part 18

63 7 0
                                    

°°Haka soyayyar su taci gaba da gudana suka cigaba da yin wayar da kuma ganawa ta kafar whatsapp sosai da sosai, kusan duk bayan awanni kadan sai sunyi magana.
Ba yadda yake magana ne kadai ke burgeta ba amma yadda yake yi cike da hikima, har tunatarwa da wa'azi yake mata a duk sanda suka gama waya.
Misali a wayarsu ta karshe bayan sun gama magana yace mata, "kada ki manta idan zaki ajiye waya ki ajiyeta da bismillah, haka duk abinda zakiyi ki fara da ita domin ambatar sunan Allah a duk abinda mutum zai fara shine makamin samun nasara a cikin abin, ki huta lafiya."
Takanyi murmushi a duk sanda yayi mata magana irin wannan, wanda yana daga cikin abinda ke kara hura wutar soyayyarsa a zuciyarta.

°Munira suka shiga jarrabawa gadan-gadan a shirye-shiryen kammala karatun da sukeyi, yayinda a gefe guda maganar aurensu ke kara tasowa sakamakon kusantowar da lokacin ke dadayi.
A ranar da suka kammala jarrabawar ne bayan sun gama doguwar hira da sauran dalibai da sallama da musayar lambobin waya da address sun rabu, misalin karfe uku da mintuna na rana suna hanyar dawowa gida cikin motarsu kirar pontiac sai hira suke da sadiya cikin nishadi.
A sannan ne wayar munira tadau karar tayi murmushi don tasan ko waye, sadiya ta kalleta wanda shi ya hanata daga wayar.
Sadiyar tace "to juliet ki daga mana."
Munira tace "ki kalli gabanki dai tuki kike kin tsaya gulma," takai wayar kunnenta bayan data sata handsfree sadiyar tayi dariya kawai.
Da irin sallamar data saba yi masa ta fara magana, ya amsa cikin irin sigar datayi masa sallamar, ta dora da cewa "baka saba kirana kamar yanzu ba."
Yace "Yau dinma da dalili kira nayi don nayi miki murna, barka da kuma tayaki farin cikin kammala karatu da kikayi a yau, dake da surukata."
Munira tace "gani gata ai tana jinka itama..." Sadiya ta shiga zancen da cewa "Mun gode surukina."
Yace "Ah! Allah yasa banyi zuba a kunnen surukata ba dana sha kunya."
Suka kalli juna sukayi dariya, munira tace "Na gode sosai da kulawa."
yayi murmushi da cewa "nima haka! ki samu farin ciki da nishadi don yau daya ce daga cikin ranaku na musamman a rayuwarki, kammala abinda aka shafe shekaru 3 anayi ya isa abin farin ciki, karki manta da yawaita fadin 'Alhamdulillah ala kulli ni'imatullahi.'"
ya katse wayar, munira ta kawar da ita daga kunnenta tare da tsuke fuska bayan data tabbatar ita sadiya ita take kallo.
bayan y'an sakanni kuma munira tace "ke! wai meye??"
Sadiyar tayi dariya kawai tare da mayar da kanta ga hanyar da take bi tace, muhsin naji dake kwarai lallai na sake yarda shine kawai ya dace dake amma ba kamal."
tayi shiru sakamakon dan karamin go slow da suka iso sannan ta dora da cewa "amma yakamata ace kun hadu yanzu saboda kun kwana biyu da haduwa, sannan tunda muka kammala karatu nasan maganar aurenmu zata taso kuma idan kika ce ba zaki auri kamal ba dole za'a nemi sanin wanda kike so."
takai karshen maganar sanda ta dubeta, munirar tadanyi shiru zuwa can ta gyada kai tace "hakane amma ina tunanin yadda zan gayawa abba wannan maganar Allah yasa dai ya fahimceni da wuri.."
Zai fahimta, insha Allahu zai fahimta.
Sadiya ta fada gami da karfafa zancen nata, munira tace "Toh Allah yasa."
