11

3.1K 149 12
                                    

ZAINABU ABU

MALLAKA.....YBK


11

'Ko dai son ganinshi ki ke Zainab' wata zuciya ta tambayeta a qwaqqalwarta. Ta yi murmushi ita kadai, ta juya kan gadonta, ta ga Salima tsaye a bakin qofa ta ware idanuwa ta na kallonta.

Ta tashi zaune da sauri ta na mamakin ganinta dan bata san tun sadda ta ke wajen ba.
"Uhmmmmm, some body is in love." Ta fada.
Tsaki kawai ta ja ta basar da ita.

Ana saura qwana biyu Zainab ta gama jarabawa Momy ta buga ma ta waya cewa in ta gama jarabawa ta sameta Abuja gidan Yaya Qassim. Itama washegari zata iso dan matarshi ta haihu nan da qwana biyu suna.

Sam bata kawo komai a ranta ba.
Ranar tafiyarta, Salima ta yo mata rakiya, har ta shiga mota ta ce "Oke Zee dama ciki gareki ko ki gaya mani, to naji, yanzu inaganin anyi mani juyin mulki daga kujerata ta besty."

Zainab ta zaro idanuwa ta ce "Inji ubanwa, in ciki gareni ai ke zaki fara sani." Take gabanta ya fadi, a ranta ta ce 'Anty Lubabatu ta yi tsiyar.

"Oho dai na ji, Allah Ya kiyaye hanya, take care of our baby." Ta rufe mata qofa. Direban na jin an rufe qofa ya tada mota, Maigadi ya wangame qofa ya fice. Har motar ta fita tana bi Salima da harara. Ita kuwa tana murmushi ta na daga ma ta hannu.

Gidan yaya Qasim cike ya ke da yan'uwa da abokan ar'ziki lokacin da zainab ta isa. Da yawa tun aurenta ba ta qara ganinsu ba, kowa yaji dadin ganinta sosai. Abun mamaki kowa ya ganta sai ya ce ta yi kyau ta yi fari. Wasu kuma su ce har da kiba ma tayi.

Sai a lokacin ita kanta ta lura da hakan.
Qata mata daga gefe ta ce "Ai aure rahama ne."
"Zainab kuwa ta san abincin talatu ne maidadi da ta ke qwasa, safe da rana da dare, Salmanu bai dauketa aiki ba sai da ya tabbatar da ta je makarantar girje girke, kafin ma ta fara aiki a gidan Anty Lubabatu sai da tayi a Hotel.

Ba su sami damar kebewa ba da Momy sai can da daddare, wuri duk ya fara tsit, wasu ma duk sun yi barci. Momy ta kirata a waya cewa ta same ta a dakin da aka safketa.

Da fara'arta ta shiga dakin, sai dai da ganin fuskar Momy Zainab ta sha jinin jikinta. Tabbas ta san aqwai wani wata a qasa.

"Gani Momy, me ya faru Momy, Allah Ya sa bani na 'bata ma ki rai ba." Ta zauna kan gadon da take zaune gab da ita ta na dubanta, gabanta na faduwa.

Bayan yan daqiqai ta dubeta ta ce "Yanzu ke Zainab ki na da ciki shine ki ka yarda ki ka biye ma Salmanu aka daga bikinku, ba abun kunya bane tun da da aurenku, amma kin san Baba abunda ya tsana kenan a haihu ba'a tare ba. Kuma Dady a tabbatar mashi hakan ba zai faruba. Dan me za ki amince da a daga biki?"
Tunda ta fara magana Zainab ta zaro idanuwa, baki bude ta na saurarenta amma ta kasa cewa qala.
'Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un' Ta fadi haka a ranta ya fi a qirga. Shikenan na shiga uku na ja ma kaina Dr Peter ya cuce ni walh'.
Momy ta ci gaba da cewa "Sati biyu da ya wuce mu na Kaduna bikin yar abokin Dady, da Katsina za mu zuce, amma samun labarin cikinki dole mu ka fasa."

Ta aje wata ambulan gaban Zainab ta ce "Dady ya nema maki visa, duk abunda zaki buqata na tafiyarki na ciki, gobe zaki tafi, gara aji kin bi mijinki da ki haihu baki tare dakinki ba, dama biki ai duk al'adace, ba ni so aji wannan zancen gida ki tafi kawai in ma anji na san yadda na rufe zancen."

ZAINABU ABU (COMPLETED)Onde histórias criam vida. Descubra agora