JADWA 20

118 10 0
                                    

Koda ta isa gida haka hidaya ta fito yana yi mata sannu da dawowa amma da ganin ta sai taji gaban ya fadi sai tayi addu'a aranta, kuma bata sa komai akan faduwar gaban ba, bayan sun dan yi fira kadan sai ta koma part inta, ta tarar da jadwa ta tashi daga bacci sai sheko da guda ta rungume ta tace mommy please call dad for I'm deeply wanna hear his voice.. hidaya ta tsaya tana kallon ta tace tohh fahhh.. wai yaushe zaki girma ne yanzu fa kina 14years next zaki shiga ss1 kin girma fah toh wai da kike cewa na kira mako Daddyn ki Ina wayen ki? Tace ni da wayanki nake so.. I want to use your phone not mine, sai ta marairaice fuska. hmm dariya abun yaba ma mommyn jadwa tace kai!! Jadwa rigima toh dauko wayan nawa sai mu kira shi.. haka ta nuna mata a hannu yana kam dinning ita kuma ta wuce dauko wa.. aran mommyn jadwa tana fada tace "ita fa jadwa duk abun nan da take yi don taga bata da kauna ko kanine da duk baza tayi wannan hmm Allah yasani Ina so na kara haihuwa da Abba amma gashi shiru, shi kuma duk irin tarin dukiyar da yake dashi bai taba nuna damuwar shi ba kan rashin yaro ko yarinya da bai kara samu ba, ko wani nashi ma babu wanda ya taba nuna hakan, ita kuma amaryan shi ma har yanzu shiru toh Allah shine yasan daidai" tana gama fadan hakan yayi dai da lokacin da jadwa ta dawo daga dauko mata wayan haka ta kira da Abba suka gaisa ta ta ba ma jadwa wayan, tana bata ta kuwa ta wuce da wayar dakin ta acan suka yi wayan take tambayan shi yaushe zai dawo yace sai nan da 4days tace toh Allah ya dawo dashi lafiya yace Ameen..

***
Washe gari tun da asuba umma ta fito waje tana tunanin inda zata gida rami kuma tana kare ma gidan kallo babu wanda ta gani saboda kowa yana bacci, bata bari an fara kiran sallah saboda ta san da an fara kiran sallah dole zata ga ma'aikatan gidan maza sun fito yin Sallah.. ko ina gidan duk inter lock ne sai ta backyard da aka zagaye da nest inda ake kiwo su dawisu da dai sauran abubuwa.. nan ta zagaya ta fara gina rami a hankali ta zuba duk wani mugun abun da boka ya bata Kamar yadda yace karta juya idan ta fara har ta gama haka ko tayi.. sai da ta gama ta tashi ta koma part inta.. Tana koma wa aka fara kiran sallah sai tayi ajiyar zuciya. Anci Sa'a babu wanda ya ganta.. toh sai ta fara tunanin ya za'ayi ta miyan kan rago kuma hidaya tace can dai ta cigaba da tunani iri iri sai tayi ma kanta alkawarin kafin gari ya waye dole zata samu mafita.. da wannan tunanin ta koma bacci abinda sai rana ya fito take sallah watarana ma bata yi, yaran ta kuma sun sa ma duniya gaba suma ba kullum suke yi kuma dama ba wuri ɗaya suke ba ta bayan part inta Abba ya basu daki mai kyau..