ta fada tare da kwantar da kanta a jikin kujerar da take kai.
Can bayan la'sar sosai misalin karfe 4:20 na yamma Zaune munira a ita kadai kasancewar falo suna musayar sako ta whatsapp da muhsin kasancewar iwar haka sukafi yin hira dashi sosai, sai dariya take gami da murmushi a wasu lokutanma harta tashi ta canja wajen zama, kana ganinta dai kasan tana cikin annashuwa hirar nayi mata dadi sosai.
kiran daya shigo mata ne ya katseta, YAYANA!! (babban yayansu dake abuja).
Ta gani manne a jikin fuskar wayar, ta zaro ido murmushin fuskarta ya karu tace "yaya ne yau a gari??"
Tayi saurin daga wayar tare da kaita kunnenta, "mara kirki!! ai na dauka wayar tawa ma ba zaki daga ba."
ya fada bayan daya amsa sallamarta.
Ta girgiza kai tare da cewa "Ah haba! ni a suwa? yayana guda naki daga wayarsa ai sai a hukuntani."
yayi dariya kawai, tace "yaya ya aiki? ya abuja? ya hidindimu?"
Yace "duk lafiya kalau kanwata.."
tayi saurin cewa "sannu yaya! kuna shan fama fa, 24 hours cikin aiki shi yasa bana ma kiranka don bana son katse maka aiki."
Yace "kaji! wato dai sai kinyi y'an dabaru kinyi kwana saboda nace baki da kirki, to ai indai ba tiyata na shiga ba babu sanda kamar ke zaki kirani naki dagawa, zakiyi y'an dabaru."
ta kyalkyale da dariya tare da cewa "toh yi hakuri zanyi kokari na ringa kiranka duk bayan wata yayi maka??"
yace "sai dai duk shekara ko kuma karni."
ta sake yin dariya a karo na biyu, sai data rufe bakinta sannan yace "an gaya min kinyi rashin lafiya kwanaki can ko?"
ta gyada kai da cewa "Eh nayi ta y'an kwanaki  amma na murmure ai tuni."
Yace "toh Allah ya kara miki lafiya kanwata kidai rinka kulawa da lafiyarki sosai da sosai, saboda itace uwar jiki kuma sai da ita ake iya yin komai."
tace "sosai kuwa, ina kulawa sosai amma kasan hakan bazai hana ayi ba in Allah ya kadarto."
Imran yace "sosai kuwa!
Amma yarannan kun girma fa! kuna nufin har kun gama degree??"
Munira tadan tsuke fuska tare da matsawa daga inda take zaune tace "kai! tambaya ma kake? shekarun da kayi dai sanda kayi naka muma su mukayi kwana daya ba'a rage mana ba, banbanci kawai kai ka rigamu yi."
yace "sannan kuma nawa bangaren yafi wuya, mass comms ai shan ruwa ma yafishi wuya amma duk da hakan na tayaku murna Allah yasa me amfani ne kuma me amfanarwa."
Munira tace "ameen summa ameen! yaya."
kamar wanda ya manta ya kuma tuno yace "Ah ina kakata ne? (sadiya) banji motsintaba, duk da itama kin koya mata rashin kirkin ta daina kiran mutane gaba daya."
Munirar tayi dariya tare da cewa "ta fita tun dazu wai store zata je kasan ita bata rabo da shopping, ka kirata a wayarta tunda Allah yasa ka samu lokaci yanzu."
Yace "ai dama ni ina da lokaci sai dai in kece baki da lokaci!"
ta sake yin dariya, yace "zan kirata yanzu, sai wani lokaci kuma ki gaisar min da abokina kamal."
har runtse ido tayi kamar wadda ta zuba madaci a bakinta, ta kautar da zancen da cewa "yaya yakamata kazo gida fa! cikin wata na 9 kake rabonka da kano, karfi da yaji sun mayar dakai dan abuja."
Yace "Zanzo sai..bikinku ya karato kinsan dole inzo saboda za'asha budiri, watakila nima bazan koma ba sai da amaryata kinga daga nan kuma nidaku sai dai daga hannu."
Sukayi dariya tare, nan dai sukayi sallama.

