16

3.6K 148 7
                                    

ZAINABU ABU

MALLAKA.....YBK



16

Ko kallonta Salmanu bayyi ba. Abunda ya qara bata ran Zainab. Ta aza kai a guiwa takaici ya cika ta, ta rasa me ma zata yi ta ji dadi. Sam ba zata iya zama da wannan matar ba. Kuka ta yi mai isarta tana tunanin maganganun da Ranee ta fada mata.
'Ina za su kuma' Ta kasa amsa ma kanta tambayar, daga qarshe ta sulale nan ta qwanta qasa tayi barci, da yake zafi ake sanyin wurin bai dame ta ba.

A kan gadon dakinta ta farka, yunwa ce ma ta tada ta, ta safka qasa da gudu, ta samu juice da madara ta sha, sanna ta danji dai dai. Da ta dan natsu ta qara hada cornflakes ta qara sha.

Salmanu ya shigo ya tsaya dai dai gabanta ya ce "Ke baki daddara da halin da kika shiga ba shekaru biyu da suka wuce ba ko, me ya sa zaki yi barci a kan tiles, kin manta pneumonia din da kika yi ne, kar ki qara zama haka ba kaya jikinki komin zafin da ake."

Bata tanka shi ba ta ja tsaki ta dauke kanta.

Ya kara waya a kunne bayan da ta yi yar qara kadan Ya ce "To safe journey." Bai qara cewa komai ba ya kashe wayar ya tura aljihu.

Daidai lolacin da ta gama shan cornflakes dinta ta tashi zata wanke cup din, ya karba ya aje.
"In na yi maki magana ina buqatar amsa." Ya fada ya na qoqarin hadiya bacin ran shi. Dan ko kallonshi bata yi ba balantana ta amsa, ya ja hannunta dole ta bi shi, dai dai stiars ta tirje, ya juyo ya sabeta da hannu daya ya dire ta a bandaki.
Ya kalli agogon hannunshi ya ce "Ki na da minti goma sha biyar ki shirya ki same ni fita zamuyi."

Ta linke hannuwa a qirji ta tamke fuska ta na kallonshi.
Ya fara nade hannun riga ya ce "I can help you if you want."

Ganin da gaske ya fara tara ruwa a bokiti, ya jawo ta zai tura cikin qwamin wanka ya sa ta bige hannunshi ta ce "Ka fita zanyi." Ko ba komai ta ji dadin jikinta in tayi, kuma an fara kiraye kirayen sallar azahar.

Tana gama sallah ya shiga dakinta ya ce "Minti sha biyar na baki kinyi talatin, oya mu je." Ya fada ya na riqe da makullin mota.
"Ba inda zani da kai malam." Ta fada ba tare da ta dubi inda ya ke ba. Ta ninke abun sallarta.
"Mama fa zamu gaido, haba zainabuna, mu je kin ji lokaci na wucewa." Ya fada ya na murmushin da bai kai ciki ba. Dan ya san in ya tafi kuma ya barta Mama ba zata ji dadi ba, da tuni ya yi nisa a hanya.

'Ba dan halinka ba' Ta fada a ranta. Ta dauki gyalenta irin kalar atamfar jikinta, puple colour dinkin riga da skirt. Sun yi mata kyau sosai. Ta bi bayan shi.

Suna shiga gidan, Mama da maryam na dawowa daga islamiya. Suka anshesu da murna, kamar ba jiya da daddare suka bar gidan ba.

Nan suka ci jallof rice tasha busashshen kifi da salad, sukayi nat. Ba kamar Zainab da ciki ba komai. Sau biyu ta na qari.

Qarfe biyu daidai Salmanu ya kalli agogonshi ya miqe ya kalli Zainab ya ce "Ta shi mu je."
Yadda ta ke kallonshi kamar ta mance tare su ka zo kuma tafiya za su yi tare, ta baje daga gefe ta saki jiki suna ta hira da Mama da Maryam kamar yadda su ka saba. Ta kasa cewa komai.

"Tun yanzu?" Mama ta tambaya.
"Kaduna zamu Mama kuma sai mun shiga Dutsinma mun gaida su Hajiya ba ni so mu yi dare." Ya bata amsa.
"E to gara ki tashi ku lallaba Zainab." Mama ta fada.

ZAINABU ABU (COMPLETED)Donde viven las historias. Descúbrelo ahora