🌸💦MATATA GIMBIYATA💦🌸
💘MY WIFE MY PRINCESS💘
STORY BY
JEEDDAH JA'OWRITTEN BY
FEEDOH DEEDOH
(NWA)EDITED BY
ROOKIEY KAXS2⃣3⃣➖2⃣4⃣
"Yaya me kace?"
Ta tambaya fuska a dak'ile tana tsaye still bata matsa ba.
Uhh.... Ammm... Heeyy Ramlah! Ban San ma har kun iso ba how was your journey?
"Inna Umma fa?"
Ya tambaya sai Kame Kame yake kamar munafuki Ramlah ta juya idanuwan ta sannan ta bar d'akin tana fad'in
"Yaushe y'ar aiki ta samu gindin zama a gidan nan? Har zata tako d'akin Yaya sannan har ta fad'a mishi maganganun da ranta yake so?"
Bayan La'asar Mr Imam na zaune ya rasa abun yi don haka ya d'auki wayar shi ya yi dialling numbern Aminin shi Dr Bilal
"Assalamu Alaikum"
"Wa'alaikumus-salam"
"Dama ina san ganinka ne"
Shiru yayi jim
"No Dr babu wata matsala kawai dai ina so mu had'u yanzu its urgent"
bai jira me Dr zai ce ba ya ajiye wayar gami da tura wheelchair d'in zuwa bathroom bayan Kusan mintina goma ya fito amma guess what readers?Daga ni Feedoh har Jeeddah Jao Saida muka Kusan sumewa dan ganin Mr Imam a tsaye gar kamar bai tab'a zama kan wheelchair ba ,sanye da dakakkiyar shadda fara Sol half jumper ta sha aiki ga kan nan yasha gyara ga hula ya kafa oh my gosh Readers Imam is a full option ,da faffad'an k'irjin shi ya tsaya gaban mirror yana gyara zaman rigar shi gami da feshe jikin shi da tsadaddun turaruka kafin ya juya ya kwashi wayoyin sa guda biyu ya bud'e wata k'ofa tsakanin windows nashi ya fice.
Shi kam ya fice amma fa daga gefe na kasa ko motsi, ya bar ni da tunani daban daban a kai na. Ko ku ma readers nasan tambayoyin ku a nan bai wuce irin nawa ba
Daman Mr Imam ba gurgu bane? Ko kuma dai yanzun nan kawai yaji ya warke? What game is he playing Kuma me yasa?
Hmmmm kudai kuciga ba da binmu zamu warware maku komi
Deenah ce zaune kan sallaya zuciyar ta cike da nadamar maganganun da ta fad'a masa can wata zuciyar tace
"come on"
"rabu da shi kin yi daidai ai bazaki bari ana cin kashi a kanki ba barshi kawai ya k'arata shi kad'ai kuma maganin ma bazaki kai masa ba"Har wani cije leb'en ta tayi sannan ta mik'e ta bar falo zuwa d'akin Sadeeya gudun kar yan masifar nan su iske ta.
Zaune ta iske Sadeeya tace
"Dan Allah kama Mani kai na Sadeeya"
ba musu Sadeeya ta hau stool ta fara mata kitso Deenah tace
"Sam sai dai a mata manya"
Da kyar ta yarda a mata k'anana shima da sharad'i Sadeeya zata yi tsifa haka suka yi ta hirar su har lokacin La'asar tayi suka yi sallah. Sadeeya ta mik'e da wuri tana fad'in"Hmm barin tashi na tambayi Hajiya me zan dafa".
Cikin rashin fahimta Deenah tace
"kamar Yaya kuma? Ki tambayi Hajiya naga akwai time table a kitchen komai a tsare yake har se kin je wajen su kin ja wa kan Ki zagi?".
Murmushi Sadeeya tayi kafin tace
"Madam kenan kin ganni nan yau shekara d'ai d'ai har goma sha biyu ina aiki a wannan gidan, babu irin halayen su da ban sani ba, zagi kam na saba da shi ,kin gani kaf masu aiki guda shida na wannan gidan ni kad'ai ce na saura harta masu wanki da gadi an canja sun fi a k'irga duk sanadiyyar wannan matar, haka yar ta tun tana k'arama babu irin taka mutane da bata sani ba, kuma duk wanda ya kuskura ya sab'a mata doka daga ta fara kukan munafurci Oga zai waje da ita, in tak'aita miki ya fi k'aunar ta akan rayuwar shi, saidai ita banga alamar tana k'aunar sa irin haka ba. Babu wanda tayi maganin su har ta koresu daga gidan se Zee "
"Wacece Zee?"
Deenah ta tambaya
"Matar Oga ce ta fari."
Sadeeya ta bata amsa a tak'aice tace
"Madam"
bari kiga in je kar na shiga magana don abun magana baya musu kad'an.........
Tana ficewa Deenah ta had'e rai tace
"wato ma har wata matar gareshi?"
taja k'aramin tsaki gami da mik'e wa kan gadon Sadeeya tana buga game......Vote
Comments
Follow nd
Share
CZYTASZ
MATATA GIMBIYATA
Literatura FaktuAttitude miss DEENAH ISMAEEL!! am talking to you right here as a father! Idan da uban ki ne yayi wannan maganar ai babu musu zaki yarda , amma dayake ni kin raina min wayau tunda ba ni na haife ki ba ,shine bari ki nuna min halin ki na y'an duniya k...