Chapter 4

170 26 17
                                    

ASALIN YASIR USMAN BAKURA

Alhaji Muhammad Bakura da Hajiya Zulaihat Bakura asalin mutanen qaramar hukumar Bakura ne a cikin Jahar Zamfara. Asalin su fulani ne gaba da baya.

Sun kasance suna da yara biyu kacal a duniya. Usman shine babba sai qanwar shi Hafsah.

Asalin sana'ar Alhaji Muhammad Bakura Noma ne. Ya gaji sana'ar noma daga wurin kakannin shi. Dukda yayi ilimin boko mai zurfin gaske bai watsar da sana'ar ba. Bayan ya gama karatun shi ne ya shiga sana'ar da qarfi. Nan da nan ya bunqasa commercial farming din kakannin shi wato Bakura farms Nig. ltd. Ya baza manyan gonaki a garuruwa na arewacin qasar nan inda ake noma da kiwo on a large scale. Alhaji Muhammad Bakura yayi fice a fannin Commercial farming a qasar Nigeria. Gwamnatin qasa tayi alfahari da shi sossai saboda ya samar da aiki ga masu ilimi da marassa ilimi a arewanci qasar nan da dama sannan kuma yayi contributing to revenue growth na qasa from exportation.

Idan ana lissafin manyan masu arziki a arewacin Nigeria, Alhaji Muhamamd Bakura yana cikin su.

Yaran shi Usman da Hafsah sun kasance 'yan gata gaba da baya. Kyawawan gaske kamar iyayen su sannan farare sol. Sun taso suna jin yaren Fulani da Hausa sossai.

USMAN dai tunda ya gama karatun shi na sakandire a nan Nigeria ya wuce America don cigaba da karatun Jami'ar shi da Masters. Ya karanci Banking and finance a University of Stanford dake qasar America. A nan ne ya hadu da Fatima. Asalin Fatima dai 'yar Adamawa ce amma kuma a America aka haife ta a dalilin iyayen ta da suke zaune a can. Fara ce sol sannan kyakyawar gaske mai dogon gashi da qira mai kyau. Zai yi wuya ka ga mace mai kyan Fatima domin kuwa ta ko ina tayi. Mahaifin ta babban ma'aikaci ne a Bankin Duniya wato world bank dake Washington DC. A yanzu haka yana daya daga cikin manyan executives na Bankin. Suna yawan zuwa Nigeria hutu domin kuwa dangin su suna nan a cikin garin Adamawa yayinda wasu suke zaune a garin Abuja. Gaba daya dangin su babu talaka a ciki. Fatima dai ita kadai ce iyayen ta suka haifa. Sun dauki soyayyar duniya sun dora akan ta. Tun tana qarama duk abinda take so shi suke yi mata. Fatima tun da ta taso take da girman kai da ji-ji da kai. Dukda a cikin turawa take, bai hana ta nuna gadara da girman kai ba. A rayuwarta bata son talaka, bata son duk wani low class. Hakan ne ya sa bata da farin jini ko alama.

Haduwar ta da Usman a Stanford University ne. A lokacin yana shekarar shi ta qarshe a Masters yayinda ita kuma ta shigo farkon degree dinta. Fatima dai akwai manyan yara Musulmai daga qasashe daban-daban da suka nemi soyayyarta amma ta qi kallon su. Tabbas Arziki yana daya daga abinda take so a mijin aure amma kuma akwai irin yanayi da hallayar da take nema wanda gaba daya a cikin maneman nata babu mai su. A ranar da ta fara ganin Usman kuwa ranar ta ga mijin aure. Tsawon lokaci tana bibiyar shi tana karantar mu'amalar shi da mutane da komai nashi. Gaba daya yayi ticking boxes na abinda take nema a wurin namiji. For the first time ever a rayuwarta ta saukar da girman Kanta ta bi namiji don neman soyayyar shi wanda kuwa ta qudiri niyyar samu da qarfin gaske don kuwa shi kadai take so.

Abun mamaki kuwa bata sha wahalar samun soyayyar shi ba domin kuwa Fatima irin macen da kowanne namiji yake burin mallaka ce. Halin ta na wulaqanci kuwa bata nuna mishi ba tunda son shi take yi. Sossai ake mamakin yadda take girmama al'amuran Usman a Stanford. Babu shakka Soyayya shegiyar abu ce.

Tuni Usman da Fatima suka qulla soyayya mai qarfin gaske. Iyayen ta suna masifar son shi musamman ganin yadda 'yar su take son shi da kuma kasancewar shi asalin bafillatani sannan dan Nigeria.

A lokacin da Usman ya kammala masters din shi ne Mahaifin Fatima ya so ya zauna yayi aiki a nan World bank yadda idan ya auri 'yar su kawai sai su cigaba da zama a nan qasar America din tunda dai basu so tayi nisa da su amma ya qi. Dalilin shi kuwa shine ya fi so ya koma Nigeria yayi ma qasar shi aiki. this has always been his dream. Yayi ma mahaifin Fatima bayani kuma ya fahimce shi. Hakan yana nufin idan ya auri Fatima zai dauke ta ya tafi da ita Nigeria kenan. Fatima kuwa was ready to sacrifice everything for Usman domin kuwa shine rayuwarta don haka komawa Nigeria da zama was never an issue.

ILHAMWhere stories live. Discover now