BAN AIKATA BA

1.7K 72 5
                                    

BAN AIKATA BA



ELOQUENCE WRITERS ASSOCIATION



Labari Da Rubutawa

Basira Sabo Nadabo


SHORT STORY


KARSHE

Ina Godiya ga Allah Mamallakin Sammai bakwai da kassai bakwai, wanda ya halicci kowa da komai, gwanine akan ko wani tsirrai, isashshe akan komai, ikonsa ikone wanda baya karewa balle ya nemi iko a gurin wanda bai da iko, yalwatacce ne wanda yalwatarsa baya karewa, gamshashshe ga kowa, da ikonka na fara rubuta wannan gajeran labarin kuma yau a cikin isah da ikonka zan gama, ina kara godiya ga ďan gatan Allah, wanda gata take gata agare shi, kai kaďai ne gwani a inda ake gwaninta, kai kaďai ne ďa tun ba'a kagi babu ba har babun ta fito ta buya kai baka san babu ba, Manzona Habibullah, Shafi'ullah Ya Muhammadur Rasulullahi Sallallahu Alaihi Wa Sallam.

Godiya a gare ku Readers da yadda kuke bani goyon baya akan duk wani novel dina, idan nace ku, ina nufin ni, idan nace nii, ina nufin ku, so ina godiya da kaunarku, Allah yasa alkhairin dake ciki ya amfanar damu, sharrin cikin sa kuma Allah ya kauda mu a gare ta, Ya Allah kuskuran dake cikin labarin nan ya Allah ka yafe, wazai yafemin banda Allah kai nake kira Merciful, Don kaine adali, kare ni Allah bani da dabara, azurtani Allah bani da dabara, ni kai kaďai nasani bani da dabara, ka kare ni Allah naa bani da dabara, Nagode sosai, Remain blessed, Fii Amanillah!


Na Sadaukar da labari na ďunguru gum ga Royal Family na, Allah ya kara haďa kawunan mu Amin Ya Allah

Page 46 to 50

Suna shigowa tun kafin ya karasa parking, Neesat ta fito da gudu taje ta rungumi baban yara, tana kuka mai tsuma zuciyar mai sauraro, ta ďagota tare dayi mata lafiyayyun mari guda uku, har sai da su Dr da baby nurse suka razana, sannan cikin kuka tace

"Ke Neeesat don gidanku ina kika shige ba tare da sanina ba, kinfi kowa sanin nice bazan yarda da karyan k'uregen da su Abba suka yarda dashi ba, haba Neesat me yasa kikayi mana haka, me yasa, ta kara fashewa da kuka"

Neeesat in banda kuka babu abinda takeyi, ta kasa magana, Umma ce ta jawota jikin ta, tare da cewa

"Haba auta me yasa zaki guje mu in mu mun kasance iyayen da basa yarda da kaddara me yasa ke bazaki iya juriya tare da amsar kaddararki hannu bibbiyu ba, Neesat bazan yafewa kaina ba inhar baki yafe min ba" ta faďa tare da marin kanta

Da sauri Neeesat ta fara girgiza kai tare da kokarin hana Ummanta cigaba da marinta, suka kara rungume juna, Dr ne yayi gyaran murya sannan suka kula da mutane a gurin don baby nurse ma kukan take taya su, sannan yace

"Kukan nan ya kamata a tsayar dashi haka mu shiga ciki koma menene sai ayi amma ba anan ba"

Sai yanzu suka gane ashe a waje suka, sun ďungumi jiki zasu shiga cikin gida kenan sukaji an daka musu tsawa tare da cewa

"Karda ki kuskura ki shigar min gida, donni bazan zauna da karuwa mai cutar kanjamau ba, kuma wallahi in kika shigar min gida sai nayi shari'a dake Neesat"

Da sauri ta juyo domin ganin Abbanta da yake kara mata gargaďi akan shiga masa gida

"Kai Adnan wallahi Allah Faineesat sai ta shiga gidan nan, nice zanyi shari'a dakai, kalle shi wai uba, ahaka ake uban? uban da bazai iya kare tsuraicin 'Ya'yansa ba, uban da bazai iya rufawa 'yarsa asiri ba to kasani Human Rights zata shiga cikin wannan maganar kuma saita nemawa Neesat 'yancinta a gurinka a matsayinka na ubanta, kuma gida sai ta shiga tunda gida dai nawa ne, in kuma ka isa to ka hanamu shiga, kalle ka uban kawai"

"Haka kika ce ko? toh shikenan zanyi maganin ku dukkan ku, dani kuke zancen" ya cigaba da sambatun sa

