🌸💦 MATATA GIMBIYATA💦🌸
💘 MY WIFE MY PRINCESS💘
STORY BY
JEEDDAH JA'OWRITTEN BY
FEEDOH DEEDOH
(NWA)EDITED BY
ROOKIEY KAXS9⃣➖🔟
Kawu na isa gida ya kira Ismaeel a waya, ba'a jima ba sai ga Ismaeel bayani kawu yamashi yanda sukayi da Khamees saida kawu ya nisa kana yace "Ismaeel Khamees ya rok'eni alfarman ka zauna d'ayan part d'inshi ni kuma na amsa mashi" da sauri Ismaeel ya d'ago, murmushi kawu yayi yace "karka damu Ismaeel in shaa Allah ba abinda zai samu matarka" sai a sannan yayi magana yace "to kawu gidan fa da na gina?" shiyasa nace karka damu bawai zaku zauna ba nan har abada ni da kaina zan umurceka da kukoma gidanka, ba yanda Ismaeel ya iya haka yama kawu bankwana yatashi ya fita...
Ba a d'auki lokaci ba su Kawu sukaje neman Auren Falmata, gaskia sun ga kara saboda an amshe su hannu biyu, abun har ya dinga ba Khamees mamaki, amma duk da haka tsanar Falmata na nan cikin ranshi bare da yaganta, nan su Kawu suka nemi aure kuma aka basu dangin Falmata suka yanka sadaki dubu hamsin nan take Kawu ya biya, aka tsaida biki sati hud'u da yake ko wane b'angare a shirye suke, kwanan su kawu d'aya suka dawo damaturu cike da karamcin mutan maiduguri....
Tunda Kawu ya gayama Ismaeel an bashi Falmata kuma an biya sadaki yake cikin murna, lefe ya had'a naji da gani yana kawowa gida Hadiza da Khamees sukace yayi yawa dole sai ya rage nan fa suka fara rigima har saida Kawu ya shiga maganan ya kuma hana a rage, a cewar shi kowa rabonshi yake ci dan haka baiga illar dan miji yama matarshi sutura ba, dan dole Khamees da Hadiza suka kyale lefen ba dan ransu ya so ba...Tun da bikin yazo Ismaeel baya zama, Khamees har mamaki yakeyi yanda Ismaeel ke rawan kai a bikin nan Hadiza tace "ba dole yayi rawar kai ba tun da ya auro mana dangin asiri" ba ayi wani event ba kasancewar Falmata bata san wani event ko d'aya ba yanda Ismaeel ya iya walima kawai sukayi, ranan juma'a aka d'aura aure ana gama d'aura aure aka taho da amarya damaturu, kwanan yan kai amarya d'aya dama turu suka juya maiduguri....
Hadiza ce tsaye bakin k'ofa tana kwalama Falmata kira ke! Da sauri ya fito kallonta tayi shek'ek'e tace "wakika aje da zai maki gyaran gidan? Dallah fito malama kifara aikinki kina tunanin hutu kika zoyi to bauta kikazo yi" bata ce komai ba ta bita sharan gidan tafarayi tana gamawa ta d'ora girkin kitchen Ismaeel ya tarda ta nan fa yafara masifa, kallonshi tayi da murmushi tace "karkadamu mijina bautan aure nakeyi dan Allah karka masu magana kaga gaba suke damu dole mu bisu". Tunda nazo gidan nan nagane Anty Hadiza da ya Khamees basu sona amma kullum burina na kyautata masu harta Saeed sun dasa mashi k'iyayyata, kwantowa yayi bisa jikinta yace "kiyi hak'uri in shaa Allah kwana kad'an zamu koma gidanmu" murmushi tayi ta cigaba da aiki..Tunda Falmata ta samu ciki take fama da laulayi kullum cikin amai take, amma duk da haka dole sai tayi aiki ba abinda ta dainayi, kullum kuma cikin kwantarma Ismaeel take da hankali akan karya damu..
Wata tara cif ta sankato d'iyarta mai kama da ita, tunda aka haifeta Ismaeel yake cikin farin ciki, a yayinda Khamees da Hadiza ke cikin bakin ciki..Ranan suna yarinya taci suna DEENAH bayan suna Ismaeel duka k'adarorinshi ya maidasu sunan Deenah, nan fa hankalin Khamees da Hadiza ya tashi, babu yanda basuyi ba dan suga sun kauda Deenah daga dunia amma Allah bai basu iko ba, watanni biyu da haihuwan Deenah Hadiza ta k'ara haihuwa itama tasamu mace ranan suna aka sama yarinya ummul Khairi..
Tunda Deenah ta taso cikin so da k'aunar iyayenta komai suka samu ita da zaran ta fita sai tadawo da kuka saboda Saeed zalintar ta yakeyi kuma ba'a hanashi kullum cikin gallaza mata sukeyi har takai ga bata fita saboda da ta fita sai tadawo da kuka tun abun na damun Ismaeel har yakai ga ya hak'ura,Haka rayuwa ta cigaba da tafiya kullum da azabar dasu Khairee kema Deenah,
BAYAN SHEKARA BIYAR
Zaune suke parlor suna fira da gudu ta shigo tana kuka, jawota yayi jikinshi ya rungume yace "Deenah kiyi hak'uri da irin abinda zaki gani gidannan kinji ko watarana sai ya zama labari" hawayenta ta goge tace "Daddy miyasa su Uncle suka tsaneni?" Bafa mai sona cikin su, Falmata tace "ba tsanarki sukai ba kinji ko" daina kuka, tashi mu raka babanki ke yake jira dama kidawo tafiya zaiyi...
Har wajen mota suka rakashi, yana shiga mota sai kuma ya fito shafa kan Deenah yayi ya kalleta yace "my dota ki tsaya kiyi karatu in shaa Allah duniya sai tayi alfahari dake" d'aga kanta tayi tana hawaye, kallon Falmata yayi yace "ga amanar Deenah nan nabari a hannunki dan Allah ki bata ilimi" ita kanta hawaye takeyi tace "in shaa Allah saika rayu da Deenah", girgiza kai yayi ya juya ya tafi bud'e mota yayi sai kuma ya k'ara juyowa shima hawaye ya keyi, hawayen ya share kana ya shiga mota, d'aga mashi hannu sukeyi har saida yafita tunda yatafi Falmata ke kuka wanda ta rasa dalilin yinshi....
Kad'an kad'an Falmata zata duba wayanta, ga bugun k'irji da takeji number d'in Ismaeel tayi try amma sai tajita kashe, k'irjinta ne ya cigaba da bugawa, kamar daga sama taji kuka da sauri ta tashi ta saka hijab taja hannun Deenah suka fita......© M@J@H
F💘J💘R💘
VOCÊ ESTÁ LENDO
MATATA GIMBIYATA
Não FicçãoAttitude miss DEENAH ISMAEEL!! am talking to you right here as a father! Idan da uban ki ne yayi wannan maganar ai babu musu zaki yarda , amma dayake ni kin raina min wayau tunda ba ni na haife ki ba ,shine bari ki nuna min halin ki na y'an duniya k...