9

3.2K 155 8
                                    

ZAINABU ABU

MALLAKA.....YBK

9

Ya ci gaba da yi masu nasiha yana rallashinta ya na dan bubbuga bayanta. Baba na son 'ya'yanshi gabadaya, amma soyayyar Zainab ta musamman ce a wajenshi.
Bayan rasuwar Mamanta, kusan suna tare da Babanta a kowane lokaci, wankanta da komai Babanta ne tun ta na 'yan watanni kadan a duniya. Shi kawai take yarda dashi a lokacin. Dan haka kowa ke ce mata Zainabun Babanta tun a waccan lokacin.
Baba ya ce "A kula sosai da addini,zamantakewa tsakanin ku da duk wanda kuka hadu dashi mutunci. Kuma ni daura aure ba tare da an tare ba sam baya cikin tsarina, amma Dadynki ya tabbatar mani ba wata matsala."
A tunanin Zainab matsalar itace aure ya lalace ba tare da tare ba, ko kuma ayi ciki a haihu ba'a tare ba. Tana tuna wannan taji gabanta ya fadi gami da jin kunyar Babanta. Haqiqa fatan da take kenan aurensu ya lalace kafin ta tare. Gashi ba zata so ta bata rana Babanta ba. 'No no no hakan ba zata taba faruwa ba in sha Allah'. Ta fada a zuciyarta.
"Ke kuma Zainab ki kare mutuncinki dana jikinki dana gidanku a duk inda kika samu kanki, ki girmama shi ki bashi haqinshi a matsayinshi na mijinki, Allah Ya yi maku albarka, in da mai wata magana bismillah ina jinku, in babu kuma ku tashi ku tafi kar ayi dare a hanya."
Salmanu cikin girmamawa ya ce "Babu wata matsala in sha Allah baba."
"To shikenan, Allah Ya tsare, Zainabu ki gaishe mani da matan birni." Haka Baba yake kiran su Husna.
Zainab ta miqe ta girgiza kanta tana murmushin yaqe. Tayi maahi sallama ta koma tayi sallama dasu Hajiyarta suka kama hanyar Katsina.
Atamface jikinta mai yau da tsada ruwan ganye da jajayen fulawoyi jikinta. Dinkin riga da siket. Ita kanta ta san dinkin ya karwbeta.
Ba su yi nisa da tafiya ba Salmanu ya kalleta ya ce "Madam ina yini tun da ni baki gaisheni."
Bata tanka ba amma ta dan ji kunya kkawaio ba komai ya girmeta, ya cancanci ta gaisheshi kamar yadda aka mata tarbiya. In kwafshi ne ta riga tayi. Dan haka kawai ta dauke kanta.
"Kinyi kyau Zeenat." Ta san neman magana ce da ta tanka.
Ta kasa daurewa ta dalla mashi harara.
Ya ce "Oh sorry, to ko ince Zainabu Abu mai tagwayen suna. Ba haka ake cewa ba. Amma gaskia masu kiranki Zeenat ma basu yi maki adalciba. Dan kinfita kyau nesa ba kusa ba. Kin san na shiga yanar gizo na ga hoton ba'indiyari da ake hada ki da ita, Allah kin fita haduwa, dan haka ni zan rinqa kiranki Zainabuna ko Zainabun babanta zan rinqa kiranki."
Sauraronshi take ta juya mashi baya cike da mamakin. Da gani yana cikin nishadi daga yanayin murmushinsa. 'Dama yana surutu haka?' Ta tambayi kanta.
"Zainab Ina son Baba wallahi, inaga bani qara kewar Babana.." Ya fada.
'Ko na baka komai a rayuwata ba zan iya sharing Babana da kai bai'. Ta fada a zuci. Jin ya bata haushi ya sa ta jawo wayarta tasa ear piece.
Bata ankara ba ya fige wayar ya tura CD, cikin wa'azin wani babban malami Kabir Gombe kuma kan aure da ma'aurata. Ta na son wa'azin malamin shiyasa bata yi mashi gardama ba. Ta jingina da wajen zamanta ta rufe idonta. ba dadewa ta ji ya tsaya da mota. Bata bude ido ba aji ya duko wajenta. Ta dan janye jikinta da sauri. Ya jawo belt ya daureta.
Ta bude baki zata ce bata so. Ya sa yatsa a bakinta ya ce "Shiiiiish......."
Ya kai hannu daga gefen kujerar da ta ke zaune ya latsa wani abu. Kujerar tayi baya sanna ta dan miqe yadda zata dan qwanta, wani abu ya fito daga qasan qafarta ya miqar da qafar ta ta.
