10

3.3K 139 8
                                    


ZAINABU ABU

MALLAKA.....YBK

10

Ta yi dariya ta ce "Kefa dadina dake ruwa ruwa ce Zainabun Babanta, yanzu mijinki zakiyi ma shagwaba ba Momy da Dady ba."
Ta qara kankameta ta na girgiza kai ta ce "Momy ku zanyi mawa Allah."
Tana d'an dukan bayanta tayi dariya ta ce "To shikenan ya wuce, tashi ku tafi." Ta tashi ta kamo hannunta suka sauko qasa, ta qara share mata fuska da hijabinta. Ta yi murmushin da yasa Zainab ta ji sanyi a ranta, Momy ta 'dan tura alamun ta wuce. Ta daga mata hannu.
Zainab ma tayi murmushi qwatanqacin ta Momy ta 'daga mata hannu ta fita. Duk Salmanu ne ya ja mata ba kowa ba, dan haka cike ta ke dashi.
Ta bud'e motar ta shiga, ta zauna ko dubanshi bata yi ba, ya tada motar suka tafi.
Gidan Mama ya nufa su ka fara yi mata sallama, ta cikata da kyauta kala kala sannan suka d'au hanya. Tana jin dad'i ganin bai tanka mata ba shima.
Can sai ji tayi ya damqo hannunta ya riqe cikin nashi. Ganin ta kasa amshe hannun yasa ta haqura.
"Na yi laifi ne Zainabuna, na san Salmanu sarkin laifi ne, ko tun wancan laifinne da na yi, na ce ki yi haquri ki yafe mani Zainabun babanta." Ya kai hannun bakinshi ya na wasa dashi.
Bata ce komai ba sai dai tayi nasarar amshe hannunta a wannan lokaci cikin sauri. Ba'a dade ba ya qara riqo hannun ya sarqa y'anyatsunta cikin nashi yana wasa da nata yatsun. Sam bata son irin yanayin da ta tsinci kanta a ciki, gaba'daya tsikar jikinta ke tashi sai dai ta san 'bata lokacinta kawai zata yi dan bata iya qwatar kanta. Hakan ya sa ta haqura.

"Qunshinki ya qara kyau, no dukkanki ma kin qara kyau Zainabuna, dole a rinqa yi maki irin wannan qunshin akai-akai." Ya qara kai hannun bakinshi ya d'ora labbanshi ka'dan. Ya yi murmushi mai bayyana farincikin da yake ciki.

'Humm....kaji qarya' Ta yi zancen a zuci.
Tabbas Mai ka'dai ta shafa bayan tayi wanka, tasa doguwar rigar wani yadi mai ruwan madara da adon filawoyi

'Wai nayi kyau....uhumm, neman magana dai kawai kake, kuma ka yi ka gama' taci gaba da zancen zuci.
Kad'an kad'an ta ja hannunta ko ta samu sa'ar anshe hannun amma ta kasa.

"A haka ma wannan hanya ce mai sauqi ta samun lada, ko baki so mu samu Zainabuna, balantana ma ace kin qara ma tafiyar tamu armashi ta hanyar yi mani hira." Ya fad'a yana d'an dubanta ya na murmushi.

"Bana so, kuma ba zanyi hirar ba. Kuma ka sakar mani hannu." Ta kalleshi ta fad'a ranta a b'ace.

"Ina so ki manta da komai da ya faru a tsakaninmu a baya Zainab, mu shimfid'a wata sabuwar rayuwa mu d'ora a kan rayuwarmu ta baya wadda zamu iya tunawa mu ji da'di a ranmu. Mu musulmai ne, dole mu yarda da qaddara mai kyau ko kuma akasin hakan. Hakan zai qara dawwamar damu a cikin imaninmu. A matsayin matata kike yanzu, kuma duk wani nauyi da ya rataya a kaina a matsayin mijinki zan yi tsayin daka domin ganin na sauke wannan nauyin, ban aureki dan in quntata maki ba. Ki bani wannan damar kin ji Zainabuna."

A karon farko ta kalleshi, daidai lokacin da ya juyo shima ya kalli qwayar idanuwanta da qwallan ciki suka sa su yin kyalli. Hawayenta suka dira a hannayensu da ya saqale kan qafarta. Ta yi saurin kauda kanta ta na tunanin inama abunda ya fada gaskiya ne. Haqiqa da tayi qoqarin zama dashi a matsayin mijinta. Sai dai sam kalamanshi basu samu mazauni a zuciyarta ba, dan haka har yanzu bata ji ta shirya yin hakan ba. Shi me zayyi da ita, wadda ya kira 'yar'iska. Fatanta kafin ya dawo daga tafiyar da zayyi komai ya lalace.

Lokaci mai tsawo ta na satar kallon hannayensu da har a lokacin ya ke wasa dashi. Ta tuna ranar da suka tafi Ibadan a karon farko, haka tayi ta kallon hannunshi a mota. Ba komai ya birgeta ba tun a lokacin sai irin yadda gashin hannunshi ya yi luf luf qwance ta ko'ina a hannun nashi. A lokacin ta rinqa tunanin da zai yarda da ta d'an sa almakashi ta rage shi da ya fi yi mashi kyau. Hakan yasa ta yin d'an murmushi ta yi saurin 'dauke kanta dan kar ya lura.

ZAINABU ABU (COMPLETED)Dove le storie prendono vita. Scoprilo ora