MAGANA TA ƘARE
true life storyMallakar: chubaɗo✍️
04
___✍️Da Zainab ya fara cin karo zata fita ɗanja da baya yayi kaɗan sannan ya kalleta yace "ke kuma ina zaki da ranan nan?" yay tambayar yana tsareta da rikitattun idanunsa waƴanda suka fara canza launi, gyara zaman hijabin dake jikinta tayi sannan ta fito da kuɗin dake Hannunta tace "Salak da Tumatur zan siyowa Umma." lumshe idanunsa yay kaɗan sannan ya zura hannunsa a aljihun wandonsa ya zaro Ɗari biyar yace "ungo ki siyo mata harda soyayyan kifi a gurin Hamza, saura kuma ki tsaya wasa harta fara jin yunwa kika yanda zanyi dake wllh sena ragargajeki" dariya tayi me sauti sannan ta ɗan marairai ce tace "Yaya don Allah kaban ɗari biyar ɗin littafin da akace mu siya tunda dai ka samu kuɗi yau." rintse idanunsa yay cikeda gundira da shegen surutunta yace "naji ai seki ware ko?" takalmin Robar daya siya mata ta ɗauka tasa ta nufi Hanyar Zaure tana dariya, tsayawa tayi trus tana kallon Nadiya ganin irin kukan datake gurya yasa ta isa gareta tace "ke lfy naga kina kuka? Meya sameki?" zainab ta jera mata tambayoyin duk a lokaci guda, kasa magana Nadiya tayi don batama san ƙaryar dazataima Zainab ɗin ba
Ganin shirun yayi yawa ne yasa Zainab ta miƙe da sauri tace "tsaya naje na dawo Umma ce ta aikeni siyan salak seki gayamin abinda kikema kukan" tana kaiwa nan ta fice da sauri zuwa aikem da akai mata, Da sallama ya shiga Rumfar amma kuma bega Umma ba hakan yasa ya nufi Uwar ɗakin Nasu kai tsaye. Umma dake zaune jikin wata ƙatuwar Akwatin ƙarfe tai saurin juyowa a mugun tsorace tareda sanya wani daddauɗan zanin gado wanda duk ƙura ta gama baibayeshi tai saurin rufe akwatin dashi, tsayawa yay daga bakin ƙofar ba tareda ya shigo ɗakinta still idanunsa nakan Ummah wadda a zuciyarta take addu'ar Allah yasa bega wannan akwatin ba.
Sakin labulan ƙofar yayi tareda komawa da baya ya zauna daga gefan shimfiɗarsa yay shiru, a ransa yana mamakin saurin daya gani a Fuskar Ummansa a lokacin daya shiga ɗakin ya sameta, tambaya ɗayace ke masa yawo a zuciyarsa itace "me Umma take ɓoyewa a lokacin data ganshi?" ya aiyana hakan a Ransa yayinda yake miƙewa ze fita, bisa ga mamakinsa har lokacin Umman bata fito ba hakan yasa yay waje abinsa tareda lalubo ragowan tabar Wiwin dake aljihun wamdonsa ya fara tashin hayaƙi.
****
PLATEAU STATE (JOS)
Unguwar Filin Sukuwa, wani ƙayataccen gini ne na alfarma wanda aka sarrafa tsarin kantangar gidan da farin Dutse, daga kallon farko idan kaiwa gidan zaka fahimci ba ƙaramin kuɗi aka kassara yayin gina wannan Gida ba, tsarin gidan Sama da ƙasa ne irin fasalin ginin mutanan ƙetare, a farfajiyar gidan kuwa danƙara-danƙaran motocine masu shegen kyau gamida tsada, haka kuma ko wace Mota dake Fake a gurin ta bawa naira Milion goma sha 12 baya.
Daga can bakin ƙofar Get ɗin Sojoji ne sanye da kaki suna aikin gadi, a hankali wata baƙar GLK ta ta silalo tareda tsayawa a bakin Get ɗin , tun kafin a danna horn tuni har an wangale mata jibgegen bakin Get ɗin Motar ta silala zuwa cikin farfajiyar Gidan inda aka tanada don ajiye motoci. Wani farin Matashin mutum ne ya fito daga cikin jibgegiyar motar wanda baze wuce Shekaru 40 a duniya ba, daga kallon farko idan kai masa zaka fahimci Ruwa biyu ne shi sabida yanayin tsarin halittar fuskarsa da kuma yanayin murɗewar gashin kansa, jikinsa a mirje yake babu alamar Ramar face zallar sheƙin jin daɗi take fita a saman tattausar fatar jikinsa.
Idanunsa sanya suke cikin Farin Glashin ƙara ƙarfin gani wanda ya ƙara baiyana ainihin ɓoyayyen kyen dake saman kyakkyawan fuskarsa, sedai kana kallon sa zaka Fahimci akwai abinda ke damunsa na daga ɓangaren Damuwa, A hankali yake takawa securitys din dake on duty se faman ranƙwafa masa suke cikeda girmama, ko kaɗan bemasan sunayi ba sabida tsabar rashin nutsuwar dake damun Zuciyarsa a nitse yasa zara-zaran yatsun hannunsa a jikin Handle ɗin ƙofar ya kunna kai zuwa ƙayataccen falon da baiyana muku irin tsaruwarsa ma ɓata lokaci ne.

YOU ARE READING
MAGANA TA ƘARE
Literatura FaktuYa kasance mutum kamar kowa, amma ɗabi'unsa da mu'amalarsa sunsha ban-ban dana sauran jama'a. murmushinsa ragaggene kamar yanda dariyarsa ta kasance, rauninsa ƙwaya ɗaya ne tak shine MAHAIFIYARSA. Dukda kasancewarsa tantagaryar ɗan-daba mai lasisi y...