AKAN RAGON LAYYA 2

735 31 0
                                    

🐑
🐑🐑
🐑🐑🐑
   AKAN RAGON LAYYA.
                        🐑
                         🐑🐑
                          🐑🐑🐑

®NWA.


Feedoh... Zuciya ta
My Zahra....lovely Aunty
Stylish.... Besty

By
Real Autarhajiya

Page 2.

Bayan kwana d'aya

GIDAN  ZAINAB

Zaune take a tsakar gida  tana jiran maigidan nata da yace mata zaiyi LAYYA.
Bata son sanyi amma gashi AKAN RAGON LAYYA ta zauna har biyar na yamma a waje.
Da sallama ya shigo fuskar sa a washe yana jin farin ciki da sauri ta mike zata masa oyoyo amma ganin ba leda barw uban gayyar wato RAGo yasaka ta koma gefe amma me cukus ya tarar da fuskar matar tasa kamar alkubs wanda yake hawa a yanzu.
Rayuwa ta kin yini lafiya?, da banyi ni ai bazaka ganni ba.... Mene haka kuma?, before everything dai yanaga banga turke ba bare RAGON LAYYA...gobe fa sallah idan ban ganshi yau ba sai tsakar dare ko kuma da safe zakaje ka siyo?.
Zainab waike bakida hankali ki ringa abu da tunani mana halan ni talaka ne ko mai k'aramin k'arfi da zaki ringa gayan magana anyhow AKAN RAGON LAYYA enough Malama ban tolerating wannan sabon halin naki idan nace banyi kin isa kisani dole?.
Eh lallai Mohd bance kai talaka bane amma alama nagani nason ka nuna halin talakawan azumi ne a bakina amma banga sabon abuba wanda zanyi bud'e baki da shi kasan Allah LAYYA ce sai kayi Zuwairat k'awata  RAGON LAYYA guda biyu tace mijin ta ya sai musu sai ni.
Tass Mohd ya saukewa Zainab mari a fuskar ta wanda ya gigitata...ke shashasha nagaji da abinda kike yi LAYYA dole ce ko kinga safiya tayi naje idi na dawo baki ganni da Rago ba chaiii mata sai abar ku.
Wallahi bazan yadda ba tunda ka mareni kamari auren ka AKAN RAGON LAYYA shine harda zuban mari?.
Fuuu tai d'aki...shikam k'ik'am ya tsaya "Inalillahi me yasa zan haka mata fa k'aramar brain garesu meyasa banyi mata bayani ba akan zanyi LAYYA gashi na mari abar k'aunata daga magana AKAN RAGON LAYYA Allah ya kayafeni.
Mayafi ya ganta dashi sai jakar ta tazo ta wuce shi...da sauri yabi bayan ta Zainab...Zainab dan Allah kiyi hak'uri wallahi nasan nai kuskure na marin ki danayi amma baikamata ace AKAN RAGON LAYYA ba zakiyi yaji gobe sallah fa....Ina ko sauraran sa batai ba saima Napep data tare ta shige sai gida.
"A'a zainabu ce haka da wannan yamman ina kika baro mijin naki ayi azumi amma ku fito ba kusha ruwa ba?".
"Baba ai ni nabar Mohd wallahi nagama auren sa. Inalillahi kamar yaya meya faru? Mari na yai. Mari?akan me? AKAN RAGON LAYYA.
AKAN RAGON LAYYA kamar yaya? Baba wai ace tsakani da Allah Mohd bazaiyi LAYYA ba saidai naji k'amshi a maqota bayan yanada halin yi...Zainab...Baban tane ya daka mata tsawa bakida hankali mijin naki kikai wa haka?, tarbiyyar dana baki kenan?.
Ke nagayamiki LAYYA ba dole bace ko dole ce sai kanada hali ba'ace kai sata ko kayi rance kayi ba.
Menene shikashikan musulmi? , tsaida Sallah,yin Azumi, Yadda da Allah da manzon sa, da kuma yin Zakkah na k'arshe aikin Hajji. Sune farillah koh? to suma basu wajaba akan wani ba.
Sallah idan ba yanda ka iya an sauwaqe maka ita kunga kenan a wani gun ba dole bace.
Zakkah...itama sai kanada halin yi...ba'a ce kai sata kayi ba kunga kenan itama ba dole bace akan wani sai maishi.
  Aikin Hajji...shima sai kanada halin yi...amma idan bakada hali baizama dole ba....Kuma shi kirane na Allah duk kud'in ka duk talaucin ka idan ubangiji ya kiraka sai kaje.
  Azumi....Dole ne tunda yana cikin shikashikan musulunci amma shima gun wani ba dole bane shima sai kanada halin yi zakayi idan bakada lafiya dole ka ajiye shi.
Yadda da Allah shine abinda yazama wajibi farillah dole ka duk musulmi wannan shine most bashida cewa sai kanada halin yi...ko kanada hali ko bakada shi wajibi ne.