Karfe goma cif ta tashi daga bacci lokacin rana ya fito sosai tayi wanka tayi sallah kai tsaye ta wuce part in hidaya tana zuwa taga tana zaune kam sallaya alamu ya nuna ta idar da salatul duhe ne tasbi a hannu ta tana ja.. ko da tayi sallama sai ta amsa ta sunyi gaisuwa take ce mata, umman yara ya gajiyan tafiya, sai umma tace wlh akwai gajiya kam Ni bana ma jin dadi wlh koda na dawo jiya sai amai take kwarawa na kasa cin komai wlh.. ashha hidaya tace wlh ban sani ai da na shigo na duba ki, kuma ina ta fada araina zan shigo idan na idar da sallah na dubu ki, sai umma tayi murmushi tace toh ai ni gashi na shigo, yanzu haka ma wani turare na su A'isha suka shigo mun da shi wlh duk sai naji a hankali ya tashi da gudu na wuce toilet na ta amai kuma banci komai ba tun jiya da nayi amai da dare hatta da aman da nayi yanzu wlh ruwa ne akwai sai wahalar da nayi.. Allah sarki cikin muryan tausayi hidaya ke fadi ta tausaya mata sosai tace wlh na tausaya maku sannu umman yara irin haka ba dadi, amma wannan fa yan da alaqa da mun kusa yin tauron suna a gidan nan.. sai ta fada tana murmushi, ita ma umma murmushi tayi tace wai ciki kike nufi? Sai ya hidaya tace eh mana ai wannan duk symptoms in shigar ciki ne duk da dai idan typhoid yayi yawa yana sa mutum yawan amai amma wannan amaryan tamu bata da typhoid sai da ciki..😁 nan umma ta kama nuna alamun kunya wai ita kunya take ji (Ni fa abunda yake bani mamaki umma fa ma karamar mata bace don ta girme hidaya sosai amma sai ta kama yin wani abu tana ji da kanta kamar irin yar shekara 25 ne aka aro hmm)
Hidaya dai dariya tayi ce don Allah ya kamata anjima mu kira Abba mu fada mashi kuma mu tafi asibitin shi ( Don Abba har asibitin shi ya bude ana raba magani kyauta kuma ana taimakon talakawa sosai a wajen ba wulaqanci kuma ya dauko kwararrun ma'aikata yana masu salary mai kyau shiyasa suke jin dadin aiki asibitin kuma suke mashi yadda yake so sannan ana samun magani masu inganci wurin sosai kuma ko sisi ba'a karɓa) umma tace A'a don Allah mommyn jadwa basai kin kira Abba ki kyaleshi kawai, hidaya na mamakin maganar umma tace toh amma dai kinsan babu yadda zamu bar gida muje asibiti bada izinin mai gida ba ko, tace ai ba inda zamu don Ni dai bazan je ko wani asibiti ba, sai hidaya tace toh ya zaki zauna da ciwo a gida ai ko don lafiyar babyn mu umma tace hmm ni dai abar zance zuwa asibitin nan dan Allah tunda jibi Abba zai dawo idan ya dawo In'sha'Allah mun je, sai hidaya tace okyy ta nice ba kya son zuwa tace wlh a'a ko shi ma sai naga zan iya ta fada a takaice ita kama hidaya taga jin haka sai tayi shiru... Sai tace mommyn jadwa don Allah Kar ki dauka ko wani abu ne fah akwai bana son zuwa ne, sai hidaya tace toh yayi ba matsala Allah ya kara lafiya.. tace Ameen tace Ni gaskiya yau a dakin ki zan wuni don kamshin turaren nan na A'ishah nasan har yanzu bai fita ba kuma yana da karfi sosai bazan iya zama ba, hidaya tace ba matsala ai.. nan umma tace mata wlh yanzu haka ma marmarin kan rago nake yi.. na samu ayi mun pepper soup inshi.. nan hidaya ta kyalkyace da dariya tace hasashe na dai ya tabbata, kai Ni ce zan fara fada ma Abba wannan albashi ko dan na samu goron albashi mai tsoka ta fada tana cikin annashiwa.. ita ko umma cikin ranta abun mamaki ya ke bata ita mai