BAN AIKATA BA

1.2K 72 2
                                    

BAN AIKATA BA


ELOQUENCE WRTERS ASSOCIATION



Labari da Rubutawa


Basira Sabo Nadabo



SHORT STORY

Alhamdulillah, an sallamo mu a asibiti Sis Ruky ta samu lafiya sosai, nagode fans da kulawarku, da masu kirana da masu bina prvt duk ina godiya kuma na kara yarda sakon da nake son isarwa yana tafiya dai dai yadda ya kamata, nagode sosai dearest fans, muna mugun tare like irin totally ďin nan, kun gane ai

Wannan nakune maymunat fcbk, da duk sauran friends ďina na facebook, Allah ya kara muku sona Amin Ya Allah


Dedicated to Shamsu Nuhu, Usman Nuhu, Abubakar Infantry (WA), Aliyu Sabo Nadabo (bro Fire)


Page 21 to 25

Tabbas cen zani kuma Abba sai yayi kuka da idonsa akan korar karen da yayi min, haka dama akace iyaye suyiwa 'ya'yan su? Kodai nice banyi sa'ar iyaye nagari ba, me yasa hakan ya faru dani bayan ban taba zama kusa da namiji ba? Ban taba zina ba wallahi BAN AIKATA BA to me yasa na kamu da cuta mai karya garkuwar jiki, zanje gidan karuwai kuma duk mai kararran kwanar daya ďauke ni dole shima ya samu, amma zanso ace Abba ne shine mutun na farko dazan gogawa wannan cutar kota abinda zai sha ne, a haka harna isa sokoto road ina sa kafata domin shiga gidan mata amma me sai naji wani kuna a zuciyata tana min kuna tare da gargaďina da nuna min kalar azabar da Allah zaimin, haba ke kuwa Faineesat karki kai kanki ga halaka, karki biyewa zuciyar da zata guje miki ranar nadama, ni musulmar zuciya ce bazan taba barinki ki aikata abinda kike tunani ba, ki tuna da nau'ikar azabar da Allah ya tanadarwa mutuna masu mugun zuciya wanda suke siyar da jikin su domin neman kuďi, kituna da kalolin azabar da Annabin mu yake yawaita faďawa sahabbansa akan masu aikata ashsha to kisani zina tana daga cikin manyan laifuka in aka cire shirka sai zina, toki tuba zuga Allah domin shi mai karbar tuban bawansa da aka zalunta ne, ASTAGFIRILLAH Ya Allah, Allah na tuba ka yafe min, da sauri na dawo da baya domin gudun karda wata zuciyar tamin huďubar shaiďan na afkawa aikin dana sani, kasuwa na nufa domin naiman aiki, babu lungu da sakon daban lek'a ba amma har yanzu shuru da kyar na samu nayi sallar azahar saboda yunwar da nakeji, ga la'asar ta kawo kai, washh Allah nagaji wallahi ina zan samu koda ruwa ne nasha ďan aikin ma babu duk inda naje basu yarda dani ba, saboda wasu mutanen irina sun aikata musu abinda ni suke tsoron ďaukata ya zanyi waye zai taimaka min, haka na tashi jiki babu kwari domin ina tunanin innaje gida audu zai bani abinci naci, to ai nayi alkawari bazan taba kayan Abba ba kai gwara na koma gida na mutu acen wa Allah zasuji tausayin gawata su kaita makwancina, a haka harna karasa gida, amma sai ganin wani nayi ba audu mai gadi ba kuma daga ganin wannan tsohon ba imani bane dashi don kwayar donsa jajawur yake

Ke! Daga ina kike, waye ya baki ikon shigowa gidan nan? To kama hanyarki inba so kike na ďauke wannan kafar naki da gora ba, shegiya mabarata masu satar kayan gidan mutane, magana nakeyi kin kureni da gwala gwalan idonki kamar na agwalan nufawa

Haka inaji ina gani tsohon nan ya kore ni a gidan mu, wai nice ake kora a gidan Abba na, wani kuka mai karfi yazo min

Kunji min ja'irar yarinya mai suffar aljanu, kila ma aljanar ce tazo min da suffar fuskar Alhaji, badan Alhaji yace min bashi da wata 'ya ba, da babu abinda zaisa bazance 'yarsa bane, sheďani aljana ce huhuhuhuw wallahi Allah nima nayi faďa da aljana da rana tsaka nima zani a sani a gidan tarihi

Kai sadau lafiyarka kalau kuwa? Tun ďazu kana magana kai kaďai

Wallahi Allah, Alhaji faďa nayi da aljana da ranar nan, daga ganin kyawunta kasan aljana ce Alhaji

Da kyau sadau mai gadi ka burgeni dama ka sheme ta ne daka kyauta min domin ni kaina ta isheni, bibiyata takeyi da sharri

Ya SubhanAllah! Nice nake bibiyar Abba na da sharri, kuma wato yama gane cewa nice aljanar da sabon mai gadi yake nufi kenan? Inna Lillahi Wa Inna Ilaihir Raji'un, Allah karka haďa wani bawanka da irin nawa kaddarar, kaddarar haďasu da iyaye marasa tauhidi

Aradun Allah inna kara ganin aljanar nan yau saina karta yasin saina kashe ta

Da gudu na faďa cikin flawowin dake kofar gidan Abba domin tsira da rayuwata, don daga ganin wannan sabon mai gadin zai aikata abinda yake faďa

Kashhh amma wannan aljana tajamin, da yanzu nima ina gidan tarihi saboda kokarin kashe aljana danayi

Ya gama dube duben sa ya koma gida, kullewa cikina yayi wanda tuni yake min da tun jiya babu abinda ya shiga cikin sa, ina zan dosa waye zai taimake ni, jafa kafata kawai nakeyi domin ban san inda nake saka kafata ba, ji nayi anyi sama dani anyi hajijiya dani an dawo dani kan wani abu, ji nayi wani abu mai sanyi yana zuba a fuskata, luuuuu na faďi ban kara sanin inda kaina yake ba

Da gudu direban motan ya fito duk a ruďe yake domin bai taba haďuwa da irin wannan hatsarin ba, Inna Lillahi jini ke zuba daga kanta kardai mutuwa tayi? Ya Ilahi na kashe 'yar mutane, ya wai waiga baiga kowa ba domin baiga shugowarta ba don shima gudu yakeyi don an mishi kirar gaggawa a asibiti


Gashi tukwici ne gare ki Jienie na Ruqayya Nuhu, wallahi jininki yawo yakeyi a cikin jikina Allah ya kara mana kaunar juna, Amin Ya Allah, Allah ya kara miki lafiya dear

Karamar Su Babban Suce Ni 'Yar Nadabo

Basira Sabo Nadabo

BAN AIKATA BAWhere stories live. Discover now