EPISODE 6

27 1 0
                                        

MAGANA TA ƘARE..!!

true life story

Mallakar:chubaɗo✍️

Not edited


06

____Miƙewa Umma tai da sauri ganin yana ƙoƙarin yin kisan kai tai saurin shan gabansa tareda riƙe katakon tana kallon tsakiyar idonsa Waƴanda suka rine daga asalin kalarsu zuwa wata daban sabida tsabar fishi, Baba Atine wadda ta fito daga ɗaki sabida jin ihun su musamman Bintalo wadda tafi dakuwa a hannunsa, da farko tana jinsu amma taki fitowa seda ya gama ragargazarsu sannan ta fito kawo ɗauki.

Daƙyar suka iya janyeshi Ita da Umma don cewa yay wllh seya kashe Bintalo har Lahira, toshe masa Baki Atine tayi cikin hanzari tace "kul na kuma jin irin wannan mummunar maganar ta fito daga bakinka Me sunan Ubana, yiwa wani fatan mutuwa ma kuskure ne ibrahim balle kuma kai da bakinka ke iƙirarin furta kalmar kisa ga Uwar wasu, haƙuri akeyi da Rayuwa a duk yanda tazoma ibrahim yanzu ka duba irin Kukan baƙin cikin da mahaifiyarka keyi duk a sanadin wannan ɓarnar dakayi!" rintse idanunsa yay da ƙarfi sabida ganin yanda Umma ke kuka da dukkan ƙarfinta, tsuguna mata yay bisa diga-digansa yace "don Allah umma kiyi haƙuri ki dena zubarda Hawayenki akan Matakin dana ɗauka akan waƴannan matan, wllh Ummah zuciyata bata iya sarrafuwa aduk lokacin da wani mahaluki ya baƙanta miki balle har yasaki zubarda hawaye!."

"Na rantse da Zatin Allah a duk lokacin da kike cikin baƙin ciki senaji dirar hakan a zuciyata, Umma indai akanki ne zan iya kiran kaina da cikakken Mahaukacin da baya iya sarrafuwa, matsayinki daban yake a zuciyata shin taya kike tsammanin wannan Ibrahim ɗin ze iya saita zafin zuciyarsa a lokacin da wannan ƴar Wahalar take jinginaki da Fajirci?" ya ƙare maganar yana kallon Umma wadda hawayen datake zubarwa suka tsaya cak, tabbas tasan ƙaunar da Gudan jinin nata ke mata me girma ce wadda kokaɗan baya iya sarrafa kansa indai akanta ne, share hawayen Fuskarta tai da Sauri tareda ɗagoshi bisa kan ƙafafunsa ta Rungumeshi tareda sakin Kuka marar Sauti da gunji, a wannan ranar Zan iya cewa baƙar Rana ta zamewa su Bintalo sabida kaf cikinsu babu wadda bata ziyarci sarkin ɗori ba. Tun daga Wannan ranar suka shiga taitayinsu akan Umma, koda zasuyi ƴan munafince-munafuncensu sedai a bayan idanunta.

Bayan wani lokaci, Hajjo ce Zaune saman tabarma a ƙaramin Soron gidansu tanacin wainar Fulawa

Tanaci suna Hira da inno Ummi ƙawarta ce ta shigo gidan aɗan Hanzarce kamar an hankaɗo ta, Hajjo wadda ke ƙoƙarin kai Wainar Fulawa Bakinta Ummi ta katseta tace "wallhi Hajjo bakida Mutunci Gabaɗaya yanzu kin zanza kamar bake ba" ta ƙare maganar tana kai mata duka a baya, ƙara Hajjo ta ƙwalla tareda dafe gurin tana galla mata harara tace "Ai wllh bazan ƙara zuwa gidanku ba balle Kuma gurin Siyar Awararki" tai maganar tana galla mata harara.

Zama Ummi tayi daga gefanta tana kallonta mamakin maganar Hajjon kwance a saman Fuskarta tace " kai Hajjo to me nai miki kekuwa?" waiyar Hajjo ta gutsira tareda dangwalar yaji takai bakinta tace "sabida bala'i kike ƙoƙarin janyo min" gwalo ido Ummi tayi wace zatai magana kenan Hajjo ta katseta ta hanyar cewa "nidai kawi karki wani cemin komai, a sanadin labarin mafarkinki da Wajagal sabida nayi dariya kawai ranar na dawo daga makaranta ya tareni, bakiga kashedin daya dinga zuba min ba amma kuma kinsan meya faru?" Hajjo ta jefawa Ummi tambayar tana ƙawata fuskarta da kyakkyawan murmushin daya bawa dogayen fararen haƙoranta damar Baiyana, sosai siririyar wushiryar dataiwa haƙoranta ado itama ta fito sosai ɗan wara idanu Ummi tayi tace "nidai na gama zaƙuwa naji ƙarshen labarin nan wllh, don Allah meya faru ?" umni tayi maganar tana ƙara gyara zamanta, Hararan Wasa Hajjo ta wurga mata tace "Malama baku gaisa bafa da inno" male baki Ummi tayi cikeda zaƙuwa tace "naji zanje mu gaisa amma don Allah ki fara ƙarasamin dramar taku tukunna" wani far Hajjo tayi da manyan idanunta a ranta tanajin kanta a sama tace "Ummi Ashe Wajagal mugun kyakkyawa ne ban sani ba? Wllh Ban taɓa sanin yanada wani irin sihirtaccen kyau ba seda yay mik murmushi a lokacin dana gaya masa dalilin dariyar daya ganni inayi" kallon galala Ummi tai mata tace "aini tun ba yau ba nasan Yaron ya Hadu, kuma kyansa wani irin kyau ne da baka iya ka iya ƙaiyadeshi cikin ƙanƙanin lokaci ba, ni babban abinda ke burgeni dashi guda ɗaya ne tak." ummi ta faɗi hakan tana kallon hajjo wadda taƙara gyara zama tana jiran ƙarin bayani a Gurin Ummi

MAGANA  TA ƘAREWhere stories live. Discover now