*NAGARTA WRITERS ASSOCIATION*
Assalamu alaikum warahmatullah!
Barka da warhaka, da fatan dukkaninku kuna lafiya? Bayan haka, ƙungiyar nan mai suna a sama, na farin cikin shaida wa ɗaukacin masoyanta, ma'abota bibiyar rubututtukan 'ya'yanta, har ma da wanda ba su ta6a bibiyar ba amma suna da ra'ayi, cewa sun samo muku hanya mafi sauƙi wacce za ku samu labaransu.
Hanya ce wacce babu batun zuwa wani group kina jajen ci gaban wani littafi, ko kuma wani shafi kin rasa shi bayan kuma kin ɗauko jin daɗin karatunsa. A wannan sabuwar hanyar tamu, baki ɗaya littafinmu za ku same shi, ku karanta ba tare da jaje ba bare har a share ku idan kun nema. Idan har kuka fara karantawa to sai dai idan wani uzuri zai tsayar da ke ki ajje karatun. Daga gare mu dai kam, cikakken littafi ne za ku samu.
Hanyar da za ku bi ita ce;
Ku je *play store,* kai tsaye wurin searching za ku rubuta *Nagarta Writers,* za ku ga manhajarmu (application) ya 6ullo, sai ku danna install, a sauƙaƙe, ba ya da wani nauyin da zai zuƙe muku data.
Bayan ya gama duka, sai ku shiga a cikinsa. Za ku ga *categories* na littattafanmu baki ɗaya. Sai ku zaɓi category ɗin da kuke son dubawa, misali kina son karatun horror, a categories ɗin za ku ga horror sai ku shiga. Za ku ga littattafai sai ku za6i wanda kuke so.
Ba a nan kaɗai abun ya tsaya ba, a kusa da categories akwai inda *Authors* yake, sai ku shiga. Za ku ga jerin members na nagarta, sai ku za6i sunan wacce kuke son karanta littafinta.
Haka kuma, akwai wurin searching daga can sama, za ku iya saka #tag na littafin ko kuma sunansa, ko sunan marubuciyar, za ku ga ya ɓullo sai kawai ku shige.
Zaku iya adana littafin a ma'adanar app din, wato saved da ke rubuce, dan saukin samun littafin da kike kan karantawa.
Wannan wata hanya ce mai sauƙin gaske, wacce muke fatan dukkanin masoyanmu na gaskiya za su ji daɗinta. Za kuma su yi alfahari da wannan ci-gaba da muka samu.
Daga yanzu ba za ku sake samun wani sabon littafinmu a whatsapp ba, sai dai wanda suka riga da suka fara ne za su ƙarasa shi a nan. Daga nan kuma sai dai a app namu insha Allah.
Mun gode sosai da soyayya.
Mun gode da bibiyar labaranmu.
Muna tare da ku a kodayaushe.Ga link na app namu dan saukin isa ga manhajar:-
https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.com.nagarta
Signed by NWA OFFICIALS
Nagarta writers association
About Nagarta App
https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.com.nagartaMasu anfani da wayoyin Android OS version 6.0 and above ne kadai zasu iya installing akan wayarsu.
Wanda version nasa ke kasa da hakan playstore zai sanar da shi not compatible, wanda hakan na nufin sai ka yi updating wayarka zuwa sabuwar version nasu.
Ba laifinmu bane, doka ne daga playstore, a yi hakuri da hakan.
Bayan anyi downloading manhajar a kan waya a ka shiga ciki, a sama, bayan logo, Nagarta story ne rubuce, sai wurin nema wato Search, gefensa kuma settings, daga karshe kuma digo uku zaka gani a jere, wanda a nan ne zaka iya sanar da abokai da 'yan uwa game da application namu, ko kuma dan ajiye mana sako cikin sauki.
A kasa kuwa, zaku ga Browse da recommended. Sai All da kuma jerin categories a kasa.
A takaice wannan shafin ya kunshi dukkan abunda application din ya kunsa.Daga karshe a kasa, zaku ci karo da Home, inda dukkan rubutun da na ambato yake kenan, daga gefensa akwai Authors, ma'ana Marubutan manhajar. Idan ka danna zaka ga all ta sama, gefensa zaka ga jerin sunayen Marubuta Nagarta, daga Shugaba Benaxir Omar, zuwa ga na'ibarta Lubbatu Maitafsir sai sauran officials da members.
A nan zaki iya zabar gwanarki, wanda kowacce littafanta na kasan sunanta idan kika taba.
Daga Authors sai categories, su ma kaman sunayen suke a jere, Romance, historical fiction da dai sauransu. Dukkan wanda kuka zaba zaku ga littafansu a karkashinsu.
Daga nan sai Saved, ma'ana ma'adani, wato wurin da littafan da ka ajje domin karatu zasu zauna.
Daga karshe sai User, wurin yin register dan samun daman comment da voting.
A kowani littafi da zaku shiga akwai summary, tsokaci ko abunda littafin ya kunsa.
Idan kuna son sanar da 'yan uwa littafin da ka karanta dan su ma su karanta, bayan ka shiga cikin littafin, zaku ga alamar share a gefen dama, wanda in kuka danna zai tambayi inda zaka tura, whatsapp ne, ko Facebook ko wani app na daban.
Za a dauki summaryn littafin, da link na littafin a tura dan meshi ya samu saukin samu.
Daga karshe, bayan ka daura Application a kan wayarka, duk lokacin da a ka daura sabon littafi zaku samu sanarwa (notification) a saman wayarka, za a sanar da kai littafi kaza, daga marubuci kaza ya daura littafi cikin category kaza, sai ka danna ka shiga ciki kai tsaye don shan karatu.
Manhajarmu a yanzu playstore kawai yake, masu anfani da Iphone zasu iya shiga website namu kamar haka;-
www.nagartawriters.com.ng
Dukkan abunda yake app zaka samu a nan, sai dai saving littafi ne kawai bazaka iya ba.
A tuntubi wadan nan lambobin dan karin bayani, tsokaci, da duk wani abunda yakamata mu sani:-
08088929221
07037603276Babu Nagarta idan babu makaranta.
Mungode!
YOU ARE READING
MATATA GIMBIYATA
Non-FictionAttitude miss DEENAH ISMAEEL!! am talking to you right here as a father! Idan da uban ki ne yayi wannan maganar ai babu musu zaki yarda , amma dayake ni kin raina min wayau tunda ba ni na haife ki ba ,shine bari ki nuna min halin ki na y'an duniya k...