part 6

106 10 0
                                    

Yayi saurin sakin murmushi tare da yin dariya yace "Ameen bana mata bakin ciki don kawai bana sonta, Allah ya bata wanda yafi muhsin komai.
...Da alama kinji haushi na batawa kawarki ko?
kiyi hakuri itama ki bata hakuri duk da cewa nima na bata, banyi hakan don wulakanci ba.
Sai domin ita soyayya kamar hadin takalmi ce, kafin ya cika sunansa na takalmi dole sai an samu guda biyu kuma dukaninsu sun zama iri daya sak!
(daga zarar daya ya banbanta da daya, sai ya zama wari da wari.)

ina fatan kin gane!!
bari na koma ciki don barcin nan bai isheni ba akwai gajiya da yawa a jikina."
ya fada tare da juyawa ya wuce kai tsaye bai ko tsaya a falon ba, ta bishi da kallo tare da cewa "kai! lallai ma wannan yayan."
ta maida kanta ga wayar dake rike a hannunta ta lalubo lambar saudat tare da kiranta amma harta katse bata daga ba, batayi mamaki ba don tasan halinta sarai.
ta mike ta tattara kayan tare da komawa taci gaba da harkokinta.

°°A duk wunin ranar sageer bai dawo ba yana can cikin abokai ana ta sabgogi muhsin kuwa na gidan babu inda yaje, sai can misalin karfe takwas na dare sageer din ya dawo.
Zaune a falon hajiya ce kawai tasa TV a gaba tana klln wani tafsirin sheikh isa ali fantami, ta amsa sallamar tashi.
ya zauna tare da kawo gwauron numfashi yace "wash!" ba tare data dubeshi ba tace "ansha yawo!"
sageer yace "ansha kam! yo hajiya kwana da kwanaki a daure fa kmr wani rago."
hajiya tayi dariya kawai ba tare data dubeshi ba, ya dan zama jknsa daga kan kujerar tare da cewa "ya naga ke kadai a falon??"
hajiya tace "ynznnan ramlat ta shiga ciki tayi sallah, yayan naku ne dai yana ciki tunda ya dawo ma ina jin cin abnc ne kawai ya fito dashi."
ai dole yasha barci gajiyar daya debo bata kadan bace, in nine shi sati zanyi banje ko'ina ba..
hajiya tayi saurin cewa "sai yayi mana kai kuma kaci gaba da aikin da zaiyi..."
sageer yayi dariya tare da saurin cewa "ah hajiya wlh ban yarda ba, yabar hutun ni zan yi masa shi yaje yayi aikin."
bai gama dariyar ba fitowar muhsin ta dakatar dashi wnd yazo  dai-dai da fitowar ramlat, muhsin ya karaso yana me cewa "sarkin aiki an dawo kenan?"
ramlat ta shigo zancen da cewa "sarkin aiki ko sarkin yawo?
banda yawo wane aiki ya iya?"
sageer ya harareta kawai.
Muhsin ya zauna tare da cewa "kinsan akwai wani me karin magana da yace 'mafi yawancin masu rashin kulawa da abu to abin yafi sonsu sai dai su basu san hakan ba.'
a tafiyata ta sati daya kamfani yaci riba har ribi uku akan yadda aka saba, wnd ko ni banyi hakan ba a ckn shekaru biyu da suka gabata, amma shi yayi."
yayi nuni da sageer.
ramlat ta tabe baki tare da cewa "ka kuma bincika sosai ba kuskuren rubuta alkaluma yayi ba??"
muhsin yace "ba rubutu ya gaya min bama, masu kula da zahiri ne suka tbbtr min da haka."
sageer ya sake hararar ramlat yace "Ni fa ko? ba irinki bane da ba abnd kika sani sai girki si shara, ko a kwara na dauki tallar ruwa sai na siyar."
ya juya ga muhsin yace "ta dauka kowa irinta ne ai, sakandire kawai tayi fa! ni kuwa  kwalin degree gareni akan kasuwanci zalla babu mis kuma snd na gama duk makarantarmu bame sakamako irin nawa."
Hajiya tace "tofah kaji yabon kai."
muhsin yayi dariya tare da gyara zama ya dubi sageer yace "gobe zamu yi zama a trade fair complex na wata-wata da muka saba, zamu tare dakai don haka ka shirya da wuri.
ya dubi ramlat yace "kanwata gobe a gyara store zuwa la'asar za'a kawo kayan abinci, don nasan sunyi kasa ko?"
ramlat ta gyada kai tare da cewa "Eh! donma dai an dan samu sauki a y'an kwanakin nan me zama ya cinye abincin yana fita sana'a, da tuni sun kare duka."
duk suka yi dariya hajiya tace "kai! wadannan yaran."
sageer ya grgz kai tare da cewa "Allah yarinyar nan ta rainani, to rumbu neni dazan yita cinye abnc ni kadai??"

