🐑
🐑🐑
🐑🐑🐑
AKAN RAGON LAYYA.
🐑
🐑🐑
🐑🐑🐑By
Real 'yammatan Hajiya.
Short story Just for funny.....AMINI...shine wanda baya shayi ko shakkar gayamaka gaskiya idan kai ba daidai ba.
Amini shine wanda a wasu lokutan na daban sukan kasance dan uwa agareka...gaskiya na kan rasa wacce irin qauna mikewa juna nidaku.....qauna ce ta fisabilillah ba algus ko hainci bama iya rayuwa batare da kowanne yaji muryan kowa ba a rana ina son ku sosai....eh.
Feedoh yar_ficika
Zahra Bukar
Stylish Besty naKu na sadukarwa a bisa tsaftattaciyyar qaunar dake tsakanin mu.
Page 1
GIDAN ZAINAB
Gida ne Madaidaici mai kyawun gaske...duplex ne amma tsarin gidan abin ka k'ara kallo ne daga gani sabo ne amarya ce ko kuma dai tarewa akai.
Qiiii k'arar mashin ta karade gun . Wani matashi ne kyakyawa akan machine din. sauka yai akan mashin d'in kana ya jingine shi a gefe ya shiga daga ciki ya bude gate d'in sannan yashiga ya maida k'ofa ya rufe.
Da sallama ya shiga gidan amma saiyaji shiru k'arawa yai nan ma shiru...to ina Rayuwa ta ta shiga nida na saba tundaga gate za'a fara mun oyoyo amma shiru haka dai ya k'arasa cikin parlor'n.
Zaune ya ganta ta harde kafa tana canza chennel ko waigowa batai ba bare yasaka ran samu. Oyoyo.
"Rayuwa ta yana jiki shiru wani laifin namiki ne?.
"Mts kaga Mohd ba zancen rayuwa ta banson sanabe da soyayyar banza idan ma zaka farka ka farka dan bazan lamunta ba.
Ace yau sauran kwana 2 sallah amma ace banga RAGON LAYYA ba bare KASKON SUYA KO MURHU...a takaice dai ko ALBASA datake arha da kayan k'amshi bangani ba bare nasaka ran zakayi LAYYA shine zakazo wai Rayuwar ka.
Ido Mohd ya bude jin abinda zainab ke fad'a da sauri ya mintsini hannun sa ko zaiji mafarki yake amma inaa shiru.
Rayuwa ta AKAN RAGON LAYYA zaki zauna kina gayan magana nifa mijin kine kuma ko ba komai naci darajar girman ki danai amma kike gayan magana.
Ohhh haka ma zakace to wallahi baka isa ba AKAN RAGON LAYYA zan iya barin gidan ka dan bazan zauna naji k'amshi ba ko kuma akamun na sadaka gidan ku za'ayi LAYYA gidan mu haka yayuna suna LAYYA sai ni? ace bazan ba.
Mohd yana tsaye idan ransa yai dubu ya b'aci me zainab ke nufi daga dawowar sa?.
Kaga ka tsayan aka ko RAGON LAYYA ko TAKARDA TA. Inalillahi AKAN RAGON LAYYA zakice nabaki takardar ki kinga sallah tazo banyi LAYYA ba...ko kuma mun tab'a magana da ke AKAN RAGON LAYYA?.
Kaga nasan bamu tab'a ba amma alama nagani ta ba zakayi ba...kai AKAN KASKON SUYA ma zan iya barin gidan nan balle AKAN RAGON LAYYA.
Hannun ta yakama cikin lallashi da lallami yace Rayuwa ta insha Allah zanyi LAYYA bance miki bazan ba banga abin daga hankali ba kodai akwai wani abin daban anya?.
Aifa su zainab saiga murmushi jin yace zaiyi LAYYA nan da nan tafara blushing harda bashi light kiss a baki.
Shikam mamaki zainab tabashi AKAN RAGON LAYYA zatace zatai masa bore anya kuwa ba da akwai wata a k'asa ba?.
Habeeby tawo kayi wanka kafin na d'ora girkin?.
Ohh baki d'ora ba dama? Kai ta d'aga cikin jin kunya saboda gaskiya tasan batai daidai ba Mohd bai cancanci haka ba.
Lallai AKAN RAGON LAYYA shine ko girki ba'a mun ba dats great yammata aje ayi to.
Cikin kunya tashiga Madafa dan yimasa girki.
Cikin mintuna kad'an tagama masa jollof ta macaroni wadda taji busashen kifi da kayan lambu.
Kiran Sallah akai shiyasa ya fita zuwa masallaci danyin sallah amma dai yana cike da tunanin AKAN RAGON LAYYA auren sa ke girgiza.
