part 17

68 7 0
                                    

Sadiyar har takaici ne yakamata ta kura mata ido kawai, munira ta dago kai tare da cewa "Duka tambayoyinki A'A ne amsarsu, amma da kin tambayeni 'ina sonsa?' anan ne kawai zance miki EH!"
Wane irin hauka ne wannan??
sadiya ta tambaya.
Munira tayi yake tare da cewa "haukan SO ne, shi dama ba wani hankali gareshi ba, kurma ne baya ji sannan kuma makaho ne baya gani, ni kaina nasan bai kyauta min ba daya zo min akan wanda bansani ba a kuma lokacin da nake da wanda na sani a hannu..."
dama ba son kamal kike ba??
da sauri sauri sadiya ta cillowa munira tambayar.

Munira ta girgiza kai tare da cewa "bana sonsa!!"
Hakan yasa sadiya ta kalleta da sauri, ta dora da cewa "a baya ni kaina na dauka son kamal nake amma zuwan muhsin sai yasa na dandani ainihin meye so badon shi ba da watakila har in mutu bansan meye so ba.
SO fa yana nufin shauki, yarda da aminci, hade da kulawa da kyautatawa gaya min daya da nake samu daga kamal, amma daga haduwata da Muhsin a kankanin lokaci na samu duka wadannan, gaya min me yasa tsuntsun sona bazai tashi daga kan kamal ba.
Ba ina tunanin karbar soyayyar muhsin saboda kamal bane, tunanina kawai akan waye MUHSIN din da kuma ainihin manufarsa."
Sadiya tace "baki karbi soyayyarsa ba??"
munira ta girgiza kai ta kwashe labarin abinda muhsin ya gaya mata ta gayawa sadiya, wanda yasata shiru tana nazari.
Zuwa can tace "ya iya tsara magana kam! amma karki manta akwai mutane da yawa da sunfishi ma iya maganar da za'a yarda dasu karshe ta tabbata mayaudara ne, idan kikayi tunani kina da abinda zaisa a biyo miki ta wannan hanyar don yaudararki."
me kenan? munira ta tambaya.
sadiya tace "dukiya!! itace kadai abinda mazan yanzu suka fi so fiye da mata, mayaudara kuma ita suke rubibi."
munira tace "baki da masaniya akan AIS nig.ltd? don yace kamfaninsa ne."
Sadiya ta tabe baki tare da cewa "ina da masaniya sosai ma, kamfanin odar kayan sawa ne kowanne irin launi kama daga kanana izuwa manya da shaddoji, atamfofi, les, material, da yadi.
dama kuma kaya na gwala-gwalai da sauransu, akwai kayan ma dasu kadai ke kawo irinsu a najeriya.
Amma wane tabbaci gareki cewa shine da gaske? idan kuma karya yake fa??"
Munira ta kalleta kawai tare da komawa izuwa zaman da tayi tun dazu tace "shi yasa nace ba zaki fahimceni ba, saboda ba kece ni ba shi yasa ba zaki ji abinda nake ji ba, na tabbatar idan ba gaskiya ya fada min ba maganganunsa bazasuyi tasiri akaina haka ba."
Sadiya ta dafa kafadunta ta baya tare da yin murmushi tare da cewa "nima haka nake fata Allah yasa gasken ne, bawai bana sonki dashi bane amma ina sanar dake abinda ka iya biyo baya don ya faru da yawa.
Ke kimtsatstsiya ce kuma kamilalliya bana son abinda zai tarwatsa miki rayuwa, yadda nake son na rayu cikin farin ciki da annashuwa haka kema bana son abinda zai baki matsala ko kadan don matsalarki tawa ce."
Munira ta jawo hannunta ta bayan tare da cewa "na sani mana sadiya, nasani tun da dadewa kuma duk abubuwan da kike fada shine dai tunanin da nake yi nima amma bansan me yasa na kasa rinjayar da mummunan zaton akan kyakykyawan zaton da nake masa ba..."
ta yiwu haduwar taku akwai alkhairi ne a ciki.
sadiya ta fada abinda yayi saurin juyo da munira kenan, ta sake hada hannunta cikin nata tace "yanzu kika kara tabbatar min kece dai sadiyar nan da bata bari na fadi a jarrabawa sai ta taimakeni koda da satar amsa ne."
Sukayi dariya sanda suka hada goshinsu guri guda, sadiya ta dago kai tace "abu daya zakiyi karki kirashi ki zauna kawai kiyi shiru kici gaba da addu'a hade da nazari, idan har kika ji yarda dashi na karuwa a zuciyarki da kuma son ki kirashin to kawai kiyi hakan.
amma..idan har kika ji yana raguwa ko kuma Allah ya jefo barci ya tafi dake to shikenan sai ki dauka haka Allah ya nufa, haka idan har kika kirashi a darennan bai daga ba to karki yarda dashi domin idan har son gaskiya yake miki yadda kika kasa runtsawa to shima bai kamata yayi barci ba."
Munira ta kara yin murmushi tare da jinjina mata tace "sannu..sannu me azanci, Allah ya kara hikima da basira."
Sadiya tace "ameen! nikam barci nake ji sai Allah ya tashemu lafiya."
ta janye hannunta daga jikin na munira ta koma gadonta ta kwanta, munira ta bita da kallo kawai.

