JADWA 40

100 11 0
                                    

Koda suka isa yadda aka yi decorating in wurin ba ƙaramin kyau yayi ba manyan abokan abba da nashi kanshi Abban waje dabam suke na daddy watau iyayen ango kenan wajen su dabam shi an ƙayata wajen ba ƙaramin kyau yayi ba sai wajen ango da abokan shi sai can gefe idan aka tanadar ma mutane abokanan arziki.. Masha Allah kyaun da wurin yayi baki bazai iya fada ba haka hannu bazai iya rubutawa ba wlh kuwa sai akamanta. Ango da abokansa da iyayen sa ba ƙaramin dadi suka ji yadda tun sanda suka fara neman aure har aka kai a wannan matakin auren ba ƙaramin karrama su ake yi gashi yau babban rana shima abun yafi na ko wani, ba wani wa'azi akayi ba ko nasiha kawai dai da aka bude taro da addu'a sai fara serving in kowa ma'aikatan wani restaurant aka yi haya suka zo aka yi serve yourself abincin sai wanda kake zaka dauka masha Allah kowa da ya je wajen nan yaci ya koshi ba ƙaramin ko shi aka yi harda su raguna akayi barbecue.. ko sai yabon walima yake yi ana ta hammada sannan duk wanda zai wuce da souvenir shi a hannun babban bag ne wanda aka rubuta ma Thanks for coming! Fahad & jadwa. Cikin bag in kuwa kawai bottle water, drinks, snackers, key holders Wanda dauke yake da sunan amarya da ango, sai baban jug, sai humidifier duk aciki. Kowa sai yabon kyautar yake yi, daga nan aka ci addu'a aka sa ma amarya da ango albarka aka fara watsewa uban ango ba karamin dadi yaji ba yadda mutanen shi ke ta yabon sukin shi Alhamdulillah kawai yake ta fadi yadda Abba ya kashe kudi shima haka ya samu kudi har sun fi abunda ya kashe daga kan abokan shi na kasuwanci har abokanan.arzik da abokan daddy ba ƙaramin kudi ya samu ba shi kanshi daddy saida ya karbi account in Abban wajen wani yaron shi ya sa mai kudi alert akwai ya gani da sunan surikin shi yayi mamaki, kiran shi yayi ya amsa godiya kuma yace da ma bai turo kudin ba tunda shi kanshi yayi hidima dadyy yace su bar zan ce kawai..

Iyayen ango sun shirya tsab zasu bar garin bauchi su wuce yola don sun koma guest in su sun fara shiri, ita ko a bangaren amarya jadwa babu abunda take yi sai kuka babu wanda bai yi kuka saboda yadda jadwa da mommy suke kukan rabu da kyar Abba ya zo ya lallashe su yayi masu nasiha mai ratsa jiki yace aure ne ya haifi su duka suka suka yi dole wa'inda suka haifa suma suyi sai dai ayi hakuri da juna.. da kyar ta samu ta daina kukan amma tana yin na zuci, haka taje ta shirya ta sa lafaya fari duk idan ta ya kumbura radiya mai taimaka mata ita ma kuka take yi ban ta shirya taje ta sallame su Aunty zainab, yan uwan mommy suna sunyi mata nata nasihar sosai sai hawaye ki zuba mata radiya na goge mata da ga karshe dai suka raka ta har zuwa parking space ta shiga mota tare da wasu yan uwan mommy da na Abba a ka wuce da ita airport, ko da suka isa airport kuka mai karfi jadwa ta fara yi Abba na bayan su ya sauka da mota ta sheka da gudu ta fara rungume shi ya cigaba da rarrashin ta har sai da tayi shiru a lokacin ne ya sa ta a jirgi radiya da yan uwan mommy na bin bayan ta suka shiga jirgin aka fara shirin tashi, sai Abba ya juya ya wuce tana mashi waving tana hawaye duk dauriya irin na Abba sai da yayi hawaye bai bari sun gani ba sai yayi saurin shigewa motar shi ya bar wurin, su ko angon ne har sun isa adamawa.

A can Adamawa kuwa ba ƙaramin galima aka shirya ba ana jiran a zuwan amarya.. 

Manya manyan motoci irin na gidan yan siyasa aka aika dasu airport don daukar amarya tare da auntyn su fahad da sauran sistern dadyy guda biyu, koda suka isa bai fi minti 10 ba suka sauka da murna kowa a fuskar shi suka je suka tarɓe su ita ko jadwa ta rufe fuska da lafaya radiya ke taimaka mata wajen tafiya sai sistern mommyn da gefen ta, duka sun ji dadin yadda yan uwan fahad suka nuna masu sosai suka gaisa suna ma amarya baka da zuwa garin Adamawa.

Baya sun gama gaisawa ne suka ja ta wajen wani babban moto wanda Sultan ne Sultan ne driver wato kanin Dr fahad ana suka ce amarya zata shiyasa amarya da radiya sai Aunty step mother su Dr fahad sune a motar kawai sauran motar kuma yan uwan mommy suka shiga aka je su sai cikin gari, wani babban unguwa aka shiga dasu babu abunda ke cikin unguwar sai lafiyayyun gidaje da titi sai itatuwa da suka zagaye gefen titin ba ramin kyau unguwar yake da shi ba saboda ma duk gidajen da ke unguwar gidajen sama ne masu Allah radiya kawai take fadi.

