21

273 17 3
                                    

_*CHEATERS CLUB...*_
_(Babban goro sai Magogin ƙarfe...)_

#ROMANCE
#FICTION
#ADULTHOOD
#SEXADDICTS
#WOMENPOWER

BY
_SURAYYAHMS_
_08060712446_

⏯️2️⃣1️⃣

Wajajen 11 na dare saura shema'u marafa ta dawo gidanta dake herbert marculay way lokacin mijinta engr mahmud harya gaji da jiranta ya fara bacci, tana turo kofar dakin ta hangoshi akan gadon can a matse ya rufe jikinshi da lallausar bargo tundaga sama har kasa alaman baccin daukarsa kawai tay badon yaso ba, ajiye jakarta kawai tay akan tabl snn tabi  tacire takalminta a sulale cikin sanɗa tawuce bathrum din sharp sharp ta kimtsa kanta, snn ta dawo ta kwanta ajikinshi ta hau juje juye dan hnklinta da tunaninta sam ba'a waje guda yake ba tuna irin kalar tarwatsa taron mata dazasuyi gobe da ita da hadiza wajen tuntsirar da lamarin auren ramatu ex minister da Alhaj kyari acikin ruwan sanyi wanda hakan yasakata ta shiga saukar da murmushin mugunta dan tasani sarai aikin wann Alfa din bana wasa bane yanaci sosai.

Ta jima tana sake sake aranta dan tasan sai ta shiga rayuwar hadiza ta temaketa sosai kafin nan ta iya samun cikakken Amincewa tare da bban matsayi awajenta harta more dukiyar nata itama.

sai can data gaji da lissafi snn ta matso jikin mijinta ta mannu dashi sosai,lumshe idanunta tayi tana sauke ajiyan zuciya mai sanyi sanin cewa yakamata yau din ta bashi kulawarta ta musammn amma tuna cewa yana gajiyar da ita a duk sanda sukayi wata mu'amalar aure yasata jin bazata iya ba dan batason wani abunda zai kawo mata tsaiko a shirinsu na korar kishiya ita da kawarta hadiza maitama dan ta wann hanyar ne kawai zata samu wani matsayi na musammn a zuciyar hadiza.

Ahnkli ta dora kanta akan kirjinshi tabita dora hannunta jikinshi ta mamayeshi bada jimawa ba bacci mai nauyi ya dauketa, tun daga yanayin rungumar datayi masa acikin baccin zakasan cewa tana cikin kwanciyar hankli anata auren tare da kuma kwanciyar hanklin samun irin rayuwar datakeso din daga wajen mijin nata.

Washe gari da kyar ya tasheta dan suyi sallah amma kuma juyi kawai take bata farkan ba har ya dauro alwala ya wuce kasa izuwa masallaci domin gabatar da nashi sallahn asubahin, dan Al'adace agareshi a kowani asubahi in ya fice sallah daga nan yake zama yay karatun qur'ani snn yay morning azhkar dinsa har sai gari ya fara haske snn yake dawowa cikin gida, idan kuma bada wuri zai je aiki ba daga nan masallaci gidan motsa jiki yake wucewa, already ya riga ya saba duk sanda ya dawo cikin gidansa walau daga masjid ko daga gidan motsa jiki,kode ya tarar da shemau ta fice aiki ko tana shirin yin hakan sam bata fiye kulawa dashi ba as usual a koyaushe dai mai aikinsu hafsat ce take tarbansa.

Daga cikin masallacin ana kammala sallahn subhi engr na idar da Shafe adduoinsa yasa hannu ya dauki wayarsa ya hau rubutawa shemau sako dan daga nan wajen motsa jikin zai nufa.

Kwana biyu sam basa fiye spending time sosai ba aransa yana mugun son samun nitsuwa da ita koda bamai yawa ba.

karar bedside alarm ne ya tada shema'un daga Barci, agogon tajawo a kasale ta duba time taga har karfe shida dede mika hannu tay tanamai tattaba dayan gefenta wani uban sanyi taji aranta dataji har yanxu mijinta bai shigo ba dan  asama sama cikin gigin bacci tajishi lkcin dayake tadata.

Agurguje ta miƙe ta shiga bathrum ta watso wanka tare da alwala tazo tay sallahn 5 secnds raka'a biyu agaggauce, nan ta koma jikin madubbi ta fara tsantsarawa kanta wani irin mayyar kwalliya wanda ya dauketa kusan minti talatin wanda tun kafin ta kammalashi ma bakaramin kyau tayi ba.

After 10 minutes da gama kwalliyar tabi ta kammala shirinta tsaf ta juyo zata dauki wayarta anan taga sakon daya turo mata awaya na cewa yana matsatsin bukatarta ma'ana yana bukatar yau ta dan bashi lkcinta..Wani irin lumshe ido tay snn ta budeshi ahankli dan ita din ma aranta tanajin matsatsin bukatartasa amma kuma bazata iya fasa zuwa mission dinta na tada gurmi ba dan tasan tabbas hadiza na cikin damuwa yau din nn sosai.

CHEATERS CLUB(Babban goro sai magogin ƙarfe)Where stories live. Discover now