11:50 na dare kamar yadda ta kalli agogon har yanzu idanunta a bude suke sakamakon muryarsa dake dawowa kunnuwanta cikin salon maganar da bata taba jin amon murya mai dadinta ba, tattausan lafazi da kuma hikimar zance.

Haka shima har misalin Karfe 12:00 na daren yana zaryar a dakin babu ko alamar zai daina, sai sannan ya koma jikin gadon ya zauna a kasa.
Zuwa can kuma ya shiga yayo alwala ya jawo sallaya ya fara sallah, duk raka'a biyu idan yayi sai ya daga hannu yayi doguwar addu'a ya shafa sannan ya mike ya dora da wata.
Sai misalin 1:30 na daren ya nade dardumar tasa tare da dawowa bisa gefen gadon ya zauna ya dubi sageer dake barci harda magagi ya dafe kai tare da kawo dogon numfashi kawai.

Tuni ya fara fitar da rai da zata kirashi don yasan tuni tayi barcinta yanzu, shine kawai ke wahalar da kansa.

Bayan abinda baifi mintuna biyu bane kuma yayi saurin dagowa tamkar wanda ke barci aka watsa masa ruwa me tsananin sanyi, ya dauko wayar dake ajiye a gefen damansa data dauki ringing har wani kadawa take sakamakon bayan karar ya kuma seta ta a vibration.
Cin karo da sunanta kamar yadda ya rubuta manne a jikin wayar yasashi mikewa A hankali damuwar data mamaye ilahirin jikinsa ta kuma bayyana a fuskarsa ta fara gushewa.
Cikin kankanin lokaci murmushi ya maye ya maye gurbinta, madadin kuma ya daga wayar sai ya fuskanci alkibla tare da yin sujjada ta musamman, wannan wai ta godiya ga Allah ce daya karbi addu'arsa ya cetoshi daga fadawa mawuyacin hali.
Sai daya dago sannan ya daga wayar a hankali ya karata a kunnensa ya seta muryarsa can kasa sakamakon sanin cewa dare ya tsala, yace "kece? ashe zaki kirani? amma sai dana fitar darai??"

