AKAN RAGON LAYYA end

742 35 2
                                    

🐑
🐑🐑
🐑🐑🐑
   AKAN RAGON LAYYA.
                        🐑
                         🐑🐑
                          🐑🐑🐑

®NWA.

Eidukum Mubarukum..wa ayyamukum Sa'eedatun..wa kullu Ameen wa an tum bil alfu khair.
           🌹🌹🌹
Feedoh... Zuciya ta
My Zahra....lovely Aunty
Stylish.... Besty

By
Real Autarhajiya

Last page...

GIDAN ZAHRA BUKAR.

  "K'arar bude gate taji da kuma horn a lokaci guda...ba shakka tasan  mijin nata ne ya dawo daga Idi.
Da karsashi da yanga ta fito daga d'akin nata dan zuwa taron sa....cikin dakakken lace d'an China ta fito daga d'akin ta.
  Maimakon taji sallamar mijin ta...saijin kuka RAGO tai a filin gate d'in gidan kafin ta k'arasa ma sai gashi shida wasu ganin ta a haka yasaka shi yiwa na bayan sa magana akan su tsaya a can farfajiyar gidan.
"Wow baby kinyi kyau saikace wadda zata gasar kyau?, gentle kenan to idan ban maka kwalliya ba wa zan wa?, haka ne fa to gaskiya zan biya ladan kwalliyar...murmushi sukai a tare.
"Au yanaji kukan RAGO?  gida zaka zarce yanzu?, gida kuma aiba inda zani RAGON LAYYA mune mana ni dake.
"Gentle haba yaushe ka gama wahala damu..dududu bikin mu 3weeks fa kagama wahalar biki sannan kace zakai LAYYA gaskiya da kabarshi nama ne kullum muna ci.
Hmm Baby kenan ai ni nayi bawai dan naci nama ba saidan d'umbin ladan dake cikin LAYYA.
Idan dan nama ne inaga akwai cikin frinjin mu....so kimadena cewa wahala aikin lada ba wahala acikin sa....da banda halin yi to bazan ba...amma dayake inada hali ba gashi nayi ba.
Ohhh gentle afwaan AKAN RAGON LAYYA zaka zauna kana ta surutu tabbas kayi gaskiya kana dashi shiyasa kai wani ma nema yake wani kuma yana dashi amma saboda zalunci bazai ba bayan LAYYA farillah ce indai kanada yanda zakayi..
Nagode Allah yaqara bud'i da d'aukaka....uhmm baby AKAN RAGON LAYYA ake ta gode mun ai wajibi ne akaina yake.
Yau naga abun mamaki....wani agun da zan sai RAGON LAYYA nan....yana zaune ga kud'i dumus a hannun sa amma magana yake akan me zai kashe kud'in sa a banza yai LAYYA.
Naman da kwana goma ma yaqare...shi bazai iya ba....wallahi ya fututtuke yanata maganganu shi yanada kud'in siyan Rago goma amma ko d'an Taure bai siya saboda b'arnar kud'i ne haka kawai ka sayi Rago dan aci Asha ruwa...
Kinji jahilci bayan yanada halin yi amma yace bazai ba....da bashida ikon yi shine....amma sai kiga wasu saboda mugun ta suna dashi amma ba zasuyi ba idan an kawo na Makoto kuma suci.
  Muna zaune wani yazo ya siya tunda ni wanda nake so babu agun anje kawowa shiyasa na zauna.
A gaban mu yaxo ya siya na dubu shabiyar bakiga ba yanata murna...ikon Allah wallahi yana tsallakawa titi da RAGON LAYYA mota ta bige RAGON ko shurawa bai ba ya mutu mai motar kuma ya gudu.
Abin tausayi gurin ya dawo ya had'a kai da gwiwa yana hawaye....Yana cewa haka Allah yaso dani dama ba rabon mu bane Allah yasa haka shiyafi alkhairi.
Abin takaici wannan mutumin dariya yakama "a haf yo me yakaini nasiya kafin ma a yanka ya mutu tab gaskiya na tausaya maka gashi daga gani bakada halin yi to sai a koma gida LAYYA ai ba dole bace ka takura kanka kayi kuma ya mutu sai dariya AKAN RAGON LAYYA kake kuka haka tab...
Mutumin kam cewa yai ko a haka nasan Allah zai ban ladan LAYYA...Allah yaga nufi na kuma insha Allah sainayi LAYYA dan cika Sunnar ma'aiki SAW wannan dubu goman shinkafa nai niyyar siya amma akan magana dakai yanzu zanqara siya koda zamu kasance bamuda abinda zamuci...Kuma ni ba AKAN RAGON LAYYA nake kuka ba ina kukan rayuwa ne da RAGON yana nan amman cikin mintuna kad'an Allah ya saukar da ikon sa akan sa.
Nikam jin bayanin sa agun nace "Malam tabbas Allah yaga niyyar ka amma ita LAYYA ba dole bace ga marashi....yanzu kasai RAGON LAYYA bakada abinda zakuci a gida me kayi kenan?, Allah ma bayason irin haka ba zafafawa idan bakada shi kada kayi...yanzu idan kasai RAGON kuma bakuda abinda zakuci kayi me kenan?.
Ba gara kasai abincin da zakuci ba nama Allah bazai hanaku wanda zakusaka a baki ba......
Murmushi yai kafin ya mik'e yace tabbas haka ne nagode da tunasarwar ka gareni Allah yaga nufina.
Murmushi nima namasa...agun nace ya nuna wanda yake so....Bai kawo komai ba yacemun da kaga wanda zansiya sai akace dubu talatin bashiri na nuna wanccen daya mutu ashe ba rabo bane shima.
Kud'in na bada nace akai masa har gida na bashi dubu goma kuma nace kasai kayan aikin sa.
Bakiga godiya da yai mun ba...ai yau nasha addu'a AKAN RAGON LAYYA.
Gaskiya kayi k'ok'ari gentle Allah ya biyaka...Ameen shikuma wanda yana sane baiba Allah yasan yanda zaiyi dashi.
Nagayamiki ai yayi ma...dan ban tashi agun ba yazo da kuka kamar zai haukace kud'in aljihun sa sun zube bakiga yanda yake ba kamar zaiyi tsirara gun zazzage jikin sa.
Nikam cemasa nai Allah ne ya fidda kud'in LAYYA daga cikin kud'in naka.....Kamar ya cinye ni AKAN RAGON LAYYA kud'i na duka wajen dubu biyu sin zube nashiga uku tabbas naga ishara LAYYA abace mai girma gashi banyi ba kud'in danake so sun zube wayyo Allah nan na barshi yanata sumbatu.
Hmm Allah ya kyauta Allah kuma yasa mutane a gane dan dai LAYYA ba abin aqiyi bane indai kanada shi..haka ne kam baby tawo ki zuban tuwon sai a yanka afara aiki.
Kwarai kam naji dad'in RAGON LAYYA nan zan baka tukwici  kaima. Enye AKAN RAGON LAYYA za'aban abinda tundaga first night aka hanani lallai kam to inajira.

Madallah da wata mai alfarma ina fatan Allah ya bamu ikon yi aiki na gari a rayuwa...Allah ya kyautata makwancin mu...fatan alkhairi

'Yan NAGARTA aci nama a hankali kada azo ana layin toilet......

Feedoh yar_ficika aci a hankali dan wallahi banda kud'in siyan ja da yellow ehee....

Besty....kici na gidan ku kada kibi kwanon Ya HAJJA ki kwashe mata nata..

Autarhajiya ce.

AKAN RAGON LAYYA Tempat cerita menjadi hidup. Temukan sekarang