🌸💦MATATA GIMBIYATA💦🌸
💘MY WIFE MY PRINCESS💘
STORY BY
JEEDDAH JA'OWRITTEN BY
FEEDOH DEEDOH
(NWA)EDITED BY
ROOKIEY KAXS5⃣1⃣➖5⃣2⃣
I miss our conversation, i miss how we used to talk every minute of every day nd how i was able to tell you everything dat was on my mind. I miss you so much Maama💔 may Allah grant you jannatul firdausi Amin👏🏻
Alama yayi wa Sadeeya kan ta tafi, sannan ya k'arasa inda take zaune yayi facing d'in ta. Hannunta ya rik'e sannan da kyar ,murya ciki ciki yace
"Ko ba komai yau naga me k'auna ta tsakani da Allah ba dan ganin ido ba. Deenah na rik'e Hajiya tamkar mahaifiya domin tun ina k'arami take tare da ni, lokacin da mahaifiyata bata da lafiya, ganin yadda muka shak'u da Ummah Nah ta bar mata ni, duk wata kulawa ta takoma hannunta har na girma na zama mutum. Deenah Hajiyar da na sani da ba ita ce yanzu ba, wancan bata iya cin abinci har sai naci, bata barci in bani da lafiya sannan ko kad'an bata k'auna taga na kasa ko wani abu makamancin haka amma wai yau nine Hajiya take son taga na nakasa, Hajiya ce take son gani na a wahale?
Deenah nayi nadamar kasancewa k'ark'ashin kulawar ta tun farko! Gaskiyar mutane sukace ba'a tab'a yin Uwa biyu, Lallai wanda ta durk'usa ta haifen ita kad'ai ta san ciwo na, da ace wani ne ya fad'a min wallahi Deenah bazan tab'a amince wa ba amma yau da kunnena naji, amma na gode Allah da asirin su ya tonu yau.
Bazan musu magana ba amma ki min alk'awarin zaki sa ido a Kansu har na dawo, promise me pls"Kai Deenah ta gyada sannan tace
"In Allah ya yarda na maka alk'awari zan kula."Godiya yai mata sannan yace
"ta kai shi d'aki ba musu ta mik'e kamar wanda ruwa yayi ma duka ta tura shi d'aki. Taya shi tayi ya kwanta sannan ta kashe masa wuta, amma ganin yanayin da yake ciki yasa ta yanke shawarar kwana tare da shiZagaya wa tayi ta haye gadon ta kwanta ga duhu dan wuta a kashe yake sai hasken farin wata daga window da ya ratso har gadon hakan ya bata daman ganin irin k'uncin da Sadeeq Ke ciki wanda har lokaci hawaye yake yi yayinda yake kwance rigingine.
Matsawa tayi kusa dashi ta saka hannun ta cikin nashi ta matse.
Murmushi yayi sannan ya janyo ta jikin shi
yace
"gud nyt"
ita ma hakan ta fad'a masa sannan ta d'an d'ago ta dubi fuskarshi taga ya lumshe ido a zaton ta bacci yake yi a hankali ta maida kanta k'irjin shi ta yi lakaf har bacci ya d'auke ta........K'iran sallar fari Deenah ta bud'e idanuwa, ko da ta tashi Sadeeq baya kan gadon amma ta jiyo k'aran ruwa a bathroom dan haka ta fahimci yana bathroom ne dan haka ta mik'e tana mik'a karaf idanuwan ta suka sauk'a kan wheelchair d'in shi cike da mamaki ta Zaro idanuwa
tace
"Yaya kuma ya iya shiga bathroom ba tare da keken shi ba? Toh ko dai bango ya bi? Amma ta Yaya zai iya mik'e wa in har spine nashi ne keda problem? Ko da yake babu yadda Allah bayayi da bawan sa"
Ita kad'ai dai take ta sak'e sak'e tana tambayar kanta kuma ta bada amsa.Bata ankara ba taji har ana neman shiga sallah da wuri ta juya zata fice se taji k'arar bud'e k'ofa dan haka ta juya da sauri ai kuwa nan idanuwan ta suka yi arba da abunda bata yi zato ba bare tsammani baki ta sake ta kasa ko motsi
Tsaye yayi bakin k'ofar yana goge fuskar shi da towel ,duk da yaga yadda ta girgiza bai wani damu ba ya wuce ta ya nufi wadrobe ya d'auko jallabiyar shi brown ya zira sannan ya rataya mata towel d'in a kafad'ar ta ya kashe mata ido d'aya ya fice ta wannan k'ofar wanda sai a ranar Deenah ta san da zaman Wannan k'ofar ita dai gaba d'aya ta kasa fahimtar komai amma da yake tasan in ya dawo zai amsa query kawai ta nufi flat nata tayi alwala tayi sallah sannan kamar kullum ta d'auki Qur'an tana karatu...........
ESTÁS LEYENDO
MATATA GIMBIYATA
No FicciónAttitude miss DEENAH ISMAEEL!! am talking to you right here as a father! Idan da uban ki ne yayi wannan maganar ai babu musu zaki yarda , amma dayake ni kin raina min wayau tunda ba ni na haife ki ba ,shine bari ki nuna min halin ki na y'an duniya k...