Chapter 9

195 33 20
                                    

LATE BUKAR MAHMOUD RESIDENCE
GWARINPA

Wuraren qarfe takwas da rabi na dare Mummy tana zaune a kan 3 seater kujera na dan madaidaicin falon su yayinda Ilham take kwance a kan cinyarta tana bata labarin abinda ya faru tsakanin ta da Yasir.

Dukda falon ba babba bane, yana da kyau sossai. Ko ina tsab-tsab sai qamshi ke tashi daga ta kowanne lungu.

Ilham dai tunda ta dawo gida a yau take cike da farin ciki. Yau din ita ce rana ta farko da aikin ta na office yayi mata dadi 100%, Ba don komai ba sai don abinda ya faru tsakanin ta da Yasir. Tunda suka dawo daga Cilantro ta ji yanayin office din gaba daya ya canza saboda negative energy din da ta ajiye a gefe wanda dama Yasir din kadai take ba. Abin mamaki duk shiga Office dinshi da tayi da zarar sun hada idanuwa da shi sai ta sakar mishi murmushi.. abun har mamaki ya dinga bashi. Da ya sani cewar it's very easy to console her, he would've done so tun ranar da ta fara zuwa. Yasir dai hatta wurin meeting ya ga bambanci a yau domin kuwa gudumuwar da ta bayar ya fi na kullum yawa. Daga heads na units har clients din were impressed. Daf da za'a tashi ne Yasir ya shiga wani meeting tare da Nasreen da kuma Bilal inda suka tattauna akan wasu staff dinsu na Lagos da kuma wasu ayyukan da ake yi... Meeting din da basu gama ba har sai daf da lokacin Sallan Magrib don haka tuni Ilham ta wuce gida a lokacin.

"Na ji dadi sossai da muka shirya da shi... Wallahi aikin ma ya fi dadi yanzu. Kin san me yace mun??"

Mamy wadda take murmushi tace "tell me"

"wai idan ya qara yi mun laifi in fadi mishi ya bani haquri. Kuma ya roqe ni kar in bar aikin because he needs me... Kuma ma fa yanzu mun zama friends"

"Hmmm... Lallai Allah yayi ma ogan nan naki albarka. Gashi a dalilin shi 'ya ta is so excited and happy. Dama dai tun farko taurin kai irin naki ne ya hana kiyi mishi uzuri. "

"Wallahi Mummy har kunya na ji na yadda ya dinga bani haquri.. Boss dina fa-the CEO" Ilham ta fada cike da regret.

"Ni wannan zuciyar taki na rasa ina kika gado ta.. Ni dai ba haka nake ba, haka Daddyn ki shima ba haka yake ba.."

Ilham wadda ta fashe da dariya ce tace "toh ko wurin GM na gado??"

"ah ah wallahi... Sirika ta ba haka take ba"

"Allah sarki nayi missing dinsu... idan nayi hutu a wurin aiki zan je Maiduguri in gaishe su in sha Allah"

"aikuwa da kin kyauta.... Dazu muka yi waya da ita tace mun cewar saqo na da Sara ta aiko mun daga Chad ya biyo ta hannun ta har ma ta aika an sa mun a mota. Qila zuwa gobe su iso"

"Allah ya sa ta hado da special cleanser dina... nawa ya kusa qarewa"

"Kar ki damu tace ta hado miki da shi"

"Yauwa... Ta samo miki Dorot din da kike nema din??"

"Tace ta samo. Shi kadai nake jira a fara production gashi Turaren ya kusa qarewa a shago and I need to restock saboda na ga ana ta siya"

"Laaa na manta ma ban fadi miki ba. Na samo miki sabuwar customer"

"haba?"

"Yes Mummy, Qanwar Oga na wadda nace miki ita ce Head HR. tana ta jin qamshin turaruka na shine ta tambaye ni. Na ji tace wai a shagon ki zata hada na auren ta"

"Masha Allah... Allah ya kawo ta lafiya"

"Ameen Mummy"

"Toh yanzu dai hirar ta isa haka... tashi mu je ki ci abinci don na san idan ba na sa ki a gaba ba baza ki ci ba. Allah ya taimaka ma kwana biyu Ulcer dinki bata tashi ba"

Lazily Ilham ta tashi yayinda tace "bana wani jin yunwa fa Mummy"

"Na sani ai... wuce mu je. ko kadan ne sai kin ci. ke kam mijin ki yana da aiki. ke ba gwanar girki ba sannan baki ci. Na rasa ya zanyi da ke Ilham"

ILHAMWhere stories live. Discover now