BAN AIKATA BA

1.2K 67 0
                                    

BAN AIKATA BA



ELOQUENCE WRITERS ASSOCIATION



Labari Da Rubutawa

Basira Sabo Nadabo

SHORT STORY



Wannan naku ne Eloquence, Allah ya kara mana ďaukaka da haďin Kai, Er lurv, Sis Shamsiyya, Aysha Opera daddy's girl, pure green, Jannat Jay, Alh Admin, Auta, Autan Marubuta, Autan eloquence Allah ya barmu tare dearest members

LU'U LU'UN SARAUTA, Littafi ne na yak'i da jarumta wanda mashahuriyar marubuciyar nan HAWWA DAMARY zata kawo muku nan bada jimawa ba, littafi ne dake cike da sark'ak'iya tare da jurumta, ina samari kai harda yan mata karda ku bari a baku labari domin labarin zai tabo abubuwa da yawa, kudai ku saurare mu In Shaa Allah yana nan tafe

My Abeeda Allah ya kara miki ďaukaka duniya da lahira. Amin Ya Allah

Sis Classic Feedo tare da members na group ďinki nagode da kaunarku gare ni. Allah yabar mu tare, Amin Ya Allah


My Namecy lurv, ina sonki karki manta da kalmar Ana Tare my Baseera (Cutie Pie 👄) lurv



Dedicated to my Awesome Family, my family my everything, I love you guys❤



Page 26 to 30


Da gudu ya ciccibe ta ya sakata a motar sa yaja motar da gudu kamar zai tashi sama, ikon Allah ne kawai ya kaishi asibiti duk inda ya wuce sai an kalle shi, nurse! Tun kafin ya tsaya yake kiran nurse's ďin domin ďaukar emergency patient ďinda yake ďauke dashi, da yake kowa yasan Dr baya son sanya suma da sauri suka fito da trolling bed, suka ďauki Neesat suka ďaura akan gadon, emergency room suka nufa da itah saboda jinin data zubar, duk ya gama ruďewa saboda wannan accident ďin shine wanda ya tabayi kuma ya kawo patient ďin domin yin dressing, duk inda ya wuce sai an kalle shi domin an sanshi da rashin kula irin raunir da yake tattare da Neesat, domin cewa yakeyi wannan ba hurumin sa bane, da kanshi ya shiga cikin ďakin kuma ya dakatar da duk nurses ďin sai mutun ďaya wanda ya yaba da aikin ta domin mace ce mai mutunci tare da karamci Baby Nurse, tare suka shiga ciki, cikin yardan Allah da kyar suka tsayar da jinin dake zuba akanta, Baby Nurse ta turo ta zuwa ďakin hutu, har yanzu allurar baccin da aka mata bai sake taba

Nurse ki tabbatar kafin taci komai ki ďiba jinin ta, da kanki nake so kije lab kiyi duk wani gwaje gwajen daya kamata domin tabbatar da abinda yake raina

In Shaa Allah Dr zanyi yadda kace amma kam wannan patient ďin tana bukatar taimako tun kafin abinda muke hasashe ya zama babban abu, domin kamar bata kan magani

Uhmm kinyi tunani mai kyau Baby Nurse, In Shaa Allahu zamu san abinyi amma dai yanzu jeki ki aikata abinda na saki, kuma Don Allah tana farfaďowa a tabbatar taci wani abu mai kyau, kuma kisa ido akanta domin damuwar da take ciki zata iya guduwa

Toh yallabai In Shaa Allah zanyi yadda kace

Toh zaki iya tafiya

Dr baka duba waccen patient ďin ba

Bazan iyaba nurse ki kira Dr Ahmad Nadabo, amma ni kam yanzu bazan iyaba nurse

Toh shikenan yallabai

Alhamdulillah, Allah nagode maka, kai amma na huta wallahi duniya gidan wahala, gani yanzu kwance babu damuwa a tare dani, kuma Abba da Ummah suma zasuzo su same ni a gaban Allah zamuyi shari'a, tunda a duniya ba'a bawa karami hakkin sa, ba'a saurarar gaskiyar sa amma nasan anan za'abi min hakkina In Shaa Allahu, duk wannan bayanan da takeyi agaban Baby Nurse takeyi don ita bata lura da mutun a gurun ba, sai da Baby Nurse ta taba ta tukunna tace

BAN AIKATA BAWhere stories live. Discover now