part 5

112 10 0
                                    

"kai kuwa ya akai baka dawo ba, ba kira ba sako ga wayarka a kashe??"
hajiya ta fada.

Muhsin yace "hajiya wlh abubuwan ne suka kara yawa fiye da dah, wayar tawa kuma faduwa tayi a airport na egypt tun sanda muka sauka acan, har muka gama abnd zamu yi a egypt  (inda anan muka bata lokaci) babu waya a hannuna, sai da zamu dawo ne na samu wayar a wajen jami'an airport din ayau da asuba."
tun daga nan kuma ban budeta ba sai yanzu saboda tana ckn kayana muna dira a lagos kuma meeting din nan muka wuce..."
a takaice dai yanzu yaya kun gama komai gida kawai zakuyo??
ramlat ta fada tana me goge kumatunta, muhsin yayi murmushi tare da cewa "mun gama komai kanwata gobe da sassafe zamu yo gida misalin 11:00 ma mun dira da yardar Allah."
Allah ya yarda ya kawoku lfy.
hajiya ta fada.
ya amsa, ramlat tace "karka manta da tsarabata."
Sageer ya zaro ido tare da cewa "kaga hnkl ya kwanta harma zancen tsaraba take yi."
duk suka yi dariya.
sun dan taba hira kafin daga bisani su kammala wayar, jim kadan kuma falon ya watse duk suka nufi gadon barci cike da nutsuwa.
Ramlat kuwa saudat ta fara kira ta sanar da ita halin da ake ciki tayi farin ciki a matsayinta na masoyiyar muhsin kmr yadda take ikirari, sun danyi hira kafin suyi sallama da saudat din bayan data yi alkawarin zuwa gidan a gobe."

••••       ••••       ••••
WASHE GARI kmr yadda muhsin din ya fada misalin karfe sha daya da abn baifi mintuna sha biyu ba dan karamin jirgin irin na fitattun y'an kasuwa ya dira a filin jrgn saman na kaduna, sageer ne yazo tarar muhsin din tare da wasu daga ckn manajojin kamfanin AIS Nig. ltd.
Bayan sun gamawa gaisawa da manajojin nasa ne kai tsaye yahau mota suka yo masa rakiya izuwa gida,  bayan sun iso ne yadan gana da manajojin nasa na y'an mintuna gami da yi musu godiya suka juya izuwa ofisoshinsu sageer da muhsin suka jera izuwa ckn gidan.

Murna ta karade gidan tamkar wanda yayi tafiyar wasu shekaru ya dawo, harma da baki da suka kawo ziyara gidan kmr saudat da kannenta, da wasu daga ckn makotansu dadai sauransu.
Bayan da suka gaggaisa ne kuma ya wuce ciki nan fa ya fara karbar wayoyi daga mutane daban-daban, kama daga abokansa, yaransa da sauransu.
Sageer kuwa suna dawowa ya canja kaya yadau mukullin mota ya fice, "akuyar daure ta samu sake."
a cewar ramlat.
Sai can da yayi sallar azahar sannan ya fito falon, zaune bisa kujera saudat ce rike da wayarta a hannunta yayinda ramlat ke can daya bangaren falon sashen da tebirin cin abinci yake wanda irin labulen nan me zare ya rabasu da falon amma kana iya hango wnd yake can shima yana iya ganinsa.
"Toh ai gashi ma ya fito".
Saudat ta fada sanda ta nunashi gami da irin kallon data saba yi masa a duk sanda suka hada ido, ya bita da kll kawai tare da juyawa ya nufi inda ramlat take yana me cewa "me kuma aka girka min haka sai kamshi yake??"
ramlat tayi murmushi kafin ya karaso tace "tambayi saudat don itace karfin girkin."
saudat ta mike ta taka cikin nutsuwa tare da cewa "Na fada masa kuwa? inda ba kasa ai nan ake gardamar kokowa, gashi ga girkin ai sai ya gani da idonsa.
ya juyo ya dubeta sanda yake zama ya kakalo murmushi ya dora a fuskarsa tare da cewa "toh bari in gani amma karasa zubawa."
ya fada yana me duban ramlat din, saudat ta karaso tare da jan kujera ta zauna.
ramlat ta gama tare da juyawa tace "bari naje nayi sallah."
muhsin yace "a'ah baki ci ba ai ke.."
ni ai bana jin yunwa kune kuka sha wahala, ita hidimar girki kai kuma kasha hanya, ni din ma kuma sallah kawai zanyi.
ta fada tare da wucewa.
ya dawo da kansa saudat tayi masa wani kallo yayi saurin dauke kansa ya jawo farantin abincin tare da fara ci, yayinda taci gaba da bin kyakykyawar fuskarsa da kll.
duk da ba ita yake kallo ba amma yasan cewa idonta nakansa, hakan yasa ya kakalo hira da cewa "amma girkin naki yayi matukar dadi."
Tayi murmushi me fitar da sauti 'hmmmm!!' tare da cewa "Allah ko? ai na gani daga yanayin lomarka, ko kasan cewa na roki alfarmar abarni nayi maka kuma na bata awanni da yawa duk don nayi maka wanda zai gamsar dakai??"
ya grgz kai tare da cewa "bansani ba amma nagode."
ta sake yin murmushi a karo na biyu.