Haka suka cgb da hira cikin nishadi zuwa can hajiya ta dubi muhsin tace "yauwa dazu kawun ku ya kirani daga katsina mun gaisa sosai dasu, sunce suna yi maka barka da sauka ma ya kira wayarka  a kashe ma."
muhsin yace "Eh tun safe na kasheta ban budeta ba sbd nasan in tana kunne da wahala in samu barci yadda nake so, zan kirashi ynz mu gaisa inna shiga ciki.
Zuwa sati me zuwa ma in na samu dama zamu sa rana mu ziyarce su ta gidan goggo zamu fara bi (yayar mahaifinsu dake kano) daga nan sai mu wuce izuwa katsina."
"yakamata kam!" hajiya ta fada.
ramlat ta daga hannu tare da cewa "yeee! nizan fara kiran hajara na fada mata nasan zata ji dadin hakan."
muhsin yayi murmushi tare da cewa "za'a hadu da babbar kawa kenan?"
hajiya tace "kuma babbar abokiyar fada ba."
ramlat tace "ai ta fiye tsokana ne."
sageer yace "halinku ne yazo daya itace daidai dake ai."
ramlat tayi dariya tace "haba nafi karfinta ai."
suka cgb da hirar har izuwa sanda kowannensu yabar falon.

Bayan sati daya ne kuma a ranar litinin suka shirya dukkaninsu suka nufi kano daga nan kuma su zarce katsina domin ziyara da kuma ganawa da danginsu da y'an uwansu kmr yadda suka saba daga lokaci zuwa lokaci, kwanansu daya tak a kano suka wuce katsinan.
Sai dai zuwan nasu ba wani abu ya tada ba illa wata tsohuwar magana da aka dade da yinta tsakanin mahaifinsu da kawun nasu, batu ne akan hadin aure tsakanin babban dan kawun da ramlat.
kafin rasuwarsa anyi wannan maganar kuma hajiya ma tasan da ita, sai dai AKASI daya da aka samu shine a duniya babu wanda ramlat ta tsana kamar sammani.
tunda suka je katsinan banda fada da rigima babu abinda sukeyi, karshe har marinsa tayi wanda yasa kawun yasata a gaba dasu muhsin yayita zazzaga musu ruwan bala'i.
Hakan yasa bama su cike kwanakin da sukayi niyyar yi ba suka tattara i nasu-i nasu suka yo gida, wanda hakan ya kara fusata kawun, ya kira hajiya ya sanar da ita abinda ya faru.

Itama tayi musu fada sosai, sai da sukayi mata bayani sosai sannan ta fahimci ainihin abinda ya faru duk da hakan dai tayi musu kashedin sake maimaita hakan.

°°Suka cigaba da harkokinsu ckn nutsuwa da kwanciyar hankali kmr yadda suka saba, sai bayan kwanaki uku ne kawu ya sake kiran hajiya ya sanar mata da cewa ya turo kannensa guda biyu domin tattaunawa akan yadda za'a sa auren sammani da ramlat.
Bata samu sunyi wata doguwar hira ko kace-nace ba ya kashe wayar, haka kuwa akayi misalin karfe biyun rana na ranar alhamis din Mallam musa da mallam sani suka dira a gidan.
Sun sami kyakykyawar tarba a gidan sai da suka ci suka sha, suna zaune a falon su biyu suna taba hira sama-sama hajiya ta fito ta zauna a kujerar dake nesa kadan dasu.
suka gaisa sannan mallam musa ya gyara zama yace "hajiya kmr yadda yaya yayi miki bayani kwanaki kadan da suka gabata, munzo ne akan batun aure tsakanin sammani da raulatu."
hajiya tace "to ni me zance??
ai da kun yanke abnd kuke son yi kawai kun aiwatar, ma'ana kusa rana, ku daura auren sannan ku karbi sadaki kaga kawai sai kuzo kudau yarinyar ku kai masa."

