part 23

53 6 0
                                    

muhsin yayi murmushi kawai don yasan inda ya nufa ya dora da cewa "tun jiya muke abu daya amma kaki amsa mana abinnan."
Muhsin ya dago kansa daga jikin lallausar kujerar da yake kai yace "um um bawai naki bane m. bash ka fahimta, wato ina nuna maka cewa idan har nayi tafiyar nan zata shafi wasu abubuwa nawa sosai saboda tafiyar wata daya bawai ta kwana daya bace."
m. bash din yace "amma a yadda nasanka da yadda tarihin gwagwarmayarka ya nuna ban zaci zaka..ji tsoron tafiyar wata daya kacal ba. (yakai karshen maganar da yin y'ar dariya.)
muhsin yayi murmushi tare da cewa "bawai tsoro bane amma ka fahimci cewa kowanne mutum yana da irin tsarinsa da yadda yake tafiyar da al'amuransa, maganar gaskiya idan har zanyi tafiya ta wata daya curr to yakan daukeni tsawon wata 6 ina shirya mata amma bawai bakatatan haka ba."
wani dan farin mutum daya daga cikin wadanda ke gaf m. bash yace "amma alhaji muhsin wannan wata dama ce da mutane da yawa suke nema, wasu suke roko yayinda da yawa zasu iya biyan ko nawa don ganin sun sameta, amma kai gata tazo maka kana so kayi rejecting dinta."
Muhsin yadan juya kujerar da yake kai yace "ai ba komai ne da mutane ke so ni kuma nake sonshi ba, mudai magana akan abin amma ba wannan ba."
shiru yadan gudana na dan lokaci, zuwa can m. bash din yayi gyaran murya tare da gyara zama.
yace "amma ni ina ganin ba'a dora mana laifin matsewar da abin yayi ba, saboda tun kimanin watanni uku muka kammala zaboku.
sannan tun kimanin watanni biyu da suka wuce muke gayyatarka akan maganar amma baka amsa mana ba, sai yau da abin yazo gaf da gaf sannan kazo tabbas daka zo tuntuni da tuni mun kammala duk abinda yakamata kamar yadda muka kammala da daya abokin tafiyar taka mr. edison godwill ."
ya fuskanci muhsin sosai tare da cewa "wato ka fahimci cewa mun zabeka ne akan dukka  sauran mutanen dake arewacin kasar nan saboda dalilai da yawa,  dr. godwill kwararren malami ne daya lakanci fannin tattalin arziki..."
muhsin yace "ya haddace komai akan tattalin arziki kamar yadda ya haddace hanyar gidansa."
sukayi dariya sannan m. bash yace "kasan shi ba, to sannan kai kuma matashi ne me karsashi daka lakanci kasuwanci a aikace ba'a karance ba, hadinku zaiyi matukar dacewa kuma zaku kawowa kasar nan abinda ake so wanda wannan ne zai bamu dama mu kanmu a sake bamu wannan damar shekara me zuwa.
shi yasa muka sa dukkanin karfin gwiwarmu akanka, koba komai kayi don wannan mana."
muhsin yadan sake juya kujerar da yake kai kansa na kwance a jikinsa yadanyi nazari na dan lokaci tare da dago kansa yace "ok! shikenan zanje."
suka yi saurin duban juna suna masu murmushi, yace "amma da sharadi, maganar gaskiya sai dai a dage tafiyar nan daga gobe don bazan iya tafiya a gobe ba."

m. bash yace "muhsin bamu da ikon yin hakan saboda a bisa tsarin da yadda aka shirya taron dole ne ya zama dukkaninku daga sassan duniya kun hadu a jibi, akwai taron farko na fuska da fuska da zaku gabatar da misalin karfe tara na safe, kaga kenan ya zama dole ku tashi zuwa suwizalan a gobe."
yakai karshen maganar yana me duban muhsin din, muhsin yace "shikenan yana iya? amma dai gaskiya ban taba yin tafiya irin wannan ba, ba karamin canja min abubuwa zatayi ba wallahi."
m. bash yayi murmushi yace "a hankali komai zaka yishi ka tsara, munji dadi sosai."

Wani dake gaf dashi ya mike tare da zuwa ga muhsin ya ajiye wasu files a gabansa, muhsin yabisu daya bayan daya yana sa hannu har izuwa karshe.
sannan mutumin ya dawo, duk suka mike m. bash yace "congratulations bc. muhsin, Allah ya bada sa'a kayi gogayya da takwarorinka na duniya ka kwato mana lambar yabo me daraja ta farko.
gobe zaku tashi jirgin safe karfe 11:00 na safe, amma dole kuzo kasa da karfe 10:00 na safe tunda nasan ba'a abuja zaku zauna ba.
akwai ganawa da zakuyi da wasu manyan jami'ai, daga nan ministan kasuwanci da kansa zaiyi muku rakiya izuwa airport, kana da damar tahoha da y'an rakiya da basu wuce mutum 7 ba."
ya mika masa hannu suka gaisa tare da cewa "congratulations once again BC. muhsin."
muhsin din yabisu duka suka gaisa, tare da ficewa."
wanda shine ya kawo karshen doguwar ganawar da sukayi.

Bayan fitowarsu kai tsaye reshensu na abujar suka wuce muhsin ya duba halin da harkokin nasu ke ciki kamar yadda ya saba duk sanda ya shigo abujan, bayan sun kwashe akalla awanni biyu anan ne kuma tare suka fito izuwa motocin nasu.
isowarsu keda wuya kuma muhsin ya dubesu tare da cewa tom yanzu mun gama abinda zamuyi a cikin abuja, ya dubi garzali tare da cewa ina mukayi kuma??"
garzalin ya duba wani faffadan littafi dake hannunsa tare da cewa "zamuyi niger ne akwai taro na hukumar consumer protection council ta kasa, karfe 1:00 na rana daga nan zamu wuce cyblose center inda zaku jagoranci rufe bada horon da sukayi.
daga nan mu wuce koma kaduna kana da meeting da wakilan kamfanin talla na Almoa, da misalin karfe shida na yammaci."

Muhsin yadan cilla idanunsa kamar me nazari ya shafi fuskarsa da cewa "dankari!! Allah ya bamu ikon aiwatar dasu, yaune kawai ai gobe iwar haka mun bar kasar."
garzali yayi murmushi zaiyi magana muhsin ya katseshi da cewa "um! kaga kafar yawo har wani murmushi yake bada kai zamu ba ai."
duk sukayi dariya garzalin yace "sir duk dokin nan da nake ace babu ni? ai da tsuntsu kawai zanyi na biyoku."
Suka sake yin dariya, muhsin ya taka tare da cewa "yanzu abinda za'ayi zaku yi gaba ku wuce kai tsaye, ya dubi garzali da malam yace "mu kuma ba yanzu zamu bar abuja ba ina so inkai ziyara kafin na tafi tunda innayi tafiyar nan kuma sai sanda na dawo.
in yaso daga can kamfanin sai mubi bayansu, tunda ai da sauran lokaci."
yakai karshen maganar yana me duba rantsatstsen agogon dake hannunsa dan gaske, sai sheki yake yana daukar ido."
ok! sir!!
suka amsa, su abdul suka juya shi da sauran y'an tawagar yayinda muhsin tare da garzali da malam din suka wuce kai tsaya izuwa area 11 garki abuja."

AKASIWhere stories live. Discover now