12

3.4K 164 12
                                    


ZAINABU ABU

MALLAKA.....YBK


12

Dakin ya yi tsit, ajiyar zuciya Salmanu kadai ake ji.
Ganin baya da niyar cewa komai ya sa Zainab ta ce "Da fatan ka zo mani da takaddar sallamata."

Gabanshi ya fadi a lokacin ya tuna saqon da ya bari a bata. Daga nan durqushen ya kamata ya riqe tam, kamar tace zata gudu. "Zainab na san babu wata kalma da zan iya baki haquri da ita, amma dan Allah ki yafe mani."

Ta ture shi, murya can qasa kamar mai shirin yin kuka ta ce "Na yafe maka, amma ka sani bani qara zaman aure da kai, dan haka ka bani takaddata kamar yadda kace a shirye kake ka sallameni."

Ya qara matsawa kusa da ita har sai da yaji ta a jikinshi, ji yake da zai iya cire mata duk wata damuwa ko wani zafi da take ji a ranta, haqiqa ya san shi din mailaifine a wajen abun qaunarsa. Wanda na baya bayannan duk ya shafe na yarintarsu. Ya ce "Na gode Zainab, amma cewa nayi zan sallameki ba cewa nayi zan baki takaddaba, zan iya baki, in ita zata faranta maki rai, amma musulunci baya son saki musammam a irin halin da kike ciki, sadda kika haihu sannan kike gama idda ko da mun rabu yanzu, dan haka ki bari har ki haihu sannan, in har a lokacin kin ji kina da bukatar hakan." A ranar ya samu labarin halin da Zainab ke ciki, ya shigo jirgin da zai baro Japan zuwa Korea ba tare da qara bata lokaci ba. Dole ne ya fuskanci duk wani hukunci da zata yanke a kanshi.

Jin haka yasa da sauri ta tureshi daga jikinta, ta tashi zaune duk da ba wani qarfi ke gareta ba har yanzu, ta zaro idanu tana kallonshi a ido ta dafe cikin da hannayenta ta ce "Kar ma ka qara wannan tunanin, abunda ke cikina 'danane, zan iya riqeshi ba tare da taimakon kowa ba, kar ka manta da abuna na zo, kuma da takarduna sun hadu zan tafi gida kamar yadda ka ce."

Ya miqe ya juya mata baya sannan ya taka har zuwa tagar dakin ya tsaya. Hannayenshi cikin aljihun wandonshi. Ya lumshe idanuwanshi yana qoqarin fahimtar irin halin da Zainab ke ciki. Ya sake juyowa ya dawo inda take ya ce "Zainab kiyi haquri, ki bar wannan maganar "please", kar ki manta kince kin yafe mani, a cikakkiyar budurwa na sameki, kuma cikinki yau qwananshi ashirin da tara daidai a lissafin da akayi na asibiti, dan haka d'ana ne babu tantama ba shakka a ciki, zan yi maki duk abunda kike so, da zarar kin qara samun lafiya kuma takaddun ki sun kammala zaki tafi gida, innhaka kike so"

"Good." Ta fada, tasa bayan hannunta ta share qwallan da ke gangarowa daga idanuwanta ta koma ta qwanta. Shi kuma ya bar gidan gabadaya.

Ba dadewa ya dawo da kaya niqi niqi, manya manyan ledoji cike da tarkacen kayan ciye ciye, kala kala yayi ta jerawa gabanta. Bata ko kalleshiba duk da uwar yunwar da ta riga ta samu gurin zama a cikinta.

Sai da ya gama ya fita, sannan ta tashi zaune daga kan gado ta jawo dan abunda take ganin zata iya ci. Duk ciki wani biredi ne kawai ya fi birgeta, ta dauka ta fara ci. Kafin ta gama ya kawo madara da juice da ruwa, kowane ya zuba a kofi y ajiye mata a tebur din kusa da gado (bed side stool).

Bakin qofar dakin ya koma ya zauna kan kujera dan ya lura zaman shi kusa da ita na takura ta. Da Laptop dinsa a hannun ya na yan latse latsenshi na iska dan hankalinshi na kanta, duk motsin da tayi kan idonshi. Har barci ya qara qwasheta. Ko da ta farka ya qwashe kayan da ya jera, ya kuma jera wasu, kuma yana nan dai bakin qofar.

Ta na qoqarin tashi, wannan karon kallon da ta yi mashi bai sa ya fasa zuwa inda take ba, ya qaraso gabanta, ya yi murmushi ya ce "Ki bari in taimaka maki."

ZAINABU ABU (COMPLETED)Tempat cerita menjadi hidup. Temukan sekarang