Shiru ya sake gudana tsakaninsu zuwa can tace "Muhsin!!"
kansa na kasa yace "na'am!!"
ka dago mana naga kwayar idonka.
ba tare daya dago din ba yace "ai kunne ke ji ba kwayar ido ba."
ta daga kai tare da cewa "nace ka dauka zanyi hakan a banza ne."
ya grgz kai tare da cewa "a'a nasan ba a banza kikayi ba, a tunanina kinyi ne sbd mutuntaka da girmamawa da kuma karramawa wnd dama can akwai ta tsakanin ahalinmu da naku."
tadan tauna lebenta tare da cewa "uhm! hakane amma akwai abinda baka fada ba a ckn maganarka, ma'ana kayi tuya ka manta da albasa."
har yanzu kan nasa na kasa yace "unhum! me na manta??"
ta dubeshi sosai tare da cewa "soyayya!!!!"
ya dakatar da cokalin dake daf da shiga bakinsa sanda ya dubi saudat din a karon farko tunda ta fara maganar, yaci gaba ba tare daya bata amsa ba.
Zuwa can tace "da mamaki ace baka san cewa ina bala'in sonka ba."
Sai daya kai lomar daya dauko sannan yace "na dade da sani mana."
tadan bishi da kll fuskarsa ta a sake tare da cewa "bana jin ka fahimci abnd nake nufi sosai."
ya ajiye cokalin dake hannunsa tare da hade hannayen nasa akan tebirin yace "kece dai kika gaza fahimtar abnd nake nufi..."

"nice ban fahimceka ba kokaine baka fahimceni ba duk bashine MANUFA TA ba, so nake kawai naji amsa daga gareka na kuma ga 'feeling' a tattare dakai."
ta fada sanda ta kura masa ido.
yace "amsa!! feeling!!
an samu AKASI domin dukkaninsu ba zasu zo miki a yadda kike zato ba..."
kirjinta ya buga da karfi idonta ya zaro waje tace "ban gane abnd kake nufi ba."
Ya dubeta sosai tare da cewa "na dade da fahimtar kina sona kmr yadda ya kamata ki dade da fahimtar bana ra'ayinki, SOYAYYA HADUWAR ZUKATA BIYU CE A WURI DAYA bawai bangare daya kawai ba.
ki dawo da zuciyarki daga yawon data tafi domin bulayi kawai take, abnd take son samu bazai samu a gunta ba, domin babu soyayya a tsarin rayuwata yanzun."
ya fada tare da jawo farantin abincinsa yaci gaba da ci babu wani damuwa a tare dashi, ita kuwa hawaye ne kmr an jawo su suka yo waje daga idanunta tabishi da kll kawai tamkar zata hadiyi zuciya ta mutu!!

