MAGANA TA ƘARE
true life storyChubaɗo ✍️
010
____Yana sauka a bakin Hotel ɗin ya kalli me napep ɗin yace "don Allah ƙarfe nawa?" yay maganar tareda miƙa mishi kuɗin sa, agogon dake ɗaure a hannunsa me Napep ɗin ya kallah sannan yace "goma da Arba'in." juyawa yay a ɗn hanzarce yay cikin Hotel ɗin
Tun a farfajiyar Hotel ɗin aketa faman tsareshi da tambayoyi tun yana shanye ɓacin Ransa harya fara Hasala, ƙyaleshi sukai ya shike fuskar nan tasa a ɗaure kaman baitaɓa ɗariya ba harya haura saman inda ɗakunan suke
A bakin ƙofar ɗakin ya tsaya tareda fara ƙoƙarin saita kansa sannan ya fara ƙwanƙwasa ƙofar, Mano dake gaban Madubi yana shiryawa cikin wani brown ɗin kaftani irin na Asalin mutanan Agadaz kansa ɗaure cikin wani haɗaɗɗen rawni cikin harshen turanci yace "who's that ?" wajagal dake tsaye jikin ƙofar yay saurin shafa kansa yace "I'm Ibrahim Alqasim." yay maganar yana sauke Ajiyar zuciya, a hankali cikin Nutsuwa Mano ya ɗaga kai ya kalli na'urar Cctv camara ɗin dake manne jikin gefan ƙofar ɗakin wadda ta baiyana fiskar Wajagal tun tsaiwarsa a bakin ƙofar, wani wadataccen Murmushi ya saki sannan ya fara takawa cikin takunsa na dattijantaka ya isa jikin ƙofar ya buɗe masa cikin harshen turanci yace " masha Allah I'm very happy to see you Mr. Ibrahim " wara manyan idanunsa Wajagal yay yana kallonsa yace " I'm sorry sir I'm not a Mr. Just call me With Ibrahim only" murmushi Mano yay me sauti don shiba mutum bane me yawan dariya ba yace "its okay dear but I can call you with your name bcoz is my father name" guri kan wata lallausar kujera ya zauna still yana kallon Mano wanda ke ƙoƙarin rufe ƙofar ɗakin yace "Eyyah" murmushi Mano ya kuma saki a karo na biyu yace " don't worry about it i should call you friend if you don't mind." murmushi Wajagal ya saki shima sannan ya ɗaga kafaɗa yace "indai ya maka a ranka to nima yamin" yay maganar yana maida kallonsa ga Ibrahim Buzu wnda yake kwance sambal duk ya ƙara Faɗawa daga jiya daya ganshi zuwa yau, miƙewa yay zuwa inda tankasheshen Gadon yake tareda ɗaukar hannunsa ya ɗora bisa goshinsa yay shiru kamar me son gano wni Abu a taredashi, ɗauke hannun yay da suri sannan ya kalli mano cikin harshen turanci yace "Amma meya samu wannan mutumin haka?" yay tambayar yana kallon Mano ido cikin ido, nan da nan yaga yanayinsa yay wata irin canzawa a lokaci guda tun kafin yakai ga yin magana tuni hawaye sun fara zubo masa.
Jikin Wajagal ne yay sanyi seyaji dama be tambayeshi ba wata ƙila da be sanyashi zubar da hawaye ba, a hankalin ya buɗe bakinsa yace " I'm so sorry please I don't mean to hurt you!" share hawayen Mano yay tareda ƙaƙalo murmushi wanda yafi kamada na dole yace "its okay dear insha Allah I will tell you bt not now maybe some other time." yay maganar yana komawa gaban Madubi don gyara zaman rwanin dake kansa, seda ya gama tsaf sannan ya dubi Wajagal dake zaune har lokacin a gefan gadon cikin harshen turanci yace "don Allah kaimin wata alfarma guda ɗaya mana, inaso ka zauna ka kular min da Babana zanje wani waje na dawo ne har a raina nakejin cewar na yarda dakai bana zaton cewar zaka iya cutar dani shiyasa na zaɓe ka." mano yay maganar yana kallon Wajagal wanda shima ɗin shi yake kallo.
Ɗaga masa kai yayi alamar gamsuwa sannan yace "kada ka jima don Allah don ban gayawa Ummata zan daɗe a nan ba" ɗaga masa kai yayi alamar gamsuwa da jawabinsa sannan ya ɗauki keyn motarsa da kuma wata baƙar jaka ya fita daga ɗakin bayan ya sumbaci goshin mahaifin nasa.
Tafiya mintuna talatin yayi sannan ya isa gidan Nurudden ɗin abinka da zamani na kimiya da map ɗin wayarsa yay amfani harya isa location ɗin Nurudden ɗin, gida ne makeke na afarma dagashi se iyalansa ne kawai a gidan gaisawa sukai da Hajiya fatima matar Nurudden ɗin sannan ta fita ta basu guri, Nurudden ya kalli Mano da kulawa yace "ina ganin wannan baze zama matsala ba don haka ka kwantar da Hankalinka insha Allah Alhaji zai samu sauƙi, tunda ka turamin Adireshin malamin nasa ai min cigiyarsa amma har yanzu shiru babu wani labari."

YOU ARE READING
MAGANA TA ƘARE
Non-FictionYa kasance mutum kamar kowa, amma ɗabi'unsa da mu'amalarsa sunsha ban-ban dana sauran jama'a. murmushinsa ragaggene kamar yanda dariyarsa ta kasance, rauninsa ƙwaya ɗaya ne tak shine MAHAIFIYARSA. Dukda kasancewarsa tantagaryar ɗan-daba mai lasisi y...