Ya koma mazauninshi ya ce "Ki huta sosai." Ya fada yana murmushi sannan yaci gaba da tafiya.
Ta tuna ranar da zai kaini interview a Ibadan, sadda ya daure ta belt. Ta danyi murmushi.
Ba'ayi minti biyar ba ta ji kujerar na girgiza ta. Ta tashi da sauri ta na zaro idanuwa cikin tsoro ta kalleshi. sai cewa yayi
Yayi murmushi ya ce "Baqauya, koma ki qwanta massage ne ake maki dan ki ji dadin hutawa."
Ta ce "Ka kashe pls bana so."
Ya d'aga kafada ya ce "Na qi in kashe."
Yadda yayi abun kamar Muhammad na rikici. Ya bata dariya amma ta dake. Ya jawo hannunta ta fizge da sauri.
Ya ce b"Bki son in kashe ke nan." Tananan tana tunanin yadda zata yi, ta yanke shawarar gara Massage din da ta bar mashi hannunta. Ta koma ta qwanta, ba'a dade ba ya latsa wani abu daga jikin sitiyarin motar ya ce "Na kashe ranki shi dade." Har a ranta taji dadin hakan.
Ana kiran sallar la'asar suka isa gidan su Momy. Ta ji dadin ganinsu sosai, ba kamar Mohd mai sonta sosai, kullun sai da kuka suke rabuwa in sun hadu.
"Ga abinci nan kan tebur sai kuci." Momy ta fada bayan sunngama gaisawa.
"To Momy ni dai yanzu ai na zama maigida kamata yayi matata ta zuba mani ko kuwa."
"Ai in ma kace Zainab bata taba zuba maka abinci ba ba zannyarda ba."
"A matsayin mijinta dai bata taba ba Momy."
"To yaushe aka dora balantana har ta tausa, taimaka Zainabu ki zuba ma shi." Ta fada ta na murmushi
Kunyar Momy ta kama Zainabu a karon farko. Salmanu kuwa qiri qiri gaban Momy ya ce in Zainab bata yi saving dinshi abinci ba ba zai ciba.
Yaba momy kunya itama daga baya ta bar falon tana fadin "Kuji da shi."
Ganin Momy bata wurin da yace ta zuba mashi lemu, ta qi zubawa. Ta dauki plate dinta zata bi Momy, da sauri ya tare gabanta. Ta hango Momy na saukowa ta koma ta zauna a kujerar da ya jawo mata kusa da tashi. Ya kuma sagale qafarta da qafafuwanshi qarqashin table.
Ganin in ta biye mashi bacin abincin ma zasuyi ba yasa ta kyale shi maqale da qafafuwanta. Kadan kadan yayi ma ta susar qadangare. Ta qule dan bata son abun, duk da haka ta daure.
"Wallahi kaci asa Momy na kusa." Zainab ta fada a hankali.
"Ai kuwa ni da Momy sai fatan alkhairi, ba'a so na ci arzikin Momy da Dady an aureni."
"Thank GOD ka san da haka."
"Ni kuwa na san da haka, ba kin gaya mani ba ke baki so na ba ko kin manta."
"E na fada in kana so ma in qara fada maka, bani son ka."
Ya yi murmushin yaqe ya ce "Kin ce AK kike so ko?"
Hankalinta qwance ta ce "Ya AK, da ma waau da yawa yan...."
Yadda ya dago idonshi ya sa a nata ya sa ta kasa qarasa maganarta.
Ya yi dariya kadan yace "Ke za'a kai gaisuwar neman auren shi ma, kice wa zai aura in gaya maki dan na san baki sani ba."
'Ina ruwana da wadda zai aura'. Ta fada a rai.
"Your best friend."
Ta kalleshi cikin rashin gasganta zancenshi. Ya girgiza mata kai.
Ta kai abinci bakinta kenan, wanda hakan ya sa ta qware. Da sauri ya miqa mata ruwa, ta na sha yana bubbuga mata baya.
Ta shiga ture hanunshi. Lallai ma Salima ta raina mata hankali. Saudaya suka taba maganar AK da ita, kenan cikin sati biyu har sun daidaita kenan. Abincin da Nta gama ci kenan. Ta dauko waya ta buga nan inda ta ke zaune, dan ya hanata tashi.
"Me ya faru da Abubakar na ji za'ayi da ya AK." Ta tambaya kasa kasa bayan Salima ta daga wayar, ta na dauke kanta da ga Salmanu.