Suna yin sallamar ne kuma kiran muhsin ya shigo ta kwanta bisa doguwar kujerar tare dakai wayar kunnenta, "ka gaji da jiran reply ne? kirana akayi a waya shi yasa."
Muhsin wanda ke zaune a ofis dinsa tuni ya gama tattara komai nashi hirar yake jira su gama yayi gida, kamar yadda ya sabawa kansa a yanzu kullum sai sunyi magana da ita sau uku, da safe kafin ko bayan ya fito.
sai kuma da yamma inzai tashi bayan ya gama aiki, da kuma da daddare sanda suka samu nutsuwa sosai.
Dafe da tebirin da hannunsa daya yace "ta gaya min ai."
Kamar me shirin harara haka ta kauda fuska tare da cewa "wacece??"
yace "sai dai in gaya miki kome tace min, cewa tayi 'the number you are calling is busy, please try again later.'
Sukayi dariya tare, munira tadanyi gwauron numfashi tace "wannan ai kwamfuta ce, na dauka dai wata ce kake da ita kuke hira bayan ni."
Yayi saurin cewa "Ah haba Allah ya kiyaye!! ina da me muryar zinare zancen wa kuma zan tsaya saurara? nida jin muryar wata a waya sai dai ko wannan din dake gayawa mutane sako in sunyi kira itama Allah yasa ta mutu mu huta."
Munira ta kyalkyale da dariya har sai data tashi zaune.

Haka dai suka cigaba da hirar cikin nishadi har kusan magariba sannan sukayi sallama, 6:25 abinda muhsin ya gani kenan sanda ya daga kai ya kalli agogon ofis dinsa.
"Kakk! yamma har tayi haka?"
ya gyara zaman bakin tabaran dake idonsa tare da mikewa ya gyara suit din jikinsa tare da daukar jakarsa yayi waje, a motar da yazo sabuwar corolla S 2017 da aka kawo masa ita daga japan sati biyu da suka wuce yahau kai tsaye yayi gida.

°°Bayan sati daya da kammala jarrabawarsu munira ne kuma sukayi gagarumin biki na murna kammala makaranta kamar dai yadda kowa yasan al'adar ce ta karatu kowanne iri matukar aka kammala sai anyi wannan bikin, tun misalin karfe 2:00 na rana suna makarantar sai can da yammaci lilis suka baro makarantar.
Anci ansha an sake yin sallama da lakcarori da sauran dalibai, vice cencelor na jami'ar bayeron da kansa ne yayi musu bayani na karshe cikin salon tayasu murnar yayesu da jami'ar tayi a wannan rana.
Dukkaninsu jikinsu sanye yake da rigar graduation me dauke da tambarin makarantar, abokai da kawaye anyi hotuna sosai kamar ba za'a rabu musamman wadanda suka shaku sosai, a haka dai karshe aka watse kowa ya kama gabansa.
Sanda suka isa gida magriba tayi bayan sunyi sallah ne kuma suka fito falo, inda yara da iyayensu mata ke zaune suka yita hira kamar yadda suka saba kusan kullum, bayan sunci abinci ne kuma zuwa can misalin karfe tara saura dan wani abin munira da sadiya suka dawo dakinsu suka dora da wata hirar.
Zuwa can ne kuma amira ta shigo dakin daga yin sallamarta tun daga bakin kofa sadiya tace "malama meya kawoki??
koma inda kika fito, ki zauna cikin sa'anninki yara ba zakiyi ba sai son girman tsiya."
amirar ta tsaya kamar ta fashe da kuka ta tabe baki tare da cewa "to Abba ne yace a kiraku, idan kuma ba zakije ba sai kiyi masa bayani."
ta juya ta fice duk da kiranta da munira keyi baisa ta juyo ba, suka dubi juna ita da sadiya tace "gaskiya kina shakawa yarinyar nan da yawa."
Sukayi dariya, sadiya tace "ai inta tashi yimin nata rashin mutuncin sai naji kamar na bugeta don haushi."
ta mike daga zaunen da take tare da cewa "tashi muje tunda kika ji kiran gaggawa haka daga Abba to akwai magana."

•Zaune suka tarar dashi cikin dakinsa bisa kujera rike da wasu takardu yana dubasu daya bayan daya, wadanda da alama na wasu kayan ne daya siya kasancewarsa hamshakin dan kasuwa."

AKASIWhere stories live. Discover now