🌸💦MATATA GIMBIYATA💦🌸
💘MY WIFE MY PRINCESS💘
STORY BY
JEEDDAH JA'OWRITTEN BY
FEEDOH DEEDOH
(NWA)EDITED BY
ROOKIEY KAXS2⃣5⃣➖2⃣6⃣
Tuk'i yake tamkar baya son yi babu abunda yake tunawa sai maganganun Deenah, bai ankara ba ya kusa Buga wa wata mota da kyar ya yi controlling motar shi , motar ta mutu kuma tak'i tashi ya rasa yadda zai yi dan haka ya fito ya doki tayan motar da kaf'an shi cike da jin haushi ya ce
"Oohhhh! Deenah get out of my head!!"
Nan ya Zaro waya ya k'ira Bilal yace
"Kawai mu had'u a d'ayan gida na coz mota na ya tsaya bazan iya k'araso wa office nawa ba"
ba tare da b'ata lokaci ba ya kashe wayar gami da tsayar da taxi ya masa kwatancen inda zashi ,Kusan a tare suka iso ma da Bilal dan haka suka wuce garden dan tattaunawa.
"Bilal am having a feeling kamar Ina takura ma Deenah da yawa, and its not good saboda zata iya tsana ta in the process, tunda tazo bata tab'a tsallake magana ta ba kuma to tell you the truth Bilal am in luv wit Deenah"
Da sauri Bilal ya d'ago kai yace
"I know my Frnd but bana so kayi giving in da wuri duba da yadda Zee tayi treating naka after irin love d'in dake tsakanin ku! It's time ka rage muzanta wa Deenah but don't ever give in!"Shiru Mr Imam yayi yace
"Thanks for your advice"
nan suka tab'a hira sannan Bilal yayi masa sallama ya tafi.
Kan shi ya jingina a kujeran da yake zaune ya lumshe idanuwa tunanin abubuwan da yayi wa Deenah yake ta yi chan ya bud'e ido yace
"'''MATATA,GIMBIYATA''' "
har Yaushe zamu cigaba da kasance wa haka? Yaushe zan fitar miki da gaskiya ta? I don't want to keep hurting you further am sorry......*********** *********
"Wai waye Ke doka mana sallama haka kamar limami sabon d'auka"?
Muryar Hajiya ne ya Faso har kunnen Sadeeya wanda ta kai minti goma sha biyar a wajen babu wanda ya amsa yanzun ma dan sunga dama ne shiyasa.
Murya na rawa tace
"nice Sadeeya daman zan tambaya ne ko da abunda za'a d'aura for dinner"
tsaki Hajiya ta ja sannan tace
"a buga sakwara da miyan egusi da bitter leaf"
"An Gama Hajiya"
Cewar Sadeeya Tana yamutsa fuska kamar zata yi kuka ta sauko ta fara kici kicin d'aura tukunya Deenah ma ta fito taya ta dan aikin zai fi sauri.Buga sakwara take tana gumi Amma da yake dama can ta saba da wuya sam bata damu ba.
Cikin k'ananan kayan sa ba k'aramin kyau yayi ba shaved and clean ga wani k'amshi dake tashi, direct kitchen d'in ya zuba wa ido Deenah bata ma san yana yi ba har ta gama ta kwashe Sannan ta fito tana goge hannu da kitchen towel karaf idanuwan su suka had'e da sauri ta kawar da kanta gefe sannan ta nufi hanyar d'akin Sadeeya.....
Shu'umin Murmushi yayi da gangan ya fad'o daga wheelchair d'in, da gudu ta juyo haka ma Sadeeya. Sadeeya ta d'ago wheelchair d'in Deenah ta fara k'ok'arin d'aga shi ,da gangan ya sake jikin sa sai kokawa take yi amma ta kasa Saida yaga tayi laushi sannan ya bari ta maida shi se haki take yi.
Ko da ta mik'e jiri ne ya kwashe ta, sulalewa tayi zata zube ya chafke hannun ta gami da janyo ta jikin sa ,yana k'arema fuskar ta kallo cike da damuwa kafin kace me Sadeeya ta kawo ruwa ya yayyafa mata..