"Siyasa nayi ta nemanki kin kashe waya, dazu dazu muka yanke shawar zaibturo bayan mungama qaya dake. Abubakar kuwa rana daya aka daura aurenku da shi." Ta bata amsa.
Take taji Salima ta bata tausayi, shekarunsu a qalla shida tare. Shi kuma dama Ya AK tun bikin zahrah ya sa ta qyasa taqi bashi fuska saboda alqawarinta da Abubakar. Ta kasa gaya ma Zainab komai ganin itama hankalina ba aqwance yake ba. Qwalla ta ji ya fara bin fuskarta bayan ta gama bata labari. Haqiqa ta tausaya mata ganin yadda ta qi kula kowa sai shi. Kuma tabbas kowa yasan tana son Abubakar.
Salmanu ya miqa mata tissue. Ta karba ta fara goge qwallan fuskarta, ta fara ture shi jin yana shafar bayanta cikin sigar rallashi.
"In kun gama cin abincin a tashi a gaido mama, ni da naga kun dade baku zo bama na dauka can kuka tsaya, duk ta damu wai baki da lafiya." Momy ta gani tsaye kusa da su. Ta na kallonta tana magana.
Gabanta ya fadi ta miqe tsaye da sauri bayan ta qara ture hannun Salmanu daga bayanta. Ta tabbatar da Momy ta gamsu a wannan yanayi. Take taji ranta ya sosu bata ji dadi ba.
Shi kuwa Salmanu ko a jikinshi, ya dauki ruwan dake gabanshi a kofi ya shanye ya miqe ya ce "Wallahi mun dade muna hira da Baba ne, in kin shirya ki sameni a waje." Ya kalli Zainab sannan ya fice abunshi.
Ta kasa kallon idon Momy, ta tashi ta shige dakinta. Ta kimtsa ta fito ta ce "Momy za mu tafi."
"To ku gaisheta."
"Za ta ji Momy." Ta fita.
Bai ko kalli fuskarta da ta daure ba, tana shifa ya tada mota su ka tafi.
A hanya ya tsaya wani qaton shagi. Allah kadai yasan meda dame ya saya da ya shiga, ya dauko wasu kayan aka biyo shi da wasu. Ya dawo sannan suka wuce gidan mama.
"Ki dauki wa'annan ki ba mama." Ya ga bata motsa ba ya kalleta ya ce "Lafiya?" Ya lura cewa ranta ya baci.
Bata kalleshi ba ta ce "Dan Allah ni dai ka daina tabani, kaga Momy ta ga me kake mani dazu, sai ta dauka wani abu...".
Yayi murmushi ya juyo yana fuskantarta sosai ya ce "Me zata dauka, na kusanci matata, to sai me. Ko haramunne, ko ance maki kar ki yarda in kusanceki ne?"
'Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un' Abunda take ta fada kenan a ranta. Kamar ta saki fitsari a zaune. 'Me ma ya kaini yi mashi wannan maganar'. Can dai ta daure ta kalleshi tace "Da gaske na ke Allah." Ta daure fuska.
Irin kallon da yake mata tuni ta qara shan jinin jikinta. Gabana ya fadi ya shiga dukan tara tara. Musammam sadda ya daga gida daya ya hada da kanne mata ido daya ya yi murmushin mugunta da gefe daya na bakinshi. A lokaci daya ya duko daidai fuskarta ya ce "Nima da gaske nake, in kin shirya ko yau a shirye nake."
Takaici ya kamata ta bude kofa ta qwashi ledoji biyu dake gabanta ta fita. Ya debo sauran ya biyo bayanta naya dariya har suka isa cikin gidan.
Suna shiga da sallama ya rinqa qwala ma mama kira.
Ta amsa daga ciki.
"To gata dai na kawo maki Mama." Ya fada dai dai lokacin da ta fito ta taryesu a tsakar gida.
Da murnarta ta rungume Zainab tana fadin "Oyoyo Oyoyo ga amaryar auta." A lokacin Zainab ta lura babu wani mutun a duniya da take kunya irin Mama
A cikin falonta Zainab ta sulale qasa da dubara ta gaisheta a durqushe.
Ba irin wannan gaisuwar ta saba yi mata ba cikin kunya. Ta kama hannunta ta zaunar da ita a gefenta kan kujera.
Salmanu ya aje kayan hannunshi ya zauna a gefenta a hannun kuhera suka sa ta tsakiya shi da Mama.
