BAN AIKATA BA

961 47 2
                                    

BAN AIKATA BA

ELOQUENCE WRITERS ASSOCIATION

Labari da Rubutawa

Basira Sabo Nadabo

SHORT STORY

My Namecy kin fita daban wallahi, ban taba haďuwa da kawa irinki ba Allah yabar mu tare Amin Ya Allah. My sweet Baseera like know other. I double heart you lurv muaahhh

Allah Ya baki lafiya Sis Ayusher Allah yasa kaffara ne. Amin Ya Allah

Ina kike my zuciya my kawa Baby Nurse (Mom Anielurv) ina sonki sosai dear

Yayata SophiaG ina sonki Allah

Aunty Rash Kardam wannan naki ne tare da duk wani member na groups ďinki ina godiya da soyayar da kukewa littafina

Dedicated to Hussaini Ďan Hajia and Maitama Sabo Nadabo

Page 11 to 15

Babu wanda zai bani amsa ta babu, duk ciki karajin kuka take magana

Yanzu Alhaji kana ganin abinda ka aikata dai dai ne

Wato bani da ikon zartar da hukunci a gidana abi kenan ko, kema in bazaki iya zama ba ga kofa a buďe take zaki iya binta kuma daga yau bana bukatar a kara tada maganar wulakantacciyar yarinyar cen ni na cire ta acikin zuri'a na

Amma Alhaji kayi tunani ba haka Faineesat take ba, bamu taba kamata da aikata ashsha ba, ka duba wannan maganar

Kina yawo da itane ko kuma tare kuke zuwa karatu, ko kuma zakice min likita ya mata k'arya ne, eh ke nake saurare

A'ah bana yawo da itah kuma ba tare muke zuwa karatu ba sannan bance likita yayi mata k'arya ba

Toh maganar nan ta mutu, bana son a kara tada ta a gidan nan, ko me yasa ba'a taba samun sauran yan uwanta da cutar ba, saboda sun kama kansu gasu zaune lafiya a gidan auren su, inace saboda daďin tarbiyar da suka samu ne yau ga baban yara cen zaune a saudiya tare da yaranta, amma Faineesat saboda ta raina mu shine ta saka mana da abinda bazamu manta ba

Amma baka ganin duniya zata zage mu kuma za'a c.......

Ya isheni nace bana sonjin maganar Faineesat a gidana doka ce kuma dole a bita nagama magana, ya ďauki hular sa ya saka ya fice

Yanzu haka zan zuba idon akan duk abinda yace? Amma ya zanyi ita tajawa kanta Allah ya kara, nayi asarar ďaukar cikinki Neesat

_SubhanAllah, wai uwa kenan, anya iyayen mu kuna kyauta mana kuwa, kuna ďaura mugun baki akan mu, Allah ya shirya shine abinda ya kata tsakanin ki da yaranki, ALLAH yasa mu dace Amin Ya Allah_

Tada ikama da limamin unguwar mune ya dawo dani daga tunanin da nakeyi, hijab ďina na dauka nasa na fita domin samun ruwar da zanyi alwala, a kofar masallacin mutane a cike kasancewa yau lahadi kowa yana gida, cikin masallacin ya cika har waje, ga wasu kuma suna alwala na rab'a gefen su na taro ruwa a buta nayi alwala tare da cika wata buta na tafi dashi saboda anjima basai na fito ba, duk wannan abin a idon Abba nakeyi saboda yana ďaya daga cikin masuyin alwala a gurin, har na shige gida nayi sallah tare da neman taimakon Allah ya bayyanar da gaskiyar al'amarin nan, ga yunwa da nakeji wani irin rayuwa ne, to waye yasa min cutar kanjamau, wallahi ban taba zina ba ni da ko saurayi bani dashi, kuma bani da abokin gaba balle nace makiya ne suke bibiyata, ban taba faďa da kowa ba tun tasowa na, bani da kawa har sai da nashiga university itama bama shiri sosai, tunda ba depertmen ďinmu ďaya ba, toh waye wani bera ne yazo ya wuce ta kafata da gudu na tashi saboda ba karamin bera ne, shiba b'urgu ba amma gashi kato, ya gama yawon sa ya koma ramin sa, na fita na kwaso duwatsu na toshe ramin kodon na samu damar yin bacci cikin salama yau, ga ďakin duk kura ga yanar gizo gizo saboda ďakin ya daďe ba'a buďe taba ga yunwa ga k'ishi na rasa ina zansa kaina, dole gobe na fita nemar aiki don taimakon kaina bazan iya zama haka ba, inba kashe kaina zanyi ba, gashi Abba yamin iyaka da duk komai na gidan sa, ga duhu ya fara lillibewa wani tsoro ne yake shiga na ga yunwa, in banda kuka da karatun Al'Kur'Ani babu abinda nakeyi, kai dole ma na fita nemar taimakon kaina da kuma maganin cutar dake jikina kodon lafiyar kaina, amma ta ina zan fara gurinwa zani waye zai taimaka min!? Nasan da Aunty Baban yara tana kasa da itace zata fara taimako na koda kuwa Abba zai kashe tane, amma akwai Allah kuma a gare shi na dogara In Shaa Allah zan bawa Abba mamaki, bazan taba neman taimakon sa ba, koda na sile ďaya ne, Ya Allah ka taimaka min Don Girman Zatinka Ya Allah! Ta karashe maganar da kuka mai cin rai

Karamar Su Babban Suce Ni 'Yar Nadabo

Basira Sabo Nadabo

BAN AIKATA BAWhere stories live. Discover now