Bare kuma LAYYA wadda ba'a lissafata ba acikin shikashikan musulunci.....gaskiya kuna hauka itafa LAYYA sai kanada hali kuma idan mutum yayi shi za'a bawa ladan bake ba, wallahi da kayi sata ko kai Maula dan kayi LAYYA gara ka zauna kaiwa Annabi Salati Allah yasan nufin ka bawai kaqi yi bane da wata manufa.
  Amma idan kanada halin yi sai kayi...tabbas kinyi hauka  AKAN RAGON LAYYA zaki ka so auren ki naman da idan ya jima yai wata guda aure dayake da daraja zaki qasqantashi AKAN RAGON LAYYA.
Tur da mata masu irin wannan halin...ke da kanki kinsan mijin ki idan yana dashi ko bayada shi amma saboda kar ace bakuyi ba saiki d'agawa maigidan hankali akan sai yayi auren ko LAYYA?.
Tabbas LAYYA Allah ne ya hallata ta amma kuma yafifita Aure akan ta darajar aure tafi gaban wasa....saboda haka maza tashi ki koma gidan ki idan Allah yasa zakuyi fine idan kuma bakuyi ba dama can Allah ya tsara naman ne bakici kome?.
Hmm Abba kyaleta wallahi k'awarta  zuwairat d'azu naje unguwar su ba kaji ba unguwar ta d'auka ta kaso auren ta AKAN RAGON LAYYA taiwa mijin magana akan ya siya Rago yace bashida hali zata k'ara yaimata saki guda yanzu ba gashi ba batada RAGON batada auren me akayi kenan?
Da sauri na d'ago "Yaya kikace auren ta ya mutu AKAN RAGON LAYYA?kwarai kuwa. Inalillahi kenan nima so tai nawa auren ya mutu nan nagayawa Yayu na abinda mukai da ita.
Aikam tasha tsinuwa Abba kam cewa yai bani ba ita ba k'awar arzik'i bace tunda bazata iya bada kyakyawar shawara ba.
Cikin sanyin jiki na fito daga gida lokacin anata kiran Sallah...Abba yaso nasha ruwa amma naki inason naga wani miji na ke ciki.
Shikam lokacin data tawo gida ashe ya biyo bayan ta har zai shiga saiyaji yanda yan uwan ta ta Abban ta sukai mata fad'a bashiri ya juya gida RAGUNAN daya siya shi yasa aka kamasa guda kafin ta dawo har an kulle su.
Da sallama ta shigo turus tai ganin RAGUNA har biyu ga kayan miya a markade sai naman kasuwa Alayyahu abu dai rankacakaf....kunya ce ta kamata batasan ma tafara hawaye ba saijitai ya rungumeta ta baya yana goge mata hawayen.
Rayuwa karki mun asaran hawayen ki tabbas kin cancanci fiye da haka banqi kawo miki RAGON ba da wata manufa saidan banson gidan mu ya lalace da kashin su amma ni Allah ya horen kud'in siya kunga kuwa dole nai tunda indai kanada halin yi wajibi ne kayi idan bakada shi ne baizama dole ba.
Yanzu sai ayi hak'uri ga RAGON LAYYA  nan...da AKAN RAGON LAYYA ake son tadamun  hankali to gashi nan.
Yo alwala muyi sallah sai muci abinci nasiyo mana komai a Golden dragon sai pizza a L&Z shayi kuma na Green park banson wahalar dake shiyasa.
Cikin kunya ina mak'ale a jikin sa nace Rayuwa ta da nayi girkin fa saidai a zubar? Noo bana turoma ki text message ba akan kada kiyi komai?, kodai baki duba ba kina ta tunani AKANRAGON LAYYA?.
Murmushi nai daga nan fa mukai sallah naci abinci sai kitchen dan gyara kayayyakin na abincin sallah da zan.
Ina shiga basaiga MURHU ba...KASKON SUYA MATSAMI harda kayan K'AMSHI da ALBASA komai dai sai san barka.
Hmmm Rayuwa ta ga komai nan ansiyo har KASKON SUYA da aka cemun AKAN KASKON SUYA ma za'a iya barin gida na...to yanzu sai a zauna tunda gashi na kawo basai kinsha wahala ba wajen aro bare suya takaimana yamma itadai murmushi kawai take a zuciyar ta tace mahaqurci mawadaci abinda arziqi bai baka ba tsiya bazata baka shi ba.
Tabbas mata ana hauka ace AKAN RAGON LAYYA saika bi katada hankali bayan kasan idan mutum yai LAYYA ladan nasa ne ku naku ci...to tunda baiyi ba Allah da ya yi ka bazai hanaka abin sawa a baki ba.

Loading next page....Gidan ZAHRA BUKAR.

Autar Hajiya

AKAN RAGON LAYYA Where stories live. Discover now