part 1

669 24 0
                                    

UNGUWAR BAILARI QTRS.
Y'ar karamar unguwace dake da tsirarun gidaje idan ka kwatanta da daruruwan dake a kewayenta, sai dai ita ta fita daban kasantuwarta mafi kyau da tsari da kawa fiye da sauran.
Sai dai ba abin mamaki bane kasancewar mutanen dake cikinta ba kananan mutane bane, unguwace ta masu abin hannu, kama daga kan manyan y'an kasuwa, manyan ma'aikatan gwamnati da sauransu.

Babu mutane masu wani dimbin yawa dake kaiwa da kawowa a cikinta sabanin sauran unguwannin yaku-bayi, idan da zaka zauna a ckn unguwar tsawon wuni guda zaka iya lissafa mutanen da suka shigo ko suka fita daga unguwar.
Hayaniya kuwa sai dai ka jiyota daga unguwannin dake kewaye da unguwar ko kuma titunan dake zagaye da ita.

A takaice dai zaka iya kiranta unguwa da mutanen cikinta ke raye ckn nutsuwa da kwanciyar hankali.
*A ckn rukunin gidajen akwai gdn daya fita daban, idan da za'a baka damar fito da daya tak da zaka kirashi na daban a ckn kayatacciyar unguwar ba shakka da kanka zaka fitar dashi a matsayin Wanda ya fita zakka.

* Kimanin misalin karfe biyar na yamma, A hnkl tsaleliyar mota kirar Honda anaconda Wanda matashi me suna SAGEER ke tukawa take ratsa kwaltar dake tsakiyar unguwar, yanayin tafiyar motar na kama da tukin kasaita.
Ko kuma Wanda ke tukin ba sauri yake ba ko kuma cike yake da matsananciyar gajiya, data tilasta masa rashin hanzarin.
A hankali motar ta durfafi daya Daga ckn jerin rukunin kyawawan gidajen wanda kallo daya zaka yi masa kasan ya fita daban da sauran, ta fuskar girma da kuma kawatuwa.
Tafkeken gida ne dake da cikakken zubi da tsari, duk kakai ga sani ko ganin kayatattun gidajen alfarma wannan ya wuce saninka.

AKASIWhere stories live. Discover now