Ita dai Neesat sai kuka takeyi domin har yanzu ta kasa yarda da Abba uba ne a gare ta, don Wannan uban ba uba bane, Umma tace

"Ku wuce mu tafi kuma naga uban da zai hanaki shigarmin gida, tunda gida nawa ne, mutun kuma yayi magana na feďe masa tun daga biri har wutsiyarta"

Haka Abba yanaji kuma yana gani Neesat ta shiga gidan da yake ikirari nashi ne, bayan an gama gaggaisawa, baby nurse ta basu umma labarin tun daga randa aka kawota asibitin da yadda ta samu cutar HIV da kuma rabuwarta da cutar, sannan Dr shima ya ďaura nasa daga karshe ya kara neman a bashi dama ya aure ta, tunda suka fara magana umma suke kuka, ni kaina Ceeber na rasa gane kukan me sukeyi na farin ciki ne kona bakin ciki, da sauri ya shigo ďakin kamar an ingizo ne har yana tuntube ga fuskarshi duk hawaye ya fara nuna Neesat da hannu yana kuka sannan yace

"Hakik'a na zalinci kaina na cutar da kaina, na wulakanta kaina, Faineesat bake na wulakanta ba nine na wulakanta, hakika nayi batan bakatantan domin yau Allah ya nuna min ikana don nima ina ďauke da cutar HIV" ya kara fashewa da kuka

Duk a razane suka mike, daga ganin su sunyi sumar tsaye ne, babu abinda kakeji sai sautin kukan Abba, sannan ya cigaba da cewa

"Ban kasance uba nagari ba, umman ku ta sani, tasan cewa ni manemin mata ne amma saboda ku ta rufamin asiri ba tare da ta tona mugun halayyata ba, ďazu bayan shiganku gida na fita zuwa sokoto road domin na huce haushin dake raina, ina zuwa na tarar da peace tana kuka, na tambaye ta musabbabin kukan saita ďauki wani takarda ta mika min sannan ta ďaura da cewa, Alhaji bawai ina kuka don na kamu da HIV bane a'ah ina kuka ne don cutar takai stage ďin da zan rasa rayuwata kuma ina bakin cikin ban gama yaďawa mugayen mutane irinka ba, wanda bai san mutunci ba, tunda naji wannan maganar hankalina ya tashi kuma nasan cewa Allah ne yake gwada min tashi kalar azabar tun yanzu kafin tafiya tayi nisa" ya kara fashewa da kuka

Baban yara ce tayi karfin halin cewa

"Yanzu Abba kana son ce mana umma ma tana ďauke da wannan mugun cutar?"

"A'ah Baban yara ummanku bata ďauke dashi saboda yau kimanin wata biyu kenan muka raba ďaki saboda tace min tana gudun ďaukar cuta, gashi cutar ta bayyana" duk cikin kuka yake magana

Neeesat dai ta kasa cewa komai domin tana ganin kamar a mafarki takejin wannan mumnunar labarin, da kyar aka samu yayi shuru, sannan Dr yayi masa bayanin kila shi baya ďauke da cutar amma ya kwantar da hankalinsa inma yana dashi zai ďaura shi akan magani, sannan ya kara neman Abba ya bashi auren Neesat, kuma ya amince nan da sati biyu za'a daura auren, yaje ya turo iyayen sa, karshe dai Dr basu bar gidan ba har saida ya dai dai tsakanin Abba da Neesat tare da Umma

BAYAN SATI BIYU

Kofar gidan a cike yake da jama'a ta ko ina bullowa ssukeyi domin shaida ďaurin auren Dr Falal Jalal tare da amarayar sa Faineesat Adnan, akan naira dubu hamsin lakadan ba ajalan ba, anci ansha an gwangwaje tare da barin nairori, su Baby Nurse manyan kawaye domin sune akan komai na bikin, sai dai muyi musu fatan zama lafiya tare da zuri'a ďayyiba Amin Ya Allah.

TAMMAT BI HAMDULLAH

Allah Nagode maka daka bani ikon farawa lafiya kuma na sauke shi lafiya
Jinjina da yabo su kara tabbata ga Manzon Habibullah, Shafi'ullah Ya Muhammadur Rasulullahi Sallallahu Alaihi Wa Sallam.

Karku Shafa'a kuma ku manta cewa dai

Karamar Su Babban Suce Ni 'Yar Nadabo Cheee


Basira Sabo Nadabo

You've reached the end of published parts.

⏰ Last updated: Oct 15, 2017 ⏰

Add this story to your Library to get notified about new parts!

BAN AIKATA BAWhere stories live. Discover now