ke gare ta dama ace cikin ne ai da tafi kowa jin dadi ko don tasan idan ta aje yaro da Alhaji akwai riba sosai amma har yanzu shiru ba komai ko batan wata bata taba yi don kuma ita ba juya bace tunda ka yaran ta a gaban ta, amma mata sai maganar ciki ciki take tun dazu lalle matan nan ba hankalin, ita ta haɗa plan inta yadda zata samu zuci abincin nan tare maganin boka ya fara aiki kan ta, ita kuma ta dameta da wani shirme wai suje asibiti, yauu in sun je asibiti ba abinda za'a gani wlh don ita tasan babu abunda ke cikin cikinta kuwa... Nan hidaya ta bubbuga ta tace umman yara mai kike tunani ne ina ta magana baki ji, tace yi hakuri don Allah mommyn jadwa zan samu? Tace mai zai hana yanzu zan kira lantana tazo taje ka suwa ta sayo idan ya sayi sai tasa girkinta fara dafawa In'sha'Allah zaki Sha pepper soup kuwa maman baby. Kallonta umma tayi da murmushi tace toh Nagode..
Nan ko ta kira lantana gaban ta taɓa kudi tace taje tayi sayo kuma idan ta dawo karya bata lokaci ta fara dafawa. Tace toh Hajiya ta karba ta wuce.
Ita ko aran umma tana tunanin ta ya za'ayi ta zuba maganin tunda mai aiki ne zata dafa , nan dai tace ai ba za'a rasa yadda za'ayi ba ta dai dawo Ni kuma umma ta fada a ranta.
Lantana mai aiki ta dawo cikin lokuta kadan babu dade wa kuma ta dauro girkin kamar yadda aka bata umurni, bayan wuce war ta kasuwa umma da hidaya suna cikin poulor suna ta fira ita ko hidaya zai zolayar umma take yi ita kuma ranta abun haushi yake baya, har hidaya ta dauki waya zata kira Abba umma ta hana tace ta bari sai Abba ya dawo sai ta fada ma shi. Ta yarda da hakan sun ci gaba da fira ita ko kan umma ya kulle sai tunanin take yi ta ina zata bullo ma zuba maganin nan, can sai ga lantana ta fito daga kitchen, hidaya tace ya kusa yi ko? Sai tace ai saura kadan can umma sai ta mike tsaye tace kun ga ko har kamshi ya biyo ta wlh sai naji kamshin ma yayi mun dadi bari naje na gani, sai hidaya ta kama dariya sosai tace toh sai kin dawo.. aiko ta mike da sauri sai kitchen dama maganin yana kulle cikin rigar ta sai ta fito dashi tana kalle kalle da sauri ta bude girki kan rago sai zaɓarɓaka yake yi ai ko ta fara barbada maganin da sauri tana yi ta na kallo kofa tana gamawa sai tayi ajiyar zuciya ta mayar da marfi ta rufe ta gyara jikin ta, tafito tana rufe rufe fuska kamar munafuka, sai iso dab dasu ta zauna tace gaskiya lantana ki iya girki wlh saura kadan yayi ni duk na gaji kamar na debo hakanan sai hidaya ta kama dariya tace ai dama kin debo hakanan abun ki, tana gama fadan haka yayi daidai da lokacin dasu Fatima suka shigo dakin wai sun zo duba umman su, sai tace sai yanzu zaku zo zata fara masu fada mommyn jadwa ta tare masu tace tayi masu uzuri, nan A'isha ke tambayar jadwa sai hidaya tace ai tun jiya ta wuce gidan aunty ku zainab tana can.. nan suka ce suka zasu je sai tace toh zata ma driver magana sai anjima ya kai su.. sai suka wuce suka je zasu je lesson aka ce masu sai sun dawo.. lantana kk lokacin ta tashi ta wuce kitchen duba girki koda taje pepper soup yayi haka ta dauko wani babban kula mai kyau ta jiye shi ciki ta dauko plate masu kyau wuto dasu parlour.. tana zuwa umma ta tashi taje ta tarbe ta ta taya ta rike kaya.. ita dai hidaya sai shiri take mata har lantana ta fara gane wa.
