Chapter 8

195 32 34
                                    

URBAN-CITY CONSTRUCTION COMPANY
ABUJA-CENTRAL

Wuraren qarfe Goma da rabi na safe tana zaune a workstation dinta yayinda take hira da Marwa a waya.

"Yanzu gobe idan na zo after close of business banyi latti ba ko??"

A dayan bangaren ne Marwa tace "Sannu agogo sarkin aiki... I swear idan sai kin tashi daga ofis zaki zo henna party dina kar ki zo"

Ilham wadda ta fashe da dariya ce tace "toh amma dai kin san ni ba hutu nake yi ba balle in bar ofis kafin lokacin tashi ko??"

"Na sani amma kuma ke ma kin San cewar idan kika dauki permission daga wurin boss zai bar ki tunda ya san cewar biki na ne ko??? ko bazaki iya tambaya bane saboda kina fushi da shi??? for crying out loud Ilham, har yaushe ne zaki zauna kina fushi da ogan ki?? lafiyarki kuwa??"

Ilham dai shiru tayi ba tare da tace komai ba.

"Oh.. bazaki yi mun magana ba don nayi maganar Oga?? toh Allah ya shirye ki. Idan kin shiga office dinshi yin discussions dinku na analysis da baya qarewa ki ce ina gaishe shi" ta qarasa fada cikin tsokana.

"Ki kira shi a waya ki gaya mishi... Ni ban gan shi ba yau"

"Ban gane ba... Yayi tafiya ne???"

"No..."

"Toh baku kira shi ba ku ji ko lafiya?"

"ba ni bace PA dinshi ai..."

"amma ke kike supervising PA din... You should have asked Basira to call him ai"

"Lallai ma Marwa... Ni zan sa a kira shi don a tambaye shi his whereabouts??? are you serious??? me ya ruwana da shi??"

"Uhm uhm Ilham... kar fa a zo wata rana wadannan maganganun naki su dawo suyi haunting dinki"

"How??? don Allah ki bari.."

Beep na incoming call ta ji a wayarta yayinda tace "hold on, incoming call bari in duba in gani"

Tana dubawa kuwa ta ga sunan shi wanda har sai da zuciyarta ta buga... Irin speak of the devil dinnan!

Da sauri ta mayar da wayar kunnen ta tace "Babe let me call you back, Ga Boss din naki yana kira na"

"Okay okay.... kar ki manta ki tambaye shi why he didn't..."

"Shut up... bye" ta fada yayinda ta tayi dropping call din Marwa tayi answering nashi.

"Assalamu alaikum" yayi mata sallama cikin muryar shi mai dadi.

Asali dai wannan kiran da yayi mata shine kira na uku tunda ta fara aiki a kamfanin. Mostly through intercom yake sa a kiran ta.. Idan baya nan ne and he needs to talk to her shine yake kira ta personal call.

"Wa'alaikumus Salam... Ina kwana Sir"

"Lafiya lau"

"Dama clients dinnan da yakamata su zo office this afternoon ne suka canza plan... they asked to meet in the next one hour at Cilantro because they have other commitments later don haka ina so ki zo da analysis dinsu sai ki duba office dina ki dauko file dinsu so we can close the deal"

Shiru ta dan yi sannan tace "Okay Sir"

"Idris driver zai jira ki a waje sai ya kawo ki"

"Okay sir"

Bayan ta kashe wayar ne na ga ta jefar a kan table dinta yayinda ranta yake a bace. Tabbas bata ji dadin change of plans din ba.

Hakan ne yasa Basira ta dago kai ta kalle ta tace "Ma, is everything okay??"

ILHAMWhere stories live. Discover now