Ba wuya suka kai aka wangale wani katon gate aka shiga dasu ita dai jadwa duk tunani ya cika ranta wai yau ita ce a wani gari aure ya kawo ta ita ta ina zata fara rayuwa da wani da kuma yan uwar wani ? Shin zasu so ta ? Kowa zai so ta? Duk da tana kanin alama anan ance ba'a yabon dan kuturu sai ya shekara goma da yatsu ita ya rayuwar zai kasan ce a Adamawa da kuma Abuja ? Ita tsoron nasihar da aka mata take ji inda ake cewa tabbas aure Akwai dad'i kuma akwai daci a ciki babu wanda rayuwar auranshi yake 100% perfect saboda akwai jarabawa idan Allah bai jarabce ka ta miji na sai ya maka jarabta da 'ya'ya ko yan uwan miji ko iyayen miji ko makwabta.. shi yake ta yar mata da hankali ida ta tuna da kuma ance You should always think positive about your life domin Allah shine masanin abu fili da na boye sai taji sauki sosai. Wannan tambayar ne ya cika mata rai har aka kawo bata sani ba sai da radiya ta ta bata ta ce fito amarya mun kawo.. tana sa ka kofar ta mota da murna ana buda aka cika wajen da mutane yan uwa da abokanar arziki na gidan Dr fahad ana murna zuwan amarya..

Wata matashiya na gani wanda ake je ma Aunty nana ta zo da gudu wai ita baza ta bari amaryan su tayi tafiya ba ta hau bayan ta dariya  aka farayi a wajen da kyar aka samu jadwa ta ita hawa, don kunya duk da fuskan ta na a rufe amma ita ka Aunty Nana ba abunda ya dame ta haka ta dauke ta har parlourn daddy ta aje ta idan mommy Dr fahad take zaune da daddy har da angon namu, su ko su radiya ma sauki aka nuna masu don ance sai gobe zasu koma aka aka fara masu hidima ba tsayawa.

****
Daddy ne ya fara bude masu shirun da addu'a ya ma jadwa Barka da isowa family in su, ya cigaba da  masu nasiha irin wanda iyaye ke ma yayan su idan sunyi aure ko zasu yi aure sosai na sihar na shiga su musamman Dr fahad da daddy ke kallon shi ido cikin ido yana fada mashi da yaji tsoron Allah ya kula da ita cin ta shan ta suturar ta da lalular rashin lafiyar ta karatun ta tunda shi yace zai yi, da kulawa sosai saboda yadda ya raba ta da iyayen ta yan uwan ta abokanan ta da kowa na ta ya kawo ta nan garin idan bai kulata ba wlh sai Allah ya tambaye shi, ya kare mata mutuncin ta kar ta yi kukan koma idan yayi haka tabbas zaman su zai yi dai dai duk abunda ta mashi kar yace zai rika kai ta kara ko wajen su ko wajen iyayen ta shi kara yana zubar da mutumci ne ya tsaya shine shugaba a gidan shi ya masu adalci ya yanke hukuncin daidai da abinda ya faru sosai Dr fahad yake jin nasihar sannan ya dawo kan jadwa ya mata nata yace ta dauke su tamkar iyayen ta domin babu abunda zata nema ta rasa a gidan In'sha'Allah ta rike mijin ta da iyayen shi da yan uwan shi duk abunda ya mata ba dade ba idan ta ga baza ta iya kyale ba akwai auntyn shi wanda sun shaku sosai nasan zaki ji kunyan mahaifiyar shi toh ki sake jiki da auntyn su sosai yana cikin maganar sai ga aunty ta shigo da sallama dama tana ce wajen su radiya da sauran mutanen Bauchi tana hidima dasu, koda ta shigo ta zana kusa da jadwa tana bubbuga bayan ta alamar lallashi, haka daddy ya gaba ma nasihar shi ita ma Aunty ta daura da nata, haka Aunty ta ce mata duk abunda take so ko kuma kar yaji kunya yazo ta tambaye ta ta zama yar gida sosai jadwa taji dadin maganganun su she feel home haka take fada Alhamdulillah ko suka gama daddy ya fara fita sai mommy ta wuce waje wajen jama'a daga Aunty sai jadwa suka saura a a parlourn sai ango Dr fahad, nan Aunty ta fara mashi sheri da ya wuce gida hakanan anjima zai ganta kar ya cinye ta dariya ya kama yi yace toh Aunty dan Allah ki bani minti biyar mu gaisa mana toh tace ita ma tana dariya sai ta bar dakin nan ya je kusa da amaryan shi ya bude mata fuskan kan ta a kasa yace my forever sai tayi murmushi amma still kanta na kasa Alhamdulillah ya fada a fili ya kai bakin shi wajen forehead inta ya mata kiss wani yar taji da sauri ta ɗago sai kuma ta sauke fuskantar kasa tana wasa da yatsun ta nan ya kama hannu ta ya mike da ita tsaye tana kallon shi can sai taji idan ta yayi nauyi sai ta sauke kai nan ya je ya rungume abun shi yana fadan Alhamdulillah.. sallama suka ji sai tayi saurin sake shi tan sauke ka kasa dariya yayi yace ke fa mata nane meye na wani sauri kamar munyi sata ne ? Murmushi tayi sai ya kara matsawa kuwa da ita alamar zai kara mata wani hug in sai ta nuna mai door nan aka kara sallama sai tace Dr sweet kaje dan Allah ka bude mana yace yawwa dama magana nake ji ashe kina magana sai tayi murmushi sai ya mike zuwa door.

Ma'assalama 🦋❤️
Sorry for me not posting last week, I was going through lots but Alhamdulillah everything is going well now with the help of my Rabb.

I love you all my readers xo xo, pls do ignore mistakes it's an unedited chapter

Next chapter coming soon In'sha'Allah so stay turned and enjoy!!! ❤️

JADWA (Completed)Where stories live. Discover now