Haka umma ta zuba ma kanta bata ma tsaya lantana tayi serving inta ba ita wai nan da gaske takeyi fa..
Ta zuba masu ita da hidaya sai ta zuba ma lantana nata, aiko hidaya tace bazata ci ba nan umma gaban ta ya fadi tace aranta duk wannan wahalar kice ba zaki ci ba wlh baki isa ba. Nan umma tace kai ai gaskiya bazan yadda ba wlh tare zamuci Ni bazan ma iya ci idan bada ke ba, aiko hidaya ta kama dariya tace tohh kuma dadi na da irin ku sai rigima. Toh naji zan ci amma kadan umma tace naji ki dai ci ko kadan ne.. aiko nan umma ta dauko daga kan sofa tayi Bismillah sai ta sa baki ta fara ci, suna ta ci tare nan hidaya tace ta koshi umma tace har kin koshi tace eh dama nace maki kadan zan ci. Tace toh yayi tunda dai kin ci, ita ko lantana ta lamushe nata umma ta kara mata.. hidaya bayan ta gama sai ta wuce toilet ta wanke hannu da baki amma taji wani yanayi ta faso taci kan abun sosai shiyasa ma ta bada kudi wanda za'a sayo dayawa amma kana kawo abun taji ya fita ranta komai yasa oho.. sai ta fito tana shara bakin ta lokacin umma ta gama tace ita ma bari taje ta wanke bakinta ta hannu ta fara jin bacci ta wanta sai hidaya tace toh yayi kyau nan lantana ta wuce da food flask in kitchen..
Ko da ta dawo daga wanke baki sai ta kwanta kan sofa ta fara bacci.. ita dai hidaya tun da taci abincin nan bata jin dadin jikin ta.. koda Yamma yayi lokacin umma tace zata koma part inta. Sun wuce tare hidaya taje kara kata koda taje ta zauna kadan can ta wuce.. umma ta fara lura da yanayin hidaya ya chanza sai ta fara jin dadi a ranta koda hidaya ta koma part inta aiko da gudu ta dauko wayan taga missed calls in Abba amma bata ma bi ta kanshi ba sai numbern tabawa da ta nemo ta kirata taba bata labarin abunda ya faru.. nan tabawa ta jinjina mata tace tayi kokari sosai bata taɓa tunanin hakan daga gare ba, tace ai tunda taji shiru tasan komai na tafiya daidai ya kenan tace yanzu yaushe Alhaji zai dawo tace jibi tace mu jira muga me zai faru. Tace toh shikenan.. sai da suka gama waya da tabawa sai ta kira Abba nan ta bashi hakuri tace ta bar wayan ta ne tun dazu tana part in mommy jadwa bata jin dadi ne.. yace taje asibiti tace A'a yace meyasa wai sai ya dawo nan ta fara mashi shagwaba yace toh idan ya dawo zasu je tare ai koda ya matsa da yasan abun da yake damunta cewa tayi zazzaɓi ne yace toh Allah ya sawake.. shikenan suka yi sallama

A bangaren mommyn jadwa dai tana can ta rasa abunda yake mata dadi, can dai ta debo ruwa ta yi addu'a ta sha sai taji abu ya lafa don ita baza tace ma abunda yake damunta ba.. koda dare yayi ta kwanta sai ta manta bata yi addu'a don bacci dauke ta yayi, sai tayi mafarki ana bin ta da gudu mutane biyu mata amma ba nuna mata kamanin su can ta sai wani katon mutumi ya shagabta yana ce mata ga rami nan ta fada sai tace A'a sai fara karanto Ayatul kursiyu sai da take karshe sai ta farka duk tayi zufa sai ta kama salati can sai taji cikin ta yana murda wa sai ta wuce toilet da gudu koda taje toilet sai taji abuna zuba mata ita ta dauka ma ko fitsari ne tana kunna wuta sai jini ta gani yana zuba..

Please make una vote and comment ohh!
As I just dey see viewers I wan see voting too
Comment ohh please let me get some ideas from you guys

Enjoy!! ❤️❤️
Your khads

JADWA (Completed)Where stories live. Discover now