A firgice ta tashi gamida fizge jikin ta tana rik'e kanta idanuwan su cikin na juna.
Juya wa take k'ok'arin yi amma ta kasa d'aga k'afa tana Tsoron kar jiri ya sake d'iban ta dan haka ta dafa cushion dake gefen ta, Mr Imam ya gane bata son ma su had'a ido dan haka yayi wa Sadeeya ido. Da sauri ta kama Deenah ta kaita d'akin ta.
Murmushi yayi ya k'arasa dinning table ya zauna yayi Shiru sai ji yayi an dafa kafad'ar sa babu shiri ya juya tuni ya saki wata kyakkyawan Murmushi wanda ban tab'a ganin shi da irin ta ba. Kujera ta ja kusa da shi ta zauna tana kallon shi with much concern ta nisa sannan tace
"Tunanin me kake yi d'ana? A wannan condition d'in da kake ciki tunani ba naka bane just zero your mind"
y'ar guntuwar dariya ya saka yana d'ago kai karaf idanuwan sa kan Deenah wanda take k'ok'arin ficewa daga falon nan ya bita da kallo ya manta Hajiya a gefen shi. Hajiya ganin ya maida hankalin shi waje guda hakan yasa ta juya a ranta tace "so wancan mai k'afa kamar brugalin miyan ita kake kallo har ka iya mantawa da ina wajen? Ai kuwa zan yi maganin Ki dan ko Zee da ta gaji bala'i ma bata sa hankalin shi gushe wa ba a gaba na sai ke"
"Ke!"
Hajiya ta daka ma Deenah tsawa ba shiri ta juyo bata zame ba sai a gaban Hajiya.
"Oh Allah naga ta kaina"
shin iyayen Ki basu koya miki ladabi bane? "Cikin jin haushi Deenah ta ce
"Barka da yamma Hajiya"
sannan ta kawar da kai Ashe hakan ya bak'anta ran Mr Imam basu ankara ba sai ganin glasses suka yi a k'asa fasassu daga Deenah har ita Hajiyar sun tsorata ya sa hannu ya fisgo Deenah hakan yasa ta zube kan gwiwar ta sannan ya chafke gashin ta wanda yasa ta saki k'ara , cikin tsananin b'acin rai yana huci yace
"How dare you! Even think of greeting her in such a manner? Haka zakiyi wa Uwar Ki ? Lemme get this clear to you babu mai taka min uwa dan nasan darajar ta"
yana kai nan ya wurga Deenah kan fasassun glasses d'in sannan ya tura keken shi zuwa d'akin shi sai lokacin dan munafurci Hajiya ta fara k'iran shi
"Baba na! Pls calm down bana so kana tada hankalin ka kai da ba cikakken lafiya gareka ba"
ko kulata bai ba ya banko k'ofar side nashi ya wuce bedroom nashi kai tsaye.
Deenah dake fama da kanta ,baka jin komai se sautin kukan ta mai ratsa zuciya bata ankara ba ta ji muryar Hajiya a kanta tace
"Hmm! Zuwa yanzu dai kam nasan kin fahimci k'arfin iko na a wannan gidan, babu mai taka ni saboda haka Ki bi a hankali"
Duk abunda ake yi Sadeeya na zaune kan floor a kitchen tana hawaye, Hajiya na ficewa ta fito ta d'aga Deenah zuwa d'aki sannan ta dawo tana kwashe mess d'in da Mr Imam yayi zuciyar ta cike da tausayin Deenah ................Don't forget to vote, comments nd follow❤
ESTÁS LEYENDO
MATATA GIMBIYATA
No FicciónAttitude miss DEENAH ISMAEEL!! am talking to you right here as a father! Idan da uban ki ne yayi wannan maganar ai babu musu zaki yarda , amma dayake ni kin raina min wayau tunda ba ni na haife ki ba ,shine bari ki nuna min halin ki na y'an duniya k...