BAN AIKATA BA

1.3K 75 2
                                    

BAN AIKATA BA



ELOQUENCE WRITERS ASSOCIATION



Labari da Rubutawa

Basira Sabo Nadabo

SHORT STORY

My Namecy Baseera (CUTIE PIE 👄),Ina sonki sosai irin sosaaaiii ďin nan


BAN HAKURI

Zan dakatar da turo BAN AIKATA BA zuwa wani lokaci, saboda an kwantar da sister Ruqaiya Nuhu a asibiti, kusata a addu'a Don Allah, In Shaa Allah ana sallamo mu zakuji ni yadda kuke so, In Shaa Allah. Nagode

Dedicated to K4 nice Sabo Nadabo tare da Tweenie na K'Son Sabo Nadabo harda Ahmad Nuhu


Page 16 to 20

Kwankwasa kofar ďakin naji anayi sai tsoron yafi na ďazu domin kuwa na tabbata anzo kashe ni ne, to kodai aljanun ďakin ne suka dawo, toh amma inda aljanu ne shigowa zasuyi domin ko ina kofa ne a gurin su, mai makon a daina saima karawa akeyi cikina ne ya bada kululululu, ga zufar tsoro sai karyo min yakeyi ban taba zama a duhu ba dai dai na awa ďaya balle na awanni kuma tsoror duhun nake don ina gudun abokan kwanciya na su kara huda wani ramin su fito su cinye kafata kuma ba'a daina kwankwasa kofar ba, da kyar tare da addu'a na tambaya waye? Don Allah kuyi hakuri bani da komai sai Littafin Allah sai kuma rayuwata duk cikin rawar murya take magana

Hajiya Neesat nine audu mai gadi buďe Don Allah

Audu ka tabbata kaine? Don Allah kar kuyi muryar audu domin ku cutar dani

Wallahi hajia nine buďe ki gani, ba cutar dake zanyi ba

Toh audu gani nan, amma kayi alkawarin ba aikoka Abba yayi gurina ka cutar dani ba

Alhaji bai san da zuwa na hajia ki buďe

Da rawar hannu na zare padlock jikina sai rawa yakeyi kamar mazari, ban yarda shine ba har sai daya haska fuskarsa na gani

Hajia Neesat bazan iya juya miki baya ba koda duk duniyar nan zasu guje ki, abinci na kawo miki da abinda zaki haska ďaki saboda zama cikin duhu babu kyau balle ďaki da beraye kuma Don Allah ki daina kuka ki sani Allah yana tare dake domin na tabbata akan gaskiyarki kike

Audu ya akayi kasan abinda yake damuna?

Hajia Neesat ďazu bayan kin dawo daga masallaci Alhaji yake faďa min wai kin gama zubar masa da mutunci tare da duk abinda ya wakana, a yadda yake min magana hajia Neesat wutar tsanarki kara huruwa yakeyi a zuciyar sa don nagani a donsa, amma duk wannan ba komai bane tunda baki samawa Mahaliccinki ba, ki cigaba da addu'a Allah zai bayyanar da komai

Kayya audu, yaushe kenan gaskiyar zata bayyana a nan da nake ne zata bayyana ko a ina, nagode da kulawarka audu In Shaa Allah zan nemi na kaina ta ko wani hanya ne

SubhanAllahi hajia Neesat karda zuciya ta ďibeki ki aikata abinda zaki dawo kina nadama, komai yayi tsanani maganin sa Allah

Hmm audu kenan, BAN AIKATA BA sunce nayi gwara kawai naje na aikata abinda suke zargina dashi, wallahi audu ina bakin cikin kasan cewa ta a gidan da basu yarda da kaddara ba

A'ah karki ce haka hajia Neesat, iyaye kome suka miki suna nan a matsayin iyayenki, koda yau Alhaji ya yanyanka naman jikin kine kullun yana nan a matsayin mahaifinki Don Allah hajia Neesat ki daina wannan kalaman

Kai audu me kakeyi tun ďazu a gurin?

Eh na'am yallabai ina duba wani abune yayo nan da gudu, shine nake dubawa saboda karya cutar da hajia Neesat

Barshi ya cutar da itah tunda abinda ta zabawa kanta kenan, 'yar iskar yarinya wacce tayo kadon tsiya to ba'a gidana ba ka wuce a gurin nan, inba kana son aikinka ya kare bane yanzu nan, don duk wanda ya taimaki wannan yarinyar sai nayi shari'a dashi

Duk a kunne na Abba yake wannan muggan kalaman, Ya Ilahi wani irin uba ne wannan sai ga wahaye sharrrr kamar pampon daya lalace, saboda wannan maganar na fasa cin abincin da audu ya bani kuma In Shaa Allahu bazan taba rike koda cokalin gidan nan bane kota wani hanya zan nemi na kaina, amma ta ina cutar dake jikina ya shige ni wallahi ban taba zina ba wallahi Allah BAN AIKATA BA banyi ba, Allah banyi ba haba duniya me yasa tun farko baki min attishawa ba sai yanzu dana san daďin duniya, me na miki haka, me yasa zaki min haka duniya, kaico na, kaico da irin rayuwar dana tsinci kaina, duk cikin kuka take magana, na saka wannan na kulla wance har aka kira assalatu da saurar ruwan danayi alwalar isha'i shine nayi amfani dashi, har aka shiga sallah ban tashi akan sallaya ba sai da gari ya fara wayewa na gyara kunburarran fuska ta na fita domin neman na kaina nima, mallam audu yi sauri ka buďe min Don Allah

A'ah hajia ki zauna ni zan dinga baki nawa, ni zan zauna da yunwa amma Don Allah karki fita

Kana wahalar da kanka ne domin babu wanda ya isa ya hanani, nayi alkawarin bazan kara taba kayan Abba ba domin ko abincin jiya banci ba, Don Allah audu ka buďe min na fita tun kafin Abba ya fito ya koreka, Don Allah ka buďe min kofar nan audu

Hajia Neesat karm.....

Kaga audu buďe min kofa na fita kawai, bana son dogon sharhi, ka buďe min kofa nace audu, ta karashe maganar da kuka

Shikenan hajia Allah ya baki sa'a, yasa ki fita a sa'a hajia Neesat

Amin, nagode audu, ya buďe min kofa na fita amma me na rasa inda zan nufa domin ban san ko ina a garin nan ba daga gida sai makaranta, gashi yau na fito neman sana'a dole a ciki zanyi ďaya ko na faďa karuwanci ko kuma naje kasuwa koda shar kasuwa ne don na samu abinda zanci, to amma ai Abba sun ďauka yawon iskanci nake zuwa har nasamu cutar kanjamau tunda abinda suke zargi kenan wannan harkar zan faďa kuma zatafi kawo min kuďi sosai, sai nayi da hujja tunda abinda suke zargina kenan nasan wani gidan karuwai a sokoto road kuma manyan mutane ne ke zuwa gurin cen zani kodan na kara tabbatar musu da abinda suke zargi

Ga wannan fejin tukwici ne gare ki Sis Farida mutanen Uganda, nagode da kulawarki gare ni

Karamar Su Babban Suce Ni 'Yar Nadabo

Basira Sabo Nadabo

BAN AIKATA BAWhere stories live. Discover now