuce su Abba da sauran bokan shi suka raka su har inda suka yi parking in motocin su.. mai gadi ya bude gate suka fara fita..
Duk umma na nan tana kallon abunda ke faruwa a wurin window.. sai gumi take yi watau duk sun gama abunda suke yi kenan innalillahi wa'inna ilaihi raju'un umma kawai take fadi..

YOU ARE READING
JADWA (Completed)
AventuraHe make love stories for a niqabi girl and pious heart but step mum, sisters and fake friends that back stabbed and betrayed her. After all they go like this.. Completed but editing.... Find out in the novel Note: A Hausa novel