🌸💦MATATA GIMBIYATA💦🌸
💘MY WIFE MY PRINCESS💘
STORY BY
JEEDDAH JA'OWRITTEN BY
FEEDOH DEEDOH
(NWA)EDITED BY
ROOKIEY KAXS1⃣3⃣➖1⃣4⃣
Back to story........
A kasalance na fito daga d'aki gabana se dukan uku uku yake duk Allah Allah nake kar in had'a ido da Mr Sadiq Imam , doguwar riga ce ta atamfa wanda na ci karo da shi cikin wardrobe na saka , wani ikon Allah kamar an gwada akayi dinkin. Yayinda nake saukowa daga stairs d'in ina iya hango mutum zaune a dining section na makeken living room d'in,
Gosh !! A lokaci guda na kasa d'auke idanuwa na daga gareshi yayinda yake taunar fried potato chips wanda yasha tomato ketchup , the man is breathtaking and charming physically! Allah kad'ai yasan dalilin bacin ransa da mata! Ko me ma ya dawo dashi paralyzed? Oho?.......
Ba kamar yadda kike tunani bane cewa am paralyzed! tajiyo husky voice nashi ya doki kunnen ta, ya dawo da hannayen sa kan control na wheelchair d'in ya waigo yana facing inda take yaci gaba da fad'in
Zaifi miki sauk'i kada kiyi shishigi! Aikin ki a gidan nan bai wuce shara da goge goge ba! Shima kuma na d'auke miki flat d'ina so all i want from you is stay away from me! Kada ki dinga yin garajen had'a ido da ni, also am not interested in your helping hand, zan iya yin komai da kaina tunda Allah ya hore min hannu i don't need anybody's help! Shishigi dai ina dad'a jan kunnen ki akai And don't worry I'll pay you, your salary starting from this month idan hakan yayi miki zaki iya zuwa ki karya, and also Young lady for your information akwai kwararriyar Nutritionist a gida ba se kin yi girki ba am not sure ma zaki iya aiki da appliances d'in so gudun karkiyi wa kanki asarar mummunan fuskar nan zai fi miki kar ki yi garajen girki...Na dad'e a tsaye baki a bud'e cike da mamaki, ko da nake zaman wahala ban tab'a ganin mara mutunci irin Mr Imam ba ,shi d'in na daban ne, Wato ma y'ar k'auye ya maida ni? Ai kuwa ban san lokacin da hawaye suka soma gangarowa ba, na koma d'aki da gudu.
Fad'awa kan gado nayi nace "daman haka auren yake?" Wannan tozarcin shine sauran mata ke fuskanta? Kodai ni d'in ce kawai? Wannan wace irin kaddara ce?..Nikima tawa k'addaran haka tazo, lallai rashin iyaye ba k'aramin abu baneba hawayen da suka gangaro man ne na share su, Nasihar Mahaifiyata na tuna "inda take ceman Deenah kiyi hak'uri da duk irin abinda zaki gani a dunia, in shaa Allah watarana zaki dariya...."
Toh yaushe ne zanyi dariyan? Tambayan da banda amsar ta, murmushi nayi in shaa Allah zan jure kowace matsala ce daga wajen wanda ake kirana mijina, dan gaskiya banga k'iyayya ta a idonshi ba kamar yanda na ganta a idon su Saeed, akwai dai abinda mace ta mashi yasa ya tsani mata, koma miye a sannu zan sanshi kuma saina kauda mashi tunanin duk mata haka muke, saina canja mashi ra'ayi...Murmushi nayi na tashi dan naje na karya, ina isa downstaire na ganshi yana k'ok'arin tura wheelchair zai d'auko ruwa, da sauri na isa wajenshi na turashi yana d'auko ruwan daidai muna had'a ido wata zabura da yayi ya dakaman tsawa saida na kusa fitsari, ruwan ya watsoman bansan sanda na saki k'ara ba na duk'e k'asa...
Wace irin jakka ce ke? Banace bansan taimakon ki ba? i don't need anybodys help, Angaya maki banda hannu ne? Tun yanzu kenan ba'a je ko ina ba kin fara karyaman doka, hmmmm mata duk halinku d'aya na tsaneku wannan ya zama na k'arshe da zaki shiga harkata, dan haka get out from here, kasa tashi nayi saboda tsabar razana nayi, da k'arfi ya k'ara maimaitawa a said get out da gudu na tashi na haye sama ina kuka...Ina shiga d'aki na banko k'ofa kan gado na fad'a ina kuka, ni kuma haka tawa k'addaran take? Mutuwa bakiman adalci ba, inda iyayena na da rai bazasu barni na tozarta ba, ganin kukan baiman magani ya sa na shiga toilet na d'auro Alwalla nazo na tada sallah ina gamawa na d'aga hannu sama nafara adua neman nasara ina gamawa inda nayi sallah nan bacci ya kwasheni.....
Don't forget to hit dat orange🌟 tnx y'all
© M@J@H
F💘J💘R💘
VOCÊ ESTÁ LENDO
MATATA GIMBIYATA
Não FicçãoAttitude miss DEENAH ISMAEEL!! am talking to you right here as a father! Idan da uban ki ne yayi wannan maganar ai babu musu zaki yarda , amma dayake ni kin raina min wayau tunda ba ni na haife ki ba ,shine bari ki nuna min halin ki na y'an duniya k...