Chapter 3

181 28 26
                                    

URBAN-CITY CONSTRUCTION COMPANY
ABUJA CENTRAL

A yau wuraren qarfe tara saura minti Goma na safe tana zaune a office din Nasreen yayinda take cike assumption of duty form.

Ofis din Nasreen wanda yake 4th floor dai makeke ne sannan ya masifar haduwa. Da ganin yadda aka tsara shi zaka san dole ana ji da ita a kamfanin.

Ilham dai tun jiya da suka aiko mata da saqo akan sun bata aikin ne Mummy ta dinga lallashin ta akan tayi reporting instantly amma ta kawo mata excuse cewar ta shirya schedule dinta for the day don haka sai dai ta je washegari (which is today)

Kamar wancan ranar da ta zo interview, Sanye take cikin Jallabiya wadda ta masifar yi mata kyau. Sai baza qamshi take yi yayinda fatar jikinta take ta glowing.

"Akwai terms and conditions na kamfani a next page..." Nasreen ta fada yayinda na ga Ilham ta juya page ta fara karantawa.

"Lokacin zuwa ofis latest qarfe takwas da rabi na safe sannan lokacin tashi qarfe biyar. Kina da break na awa daya a kullum sannan idan zaki fita maybe kina da personal errand dinki to run, zaki nemi permission daga wurin line manager dinki- The CEO"

"The CEO??" Ilham ta tambaya confusedly.

"Yes.. a matsayin ki ta babban Data Analyst ta kamfanin nan zakiyi aiki directly da CEO ne dukda kina under ICT Department. Duk wasu meetings da clients tare da ke za'ayi which means kina da alot of presentations to do. You are likely to stay overtime wasu lokutta don haka duk wani overtime ana converting dinshi to kudi, Ma'ana za'a biya ki. Also, the most important thing da nake so ki sani shine idan tafiya ta kama, Maybe within Nigeria har zuwa qasashen waje and your services are required tare da ke za'a je don haka ki zama a cikin shiri a koda yaushe"

"Okay..."

"Another condition da zanyi miki bayani akai shine na Goma sha daya..."

Da sauri na ga Ilham ta kalli condition number 11.

"it says babu soyayya tsakanin ma'aikata domin kuwa yana dauke musu hankali daga aikin su. Idan har kika fada soyayya da colleague dinki toh fa dole ne daya daga cikin ku yayi resigning.."

Ilham na ga tayi murmushi tace "Noted"

"Job role dinki, salary da allowances dinki da grade level dinki are all clear right??"

"Yes they are.."

"Okay then, idan baki da wata tambaya I think sai mu je in kai ki wurin CEO sannan sai in nuna miki workstation dinki. Za'a baki Macbook da duk wani gadget da kike buqata don discharging aikin ki smoothly"

*******************

Zaune yake a office dinshi yayinda yake duba wani report na wani contract da kamfanin shi yake yi a port Harcourt.

Nasreen ce ta qwanqwaso qofar ta shigo yayinda Ilham take biye da ita.

Aikuwa Ilham tana shiga office din na ga ta tsaya cak a dalilin wani qamshi mai sanyi da dadin gaske da ya bugi hancin ta.

"Yaaya... ga Data Analyst dinka na kawo maka"

Da sauri Yasir ya dago kai ya kalli Ilham wadda take tsaye a bakin qofa tana qare ma ofis dinshi kallo.

A daidai lokacin da ta kalle shi ne yayi saurin mayar da kallon shi kan Nasreen.

"thanks Sis..."

Ilham na ga tayi saurin kallon Nasreen sannan ta kalli Yasir. Sai yanzu ta kula da kama da juna da suka yi, Babu shakka qanwar shi ce.

"You are welcome, please have a seat" ya fada yayinda ya kalle ta briefly.

Ilham ta qaraso ta zauna a kujerar da take gefen ta Nasreen yayinda ta gyara murya tace "Good morning sir"

ILHAMWhere stories live. Discover now