ZAINABU ABU. 1

5K 221 6
                                    


ZAINABU ABU

YBK

"Zeena-Zeena-Zeena.......!!!" Kakar Zainab kenan, ta ke ta faman kwala ma ta kira, da sauri ta taso ganin bata ko saurarenta, ta iske su in da ta zaune wata abokiyarta kuma maƙociyarsu da su ka taso tare su na wasan bebi "Asma'u", dukanta ta ke kamar Allah ya aiko ta.

"Zeena nace ki sake ta ko?" Ta sa hannu ta ɗagota, amma bata sake ta ba, ta jawo rigarta, nan take rigar ta yage daga sama har ƙasa. Asma'u kuwa ta sa kuka.

Ita kuma Zeena ta na huci ta ce "Gobe ma ki ƙara ja na."

"Yanzu ke Zeena ba ki barin dambe ko, kullun kece an kawo ƙararki kin duki ƴaƴan mutane, kuma Ma'u da kuke wasa koda yaushe ai yaci ace kin ɗan raga mata." Kakar Zainab ta faɗa tana kallon jikar tata.

"Zainab sunana ki daina kirana Zeena, keda masu kirana zeenat nace ku daina bani so." Ta faɗa ta na kallonta ta na huci, ta kara da kwacci ta na juya idanuwa. Ta na murguda baki.

"Uhmm ikon Allah, nima za ki yi da ni kenan, yarinya sai shegen faɗa kamar dage." Kakar ta faɗa sannan ta kama Ma'u ta fara kakkaɓe mata jikinta.

"Je ki gida kinji Ma'u, kiyi wanka sannan ki dawo zan baki alawa." Ma'u ta goge kwallanta sannan ta juya ta fita.

Ta qara juyawa ta kalli jikar ta ta tace "kinyi wanka yau?"

"A'a" Ta amsa.

"To shiga maza kiyi wanka akwai kayanki da kila bari nan shekaranjiya nasa an wanke maki su, sai ki sa."

Ba gardama tayi yadda ta ce. Tana fitowa ta ga kakarta na sallah, itama taje tayi alwala tayi sallah. Bayan sun gama ta bata abinci ta ci ta ƙoshi.

Ta kalleta ta ce "Zeena" Ba ta amsa ba dan haka ta cigaba "Mi ya haɗaki da ƙawarki?"

"Kaka nace bani son wannan sunan."

"kema ki daina ce mani kaka."

"To ai ke kakata ta ce."

"E, amma ai kina ji dai kowa Hajiya ya ke kirana."

"To ai Hajiyoyin ne kunyi yawa shiyasa na ke ce maki kaka dan ba sai ance mani wace hajiyar ba, ko so kike nima ince maki tsohuwa mai ran ƙarfe?" Ta faɗa tana dariya cikin zolaya.

"Hummm kaji ja'ira, yanzu dai bar wannan zancen bani amsar tambayata."

"Kaka wai da ga na ce mata su daina jan faɗa a makaranta dan na gaji da tare masu faɗa, gashi fuskata kullun da sabon ciwo an yageni, sai kawai ta wani taso ta zaƙalƙale mani, wai ai ko ban tare masu ba suna iya ramawa da kansu, wai ai dama ni ke shiga ba dan sunce in shigarmasu ba." Zainab ta faɗa ta na murguɗa baki cikin tsiwa, kai kace Ma'un ce a gabanta.

"To yanzu wannan shine abun dambe Zeena? To kinga dai yanzu tunda ta ce haka sai ki daina shiga cikin faɗansu, kullun dama ina gaya maki ki daina faɗa, fadan da ba naki bama sai ki ara kiyi kane-kane, kuma ƙarshe ke akeba rashin gaskia, kullun sai an kawo kashedinki kina sane da haka, ki rinƙa haƙuri kinji Zainab, bani jin daɗin hakan."

"Kaka na daina shiga faɗan kowa in sha Allah, amma duk wanda ya jani zan rama."

"To naji ban hanaki ba in an jaki ki rama, amma koshi da zaki haƙura ai da yafi, ba dadi kiyi ta dukan ƴaƴan mutane."

ZAINABU ABU (COMPLETED)Where stories live. Discover now