Zaune take a kasa manne a jikin bango tadanyi shiru sannan tace "ashe bakayi barci ba??"
yace "tayaya zan iya barci bayan ban iya sanin matsayina ba, yau itace ranar karshe harna gama fitar dare daga amincewarki, tunanina ya koma akan zan iya wayar gari da lafiya gobe ko kuma a'a!!"
Munira tace "bakai kawai ba, zuciyata nima taji irin wannan kuma tsoro ne yasa na kasa kiranka tuntuni, akance min wai akwai mayaudara da maciya amana cike fal a cikin duniyar nan.
ni kuma tunanina sai ya gaya min duk da haka akwai masoya na gaskiya, a jikina naji kai ba mayaudari bane."
Muhsin yayi murmushi tare da cewa "nagode da yarda dani da kikayi da wuri haka, nayi miki alkawarin duk me kushe abinda kikai zan bashi kunya."
Munira tace "yauwa shine babban abinda zan roka daga gareka, ka sani na gasgata kyakykyawan zatona akanka, na yarda dakai na fifita soyayyarka duk da kana matsayin boyayye a wurina, na sadaukar da zuciyata da yardata akanka don Allah karka..."
Muhsin ya dakatar da ita da cewa "basai kin rokeni ba ya zama dole in tabbatar ban baki kunya ba kuma ban watsa miki kasa a ido ba, na rantse da ubangijin daya halicci SO ya sakashi a cikin zukatanmu bazan yaudareki ba, bazan juya miki baya ba sannan bazan gujeki ba.
Allah ya zama sheda Nayi alkawarin karbarki a duk yadda na sameki, in soki a duk yadda na ganki sannan na godewa Allah a duk yadda ya bani ke.
Nayi alkawarin zan cika zuciyarki da soyayya har sai kin manta cewa akwai wata abu me sunan kiyayya a cikin duniya."

Munira ta goge hawayen da sukayi saurin gangarowa daga idanunta tace "nagode muhsin, ina rokon Allah ya shiga soyayyarmu ya dafa mana ya cire mana dacin dake cikinta idan akwai."
Muhsin yayi murmushi tare da cewa "ameen masoyiyata munirat! kinsan kuwa a yanzu haka ma ruwan sama ne ke zuba? karin alama kenan ta albarka a cikin soyayyarmu."
munira tace "kai kana daga murya dare ne fa!"
ya rike baki tare da cewa "au! na manta, wai irin na shiga shaukin nan na masoya ai harna manta kusan biyun dare yanzu na dauka biyun rana ce."
Sukayi dariya a hankali yadda su kadai suka ji kayarsu, ya zarce da cewa "yanzu dai dare yayi ki kwanta kiyi barci cikin nutsuwa da kwanciyar hankali, ki kuma shirya farkawa a matsayin sabuwar bakuwa a cikin DUNIYAR MASOYA datazo da salon soyayyar data banbanta data saura.
Domin ita ta zabi nata masoyin da kanta ba kuma tare data taba koda ganinsa ba, idan har Allah ya nufa ko bayan babu mu duniya zata tuna da cewa anyi WASU MASOYA muhsin da munira masu abin AL'AJABI.
sai da safe, I love you!!"
ya fada sanda ya rufe zancen.
tace "tom sai da safe!"
Au ke ba zaki ce kina sona ba??
ya fada da karkata fuska tamkar yana kallonta.
tadan rufe fuskarta a jikin bangon tare da katse wayar.
ya saki murmushi tare bin wayar tashi da kallo.

•Ta mike cike da karfi irin wanda tadade bata ji irinsa ba, ta koma kan gadonta ta kwanta tare da tsara masa text message da manyan bakake kamar haka:
I LOVE YOU TOO!!
yana zaunen sakon ya shigo masa ya saki murmushi kamar bazai kare ba, wani farin ciki ya lullube zuciyarsa bayan tsawon lokaci sai yanzu yaji ya dawo daidai.
Ya mike tare da komawa kan gado ya kwanta ji yayi kamar ya tashi sageer yayi masa albishir da wannan abin farin cikin amma sai ya danne, ya kwanta kawai murmushi ya kasa tsayawa a fuskarsa har yayi barci bakinsa bai rufu ba.
Cikakkiyar nutsuwa ta dawo masa da yake ya dade bai samu nutsuwa ba yasha barci sosai don washe gari ma ko ofis baije ba, sunsha hira da ita kuwa ta waya cike da farin ciki da shauki.

DAGA NAN LABARIN SOYAYYARSU YA FARA.

AKASIWhere stories live. Discover now