Chapter 1

326 42 26
                                    

URBAN-CITY CONSTRUCTION COMPANY
ABUJA CENTRAL

Zaune yake a kan executive chair na makeken office dinshi wanda yake 5th floor yayinda yake aiki a kan Macbook dinshi.

Mai karatu ko da na matsa kusa da shi, wani kyakyawan gaske na gani. Fari ne sol kamar tsaada. Dukda a zaune yake, na fahimci cewar dogo ne. Siriri ne sannan ga gashin kan shi baqi qirin mai laushin gaske wanda saboda laushi har ruffles yayi. Gashin fuskar shi ya sha gyara ya kwanta a kan kyakyawar farar fuskar shi. Kallo daya zaka yi mishi ka tabbatar lallai bafillatani ne domin kuwa yana kama da su.

Sanye yake cikin wani farin yadi wanda aka yi ma dinkin zamani da samari suke yayi.. Ya bala'in yi mishi kyau. Kai da ganin yadin ka san ya ja kudi sossai. Babu abinda yake bazawa sai qamshin designer turare.

Ko da nayi scanning office din kuwa sossai ya birge ni. Makeken office ne sannan lafiyayye wanda yake dauke da kayan zamani na gani na fada. A cikin office din harda babban lounge wanda ba don workstation din da ke ciki ba, zaka rantse falon wani gida ne. Ko ina ya dauki sanyin AC wanda ya hadu da qamshin turaruka masu tsada ya bada wani yanayi mai dadin gaske. A taqaice dai wannan office din da nake kallo ko na shugaban qasa sai haka. Babu shakka irin wannan office din ne idan kana ciki bazaka taba jin pressure na aiki ba domin kuwa it's 100% conducive.

A bisa executive table dinshi ne na ga wani tag mai dauke da suna kamar haka:

YASIR USMAN BAKURA
MD/CEO

Qofar office dinshi ta qwanqwaso sannan ta shigo.

Ya Salam.... Wata kyakyawar yarinya ce fara ta shigo. Siriya ce sannan doguwa. Kamarnin ta sak da Yasir. Babu shakka qanwar shi ce. Sanye take cikin rigar atamfa wadda aka yi ma dinkin fitted gown sannan ta yafa dan qaramin gyale a kanta. Yanayin jikinta ya fi kama da a kira ta model.

"Yaaya har yanzu baka gama analysis din bane??" ta tambaye shi yayinda ta qaraso ta zauna a daya daga cikin kujerun da aka tanada don baqi.

"Na kusa gamawa Nasreen" ya fada cikin muryar shi mai masifar dadi.

"Gaskiya muna buqatar data analyst ASAP, aikin yana yi maka yawa ai Yaaya. Allah ya sa mu samu replacement din a cikin wannan batch din"

"Ameen..."

"Dama na zo in sanar da kai cewar zan wuce conference room ne don in tabbatar komai is in order kafin ka qaraso.. the interview will start in fifteen minutes"

"Okay toh... idan na gama I will join you guys"

Miqewa tsaye tayi sannan tace "sai ka shigo"

"Alright"

***************

Zaune suke a wani wuri na musamman yayinda suke ta karatu suna tattaunawa akan irin tambayoyin da za'a yi musu.

Wata yarinya na hango zaune a can baya riqe da file dinta yayinda tayi shiru tana kallon su. Ina qoqarin qarasowa kusa da ita ne na hango wani mutum ya shigo wurin yayinda duk suka gaishe shi.

"Sannun ku da zuwa.. kamar yadda na fadi muku dazu, mun gama shirya komai don haka da zarar CEO ya shigo zamu fara. Zamu Kira ku daya bayan daya. Akwai mai tambaya a cikin ku??"

"No sir"

"alright... All the best"

"thank you sir" suka fada gaba daya.

A lokacin da na juya don komawa wurin wannan baiwar Allah kuwa sai na ga ta dora kanta a bisa gwiwa. Mamaki ne ya cika ni ganin yadda kowa ke ta kai da komowa suna tattaunawa amma banda ita...

Shin lafiyarta kuwa???

***************

Zaune suke a cikin conference room din yayinda aka yi setting komai. Panel din yana dauke da mutum biyar ne dukda CEO din wato Yasir.

ILHAMWhere stories live. Discover now