Mama ta ce "Ya jijin naki Zainab."
"Na warware Mama."
"Ya akayi hannun amarya ba qunshi ba dai a cewa ya fita cikin sati biyu. A'a Momynki tayi laifi. Bata shirya yarta ba. Ko dai da ba yanzu za'a tare ba ai ayi lalle." Ta fada tana dariya.
Salmanu ya hada hannayensu duka cikin nashi ya riqe ya ce "Dama munyi shawara Babanta ya zama Babana, ke kuma zaki zama Mamanta dan haka sai ki shirya ta ke." Ya fada yana murmushi yana kallon Zainab da take satar kallonshi da alamun tambaya a fuskarta na "Yaushe mukayi haka da kai" Da sauri ta dauke kanta dan kallon qwayar idonshi na matukar sa ta shiga wani irin yanayi da ba ta iya fassarashi.
"Kai tashi ka bani wuri, kar kayi mana shishshigi, kasan tun sadda take diyata ne?"
Hakan ya sa Zainab ta ji dadi sosai har ta yi murmushin da haqoranta suka bayyana. Mama da duk wani nata Zainab na sonsu, Salmanu ne kawai bata da ra'ayi. Idonta dai a qasa kunya na ta dawainiya da uta gaban Mama. Yau itace a matsayin surika gareta. Ta kasa kallon idonta duk yadda cukin hirarsu suke qoqarin sakata ciki.
Abinci da sha mai aikin Mama ta jera komai a gabanta kanar yadda Mamar ta umarceta.
Ganin bata ci komai ba Salmanu ya zuba lemu a kofi ya riqo hannunta ya miqa mata. Ta karba dan kar ta jawo hankalin Mama garesu.
Ta shanye ya karbi kofin ya aje ya kuma sa mata tuffan a hannu.
Ta girgiza kanta.
Mama ta ce "Ka fa kyaleta kar ka matsa mata, ba maquwa ba ce a nan gidan."
"To Allah Ya baku haquri." Ya fada ganin Zainab ta sunne kai ta yi mashi gwalo.
Haka sukayi ta hurarsu har magrib ta qarato. Salmanu ya fita masallaci. Ita kuma suka ahiga daki ita da Mama domin gabatar da sallah. Nan barci ya qwaahe Zainab. Sai dai ta farka taga maiaikin Mama na jera mata kwanonin abini daga gefe.
Ta yi bandaki tabyi alwala ta fito ta gabatar da sallar isha da shafa'i da wuturi. Tana gamawa ta sha dan farfesun da ya cike dakin da qamshi. 'Babu ko shakka wannan girkin Mama ne'. Zainab ta fada a rai. Ta ci ta qishi abunta.
Ta fito daga dakin cikin shirinta tsaf ta ji Mama na waya da Momy ta ce "Uwar biyu ya akayi amarya ba qunshi ko a hannu."
Momy ta ce "Saboda ba ta da lafiya ne a lokacin Mama amma na ahirya komai, sai nace bari a tari gaba."
Mama ta ce "To in bakuyi da gaske ba kuwa zan amshe maku wannan 'yar taku."
Ba komai Mama mun bar maki ita." Momy ta bata amsa.
"To ga auta nan na turo shi ki hado mata yan kayayyakin da zata buqata qwana biyu, na kira wasu masu gyaran jiki da lalle daga Kano gibe da sassafe zasu baro, in sun isi da wuri kila a fara yi mata gyaran jikin gobe. Ban san ko qwana nawa suke ba dai."
"To shikenan Mama sai yazo."
Hakan ya tabbatar mata da nan gidan zata kwana aqalla daya. Dan haka ta samu waje ta zauna.
Dan duk ta na jinsu maganar da suke da yake speaker ta sanya a wayar. Tuni dangantakar Momy da Mama ke birge Zainab kamar ba surukai ba.
Bayan sun gama Mama ta ce "Sai ki shirya zaman guaran jiki gobe. A qalla dai kiyi ma mijinki kwalliya kafin ya tafi ko."
Zainab ta yi murmushi ba tare da ta iya cewa komai ba.
"Kema ai kin kusa ki koma makarantar ko?" Mama ta tambayeta ganin tafi son hirar makaranta duk cikin hirar da za'ayi mata.
"E, yakama ace wannan satin na koma, amma Momy ta ce in bari sai ya tafi sannan in koma." Ta fada tana wasa da yatsun hannuta.

ZAINABU ABU (COMPLETED)Donde viven las historias. Descúbrelo ahora