"Ka fito kai tsaye ka fada min kawai, amma karyane! ni nasan BABU WANI DAN ADAM DIN DAYA ISA YA RAYU BA TARE DA SOYAYYA BA KODA KUWA ACE KIYAYYA CE KE GUDANA A JIKINSA BA JINI BA."
yayi murmushi tare da cewa "kinzo wurin, kwarai ina da masoya kuma akwai soyayya a ckn jini na amma bana jin in akwai taki a ciki...shi yasa babu wani 'feeling' naki a tare dani."
ya mayar mata da martanin gatsen ba tare daya dubeta ba.

ta goge kumatunta duk da hawayen dake gudu bai tsaya ba tace "koda ban baiwa kaina tabbacin samun yadda nake so ba amma banyi tsammanin haka daga gareka ba."
nima nasan ba haka nake ba..
ya fada tare da dorawa da cewa "na yarda da mutuntaka da girmamawa amma ban yarda da yaudarar kai ba, ina nace ina sonki na yaudareki kuma na yaudari kaina bazan iya sonki ba kuma bazan iya auranki ba!!
wannan shine magana, KIYI HAKURI!!"
..ba komai, ta fada da sheshsheka tare da mikewa tace "ba komai hakuri ya zama dole ai, duk da ina da ZAFIN SO amma ban kasance mara zuciya ba.
muhsin koda gwal aka halicceka na hakura dakai, sannan ko kai kadai ka rage namiji a duniya bazan aureka ba, kayi da y'ar halak! kuma y'ar gaske!!"
ta juya tabar wurin, kansa na kasa bai ko dago ba yace "kin bar jakarki".
kmr ba zata tsaya ba sai kuma ta tsaya cak! ta juyo taja jakar tata tare dayi masa wani kallo ta juya tabar wurin, ko kallon inda take baiyi ba ya dauko kofin lemo yakai bakinsa."
daidai sanda ta dawo falon ne ta nufi kujerar data zauna ta dauki wayarta tare da juyawa zata bar falon, daidai lkcnne ramlat ta fito ta bita da kll tare da duban inda muhsin yake tace "badai har tafiya ba??"
saudat ko waigowa bata yiba bare ta bata amsa ta fice da sauri, fuskar ramlat ta canja tadan tabe baki da tmbyr kanta 'meye kuma ya faru?'
ta taka tare da karasawa inda muhsin yake ta danne tare da cewa "abnc yayi dadi har an cinye??"
yace "indai abncnki ne zan cinyeshi duk yawansa."
na gaya maka saudat ce...
kada kiyi min karya don ba halayyarki bace, ya katseta tare da dorawa da fadin "ko a mafarki nasan dandanon abnd kika girka domin tun kina yarinya ke kike dafa mana abnc ko kin manta??"
ramlat tace "meya faru kai da ita??"
muhsin ya dauke kansa daga kanta tare da cewa "shirinta baiyi ba don bana ra'ayinta koke kin san haka, gsky na gaya mata sbd bazan yi mata karya ba."
ramlat tace "amma yaya banji dadi ba, saudat na sonka kwarai tana kulawa akanka fiye da saninka tsakanin shekaran jiya da jiya baka ji yadda ta shiga tashin hankali ba, ni na bata shawarar ta gaya maka abnd ke ranta dana san haka zakayi mata da ban bata wannan shawarar ba."
ai laifinki ne.
ya fada yana dubanta.
tace "kmr yaya??"
ya gyara zama tare da cewa "ke a tunanini wane dalilin zan iya rika dazai sani auran saudat??"
ramlat tace "meye aibinta??"
koda bata dashi to ni tana da aibu da yawa a gurina kuma bazan taba ganin daidai dinta ba don bana sonta..
ya fada.

Ramlat tayi shiru kawai kmr bata da sha'awar sake yin magana, zuwa can tace "yaya!!" zan iya fada maka gaskiya??"
ya dago kai tare da cewa "a cikin masu yin hakan kece ta daya kuma mafi karfin fada aji."
tace "koda ba saudat ba lkc yayi.. domin girma ne yake kara zuwar ma, ban taba ganin mutum irinka ba kokai babu aure a tsarin rywrka??
ko a islamiyya kawayena da yawa kan ziyarci gidajen yayyensu ina sha'awar hakan ma2ka, sai dai ni bani da wurin zuwan."
muhsin yace "idan kin gaji da ganina basai kin bullo tanan ba.."
duk da fskrta babu fara'a amma sai da tayi dariya, tare da cewa "habawa nina isa??"
ya mike tare da cewa "ki tayani da addu'ar Allah ya kawo min wadda zatayi daidai dani, me irin halina gaba daya, wadda da zarar aka kalleni aka kalleta za'aga kama.
amma ke kanki kinsan babu dacewa tsakanina da saudat."

Ramlat tayi kasa da kai kawai tare da cewa "Allah ya baka!!
itama Allah ya bata wanda ya fika."

AKASIWhere stories live. Discover now