MAFARIN LAMARI

3.6K 159 3
                                    

BISMILLAHIR-RAHMANIR-RAHIIM

Labari da Rubutawa
             Basira Sabo Nadabo

         SHEKARAR RUBUTU (2017)

            GARGAƊI

   Ban yarda a juya min labari ba ko ta wani siga, inhar ka/ ki ka juya min to wallahi ALLAH YA ISA bazan taɓa yafe wa ba, ko BANI BACE da aka juya ban yafe ba kuma wallahi ku sani zamu tsaya a gaban ALLAH, labarai na bana ɓatanci ba ne don haka ina da hujjar jawa mutun ALLAH YA ISA ga masu satar fasaha kun kasa yin na kanku sai na mutane akwai ALLAH.

                  
                      GODIYA

         Ga ALLAH maɗaukakin sarki, wanda raina da rayuwata suke hannun sa. Ina gode maka, ina neman taimakon ka. Ya Allah ina rokonka, ka kare ni daga dukkan abinki. Ya Allah ka tsare ni ga magauta masu cin dunduniyata, ALLAH ka da kabar makiya suyi nasara a kaina da iyalina, ALLAH ba ni da niyyar cutar kowa, ALLAH ka da kabar makiya suyi nasara a kaina da iyalina, domin albarkar Annabi Muhammad (S.A.W).

                     DOMIN KU

        Iyaye na abin alfaharina wanda na ɗauki so da kauna na ɗaura muku. Margayi Alhaji Sabo Nadabo da Margayi Alhaji Nuhu Abdullahi, tare da Fatima Sabo Nadabo da Zulaihat Sabo Nadabo, tare da Zainab Nuhu Abdullahi da Alisha Nuhu Abdullahi tare da sauran al'umman Annabi Muhammad (S.A.W), ina rokon ALLAH da ya yalwata haske tare da rahamarsa a kabarbarunku, Ya ALLAH ka kara gafara a gare su damu baki ɗaya Amin Ya Allah. Mahaifiyata farin cikin rayuwata nagode da kulawarki a gare ni, nagode da shawarwarinki akan yadda zan tafiyatar da rayuwata, ALLAH ya kara tsare min ke Ubangiji yaja kwana. Amin Ya Allah

               JINJINA GARE KU
     Yayye na muradina nagode da kulawarku a kaina har nakawo yanzu, ALLAH ya kara haɗa kanmu ya kauda shaiɗan a tsakanin mu. Amin Ya Allah
       
                SADAUKARWA
   
       Na sadaukar da wannan labarin ga Family na gaba ɗaya.

     LITTAFAN MARUBUCIYA

SHURAKH
BANI BACE
BAN AIKATA BA
BAKAR ZUCIYA
BARRISTER FATIMA
BAYAN WUYA
NI'IMAT
BAN KASHETA BA
NADAMATA 1&2

Bismillahir-Rahmanir-Rahiim

SHORT STORY (Gajeran Labari)

Ya ALLAH. Ina fara wa da sunan ka kuma In Shaa Allah zan gama da Handan, wannan labarin BAN AIKATA BA labari ne da yawancin mu muke tafka wannan kuskuran kuma kuskure ne mai girma wanda muke ganin sa karamin abu, ALLAH kasa na gama lafiya alfarmar Manzo, Habibullah, Shafi'ullah, Ya Mahabubullah Ya Sayyadi Ya Muhammadur-Rasulullahi Sallahu Aalaihi Wa Salaam.

                 BAN AIKATA BA tsohon littafina ne kawai kwaskwarima na ke yi mai duk mai son cikakken labarin ya je kan handle ɗina na Wattpad @Basira_Nadabo. Nagode

Page 1 to 5

Ihun neman taimako ta ke yi amma mutumin dukanta ya ke yi ba ji ba gani cikin kukan ta ke cewa.

"Wallahi Allah Abba ban taɓa zina ba kuma ban san ta yadda ciwon nan ya shiga jiki na ba. Umma ku yi min rai wallahi zan mutu, mutuwa zanyi in kuka cigaba da duka na, Don Allah Abba ka yi hakuri ban yi ba, wayyo Abba na ku yi hakuri wallahi BAN AIKATA BA, ba halina ba ne wayyo Allah na!"

"Ai wallahi gwara na kashe ki na huta ki rasa akan na barki da ranki. Ki rasa abin da zaki ɗauko min sai cuta, saboda tsabar yawon karuwancin ki, to ba a gidan nan ba kuma tun wuri ki nemi wani uban amma bani ba."
          Yana magana yana zuba mata murɗanɗan bulalar danko wanda ko jaki baza'a doke shi da ita ba.

BAN AIKATA BAWhere stories live. Discover now