Tsuuuu wayar zainab tafara k'ara da sauri ta d'auka.
"Hello qawata ai plan d'in mu yayi dan bakiga yanda yai ba yanzu dai yace zaiyi da fa ko maganar baimun gaskiya kin cika qawa tagari ai ban ragamasa ba.
Daga can b'angaren Zuwairat tace yauwa aminiya bayan RAGON LAYYA ma har LEMON juice zakice ya siyo ai mazan nan su zamane sai da wuta kece ma tun farko kika sakarmasa yanzu dai yace zaiyi?, eh mana ya amince inajin gobe ma yazo da shi kinga jibi sallah?, eh fa nima nan jiran sa muke RAGON LAYYAR.
Ok sai anjima naji alamar shigowar sa? Ok amma ki k'ara kaimi dole ne RAGON LAYYA dan bazai yuyu qawayen mu ace sunyi ba kece kawai bakiyi ba.
Haka ne Zuwairat sai anjima....hmm dad'i miji har korata kike? ba haka bane...qit ta kashe wayar ta.
Nan ya shigo abinci yaci kana sukafara hira irinta masoya har lokacin bacci yai suka kwanta.
GIDAN ZUWAIRAT.Alhaji yanzu ba zamuyi LAYYA ba? Kwarai kuwa Watanda nai banda kud'in siyan Rago ko sata kike so nayi ke nifa idan zaki takuran wallahi saiki tafi gidan ku ki zauna..
Idan Makoto suka kawo naci da yara na mu soya kin dameni AKAN RAGON LAYYA zan tsaya kina mun kananun maganganu?.
Alhaji kayi haquri bada wata manufa nai haka ba. Ke dallah can rufemun baki munafuka kinzata irin mijin qawar kine ni da kike zugawa tai rashin mutunci AKAN RAGON LAYYA?.
Alh.......jeki na sake ki saki d'aya nagaji da ke dama.
Inalillahi Alhaji AKAN RAGON LAYYA da nai magana shine zaka saken?.
Ke ko AKAN KASKON SUYA ne idan kika dameni zan k'aramiki wani...
Kuka zuwairat tasaki yanzu ya zanyi? kenan da Zainab keda Alhaji saki uku ma zai mata jibi ni daga magana amma har nasamu rabo na ko dayake babu ba abinda bata sawa... haka maza suke idan sukaga abu ya taso sai su ringa kiran babu kamar akan su aka saukar ana magana kuma siyo kanka da masifa.
(Nikam nace kwarai haka maza suke da azumi suce sun tafi ittikafi akan kada su kawo kayan azumi... yanxu kuma ga sallah yanzu zasu fara Rago yai tsada kai doguwar magana a sandaka gidan ku.....amma zuwairat ke ai daidai kenan baki duba gidan ki ba saina wata kike hange.)
Tashi tai tashiga d'aki mayafi ta janyo sai gida tana kuka AKAN RAGON LAYYA an mata saki guda.
Gidan su tai nan ta zayyanewa iyayen ta yanda akai.....aikam Baban ta me zaiyi idan ba fad'a ba ke kam zuwairat kin cika shegiya AKAN RAGON LAYYA ace an sake ki wato ku bazaku iya hak'uri da yanda ruyuwa tazo ba...Idan kana dashi yau ba lallai gobe ya kasance kana dashi ba kin ban mamaki ko da yake nima yanzu nagama shan zagi AKAN RAGON LAYYA gun uwar ki wai na siyo qarami ba babba ba saikace ance dole.
Ko a addini ba'ace dole ba idan kanada halin yi kayi idan ba hali kuma saika yi hak'uri dan bazaka takurawa kanka ba.
Yana gama fad'a ya wuce fuuu.....yabar su da cizon yatsa.
Hmm ai ke uban ki haka yake daga an magana saiya sako wa'azi saikace shine limamin masallacin qasar nan wato so yake kuma mazan ku su zama irin sa shi a tafe su a tafe..Allah ya kyauta amma dai Naziru yai rashin mutunci daga magana AKAN RAGON LAYYA sai a bika da saki?.
Hmm kad'an ma kenan gashi taiwa kanta ba Watandar ba RAGON LAYYA sai ki zauna aci dake.Auta ce
![](https://img.wattpad.com/cover/121579829-288-k357475.jpg)
ŞİMDİ OKUDUĞUN
AKAN RAGON LAYYA
AksiyonSamu da rashi duk na Allah ne....Idan Allah yabaka kayi k'ok'ari aikata kyakyawa da abinda yabaka. Allah yana jarrbawa bawan sa yaga zai cin wannan jarabawar ko kuwa?. Gulma...hassada indai kayi to zakaga k'arshen ka.....zuwairat jeki na sake ki sa...