part 22

64 7 0
                                    

Yadan kauda kai tare da saurin sake dubanta yace "amma wannan ba hujja bace da zaki rika a matsayin hujjar da zata saka ki juya min baya, kinfi kowa sanin yawan ayyukana a hakan ba karamin kokari nake yi ba.."
Ta katseshi da cewa "shi yasa nayi abinda ya dace dani  saboda ko kadan kai kam baka dace dani ba, kasan dame ni na yarda mutum yana sona??
Tayi saurin bada amsar zancen nata da cewa "ta hanyar nuna kulawarsa akaina kawai, abinda na rasa daga gareka kenan.
Soyayyar wanda ke kulawa dani tana karuwa a zuciyata kamar yada wuta ke ci a yayinda ta kama karare, sannan tana fita daga zuciya ga wanda baya kulawa dani kwatankwacin yadda ruwa ke zubewa sanda aka zubashi a rariya."
Ya bita da kallo kawai kamar ya rufeta da duka don takaici, zuwa can yadan kara sassauta muryarsa tare da cewa "amma munira karki manta gab muke da yin aure, auren nan kuma shine zai bamu damar mu kasance a tare, daga lokacin da kika zama matata kema kinsan dole duk inda naje duk yawan aikina dole idan na tashi inda kike zan nufo, yanzu kuma fa idan na tashi zanzo gidanku in kwana ne?"
Ta tabe baki tare da cewa "kenan baka da lokaci sai ka tashi daga aiki? Kuma juma'a asabar da lahadi duka a aikin kake? Meye amfanin waya to? Kenan wai kai agogo ne da kullum cikin aiki kake??"

Yabita da kallo kawai yace "munira! Ki kauda wannan maganar don Allah, ina so ki fuskanceni sosai, banzo nan don muyi sa'insa ba zuwa nayi don muyi masalaha, na karbi kuskurena kuma zan gyara, nayi miki alkawari.
Amma karki hukunta zuciyata da wannan tsatstsauran hukuncin naki, ke zaki baiwa wani labarin cewa ina sonki."
Ta girgiza kai da cewa "BAKIN ALKALAMI ya bushe kamal! bazan iya janye ra'ayina ba, ina me baka hakuri akan haka.
Akwai mata da yawa wadanda suka fi munira kyau da komai kuma kana da kudin da zaka iya aurar hudu ma, su watakila zasu iya jure rashin soyayya da kulawa matukar ka basu ci da sha shikenan, amma a wurin munira soyayya da aure sun wuce haka."

A lokacin fuskar kamal ta canja matuka, ya zuba mata ido kawai yana kallonta, na tsawon lokaci bai sake cewa komai ba.
Zuwa can ya daga kafadarsa da cewa "tom shikenan! Ance wanda kuka hadu dashi sunansa muhsin ko?
Ta daga kai da mamaki, yace "dan garin kaduna kuma a waya kuka hadu??"
Ta sake daga kai zatayi magana yayi saurin cewa "da gaske ne har yanzu baki ma ganshi ba??"
Ta sake kada kai a karo na uku tace "kwarai! Amma ya akai kasan wadannan abubuwan??"
Ba tare daya bata amsar ba ya mike tare da takawa yace "idan nine na makale murya na kiraki a matsayin muhsin fa?"
Ta dago kai ta dubeshi ya juyo yace "Ah! Bafa haka bane, amma da hakan ne ma ai da da sauki, akwai mutane da yawa da waya ta zama makaminsu na cutar mutane."

Me kake nufi??
Yayi murmushi tare da cewa "a zato na tunaninki nada yawan dazai banbance zahiri da gaibu, ashe har yanzu ke yarinya ce da bata wuce ayi mata wayo ta bata labaran almara ko tatsuniya a canja mata tunaninta ba."
Munira ta kawo gwauron numfashi tace "kamal kenan, ai nasan ba'a daki mutum a hanashi kuka ba, wannan duka ihu bayan hari ne kakeyi.
Kaga zancenka ba, tanan yake shiga ya fita tanan. (Tayi nuni da kunnenta na hagu da dama) tare da cewa "ba wani tasirin da zasu yimin."
Ya kada kai kawai tare da mayar da bakin gilashinsa izuwa idanunsa, yace "well kowanne dan adam yana da damar zabar abinda yake ganin yafi dacewa dashi, badon ni kika guda ba amma ina gargadarki da wannan zabin naki, domin da wuya idan baza kiyi da nadama a cikinsa ba.
Don daidai yake da sakin reshe ki kama ganye, kin bar wanda yake a zahiri kin kama na boye.
Akwai RANAR NADAMA, amma ba haka nake miki fata ba.
Na barki lafiya!!"
Ya juya tare da tafiya, tayi saurin cewa "idan ma haka kake fatan, da yardar Allah fatanka bazai zama gaskiya ba, sannan kaine da abin kunya daka bari na boye ya cika da yaki, yayi fafutika duk da ba'a ganshi ba amma ya kwace abinda yake hannunka, lallai wannan ya cika jarumi."
Cak! Ya tsaya kamar bazai dawo ba sai kuma ya dawo, ya fuskanceta sosai yace "ba abin mamaki bane, watakila yafini iya tsara kalamai ne..."
Ya taka tare da cewa "..na yaudara."
Kinsan wani binciken da akayi a 2001 ya nuna cewa mayaudara sunfi kowa iya tsara abubuwa na jan hankali a duniya.
Lokaci shine zai tabbatar amma kisa a ranki bayan kowanne lokaci zan iya karbarki indai kika dawo da hankalinki akaina duk dadewa, saboda ina sonki.
Ko baki gayyaceni ba kuma zan dawo, ki rike wannan."

AKASIWhere stories live. Discover now