suka dubi juna tare da dubanta mal. sani yace "hajiya ai ko baki fada ba za'ayi haka, wai dama dai mun bada dama ne gareki da ita yarinyar muji daga gareku."
hajiya ta kada kai tare da cewa "muna da damar da y'ancin kenan??"
mal. musa ya gyada kai tare da cewa "kwarai..ah to ko addini akwai wannan ko mal. sani?"
ya fada tare da duban kyamushashen farin mutumin dake gefensa, mal. sanin ya gyada kai tare da cewa "kwarai kuwa."
hajiya ta juya kanta tare da kiran sunan "ramlat!!!"
ramlat din ta amsa kiran jim kadan ta fito sanye da hijabi ta zauna nesa kadan dasu, hajiya ta gyara zamanta ckn fuskantar ramlat din tace "kawunninki sunzo akan batun aurenki da dan uwanki sammani, kin yarda da auren?? kina sonsa??"
ramlat ta dan yi shiru jim kadan kuma ta girgiza tamkar ba zata daina girgizawar ba, ckn alamar dake nuni da A'AHHH!!
"jeki".
hajiya ta fada, ramlat din ta mike kanta na kasa tabar falon.
hajiya ta juyo ta dubi dattijan tare da cewa "idan har da y'ancin to kaji amsar, wato mallam shi Alhaji ya kasa fahimtar abinda nake dubawa sai shi abnd yake dubawa kawai.
yarinyar nan bata son sammani tun ba ynz ba kuma ba jiya ba, ni daku duka munsan haka. A ganina idan har ni daku zamuyi mata adalci bai kamata ayi wannan auren ba ko kadan, saninmu ne duka zamani ya riga ya canja an daina wannan hadin auren na kuruciya kuma ace anyi kenan koda kuwa an samu AKASIn yadda aka tsara..."
"watoo.. hajiya idan na fahimceki kina so ki murda hannun agogo ya dawo baya??"
mallam sani ya tambaya.
hajiya tace "um um mal. sani bawai maganar ina dawo da hannun agogo baya bane..."
mallam musa ya katseta da cewa "toh menene? bama wai dawo da hannun agogo baya ba, tarwatsa zumunci ne kike kokarin yi na tabbata idan da hadin auren nan da dangin kine ba zaki fituttuke ki hana ba.
to ki sani hajiya abnd kike kokarin yi ko kadan ba daidai bane, ki bari ayi abinda aka shirya kuma a cika a alkawarin da aka dauka."
hajiya ta dago kanta ta dubesu kmr ba zata ce komai ba sai bayan dan lkc snn tace "mallam na kasa banbance cikakkiyar manufar wannan dagiyar taku, maganar gaskiya idan da ace yarinyar nan tana son sammani da zanfi kowa farin ciki.
Amma tunda bata sonshi ina ganin a hakura zaifi saboda kada muyi abinda zamu dawo muna dana-sani."
suka dubi juna mal. sani yace "ki fadi kai tsaye kawai hajiya, kice baki amince ba kawai."
haka nake nufi!!
ta fada ba tare data dubesu ba.
suka sake duban juna cikin sigar mamaki, mal. musa ya kada kai yace "baki amince ba ma'ana ba za'ayi ba, wato y'ar damar da muka bayar itace tasa wannan zakewar ko?
toh yaya yace a gaya miki indai Alhaji Allah yaji kan rai yayanmu ne kuma tunda shi da kansa yayi wannan alkawarin toh auren nan ba abnd zai hana ayi shi."
hajiya tayi murmushi tare da juyar da idanunta izuwa duban sama tace "ko baku bada dama ba mu mun isa ace muna da dama, ka dubi tun daga bakin gate din gidannan har izuwa shigowa cknsa kasan akwai fifikon a nunawa mutanen cknsa karfa-karfa."
Suka sake duban juna mal. musa ya rike baki tare da cewa "harda gorin arziki??
tashi mu tafi."
ya fada sanda ya mike yana duban mal. sani, tare suka mike ya kada kai tare da cewa "ynz kika nuna mana manufarki, mun gode zamu koma mu gayawa wanda ya turomu abnd kika ce."
suka juya tare da nufar hanyar fita gwiwarsu babu cikakken kwari.
Tabisu da kallo kawai jim kadan kuma ta koma ciki, tunda ta shiga bata fito ba sai misalin karfe shida da y'an mintuna na yammacin ranar sanda Alh. sabi'u ya kirata.

AKASIWhere stories live. Discover now