ZAINABU ABU 2

3.7K 184 5
                                    

ZAINABU ABU......BITA TA BIYU.....2

MALLAKA.......YBK.

Suka ci abinci a kwano ɗaya da Babanta. Bayan nan barci mai nauyi ya kwashe ta a shinfiɗar Baba, ba ta ƙara sanin me ake ba, sai farkawa tayi da asuba a gadonta.

BABAN su Zainab, Alhaji Mammam Mai jama'a asalinsu mutanen Sokoto ne, safarar kasuwanci ya kai Kakanshi jihar Katsina karamar hukumar Dutsinma, anan aka haifi kakansu, har Babansu, suka zama yan gari harda sarauta.

Mahaifiyar babansu wadda zainab ke kira da kaka bafillatanace ta asali, don haka duk yayanta farare ne sol kyawawa, ga gashi laya laya maza da matansu.

Sauran yan'uwan babansu Zainab duk sunyi karatu mai tsawo, amma shi sai yafi bada himma ga harkar noma da kasuwanci. Kasuwancin shi bai tsaya cikin gida ba kawai, aa, harda yan kasashen dake makotaka da kasarmu ta gado Nigeria. Wata kila dan shine na fari kuma yanason taimaka wa babanshi da kakanshi a harkarsu ta noma da kasuwanci, dan duk harkar da suke kenan. Har daga baya yayi karfu sosai a cikin harkar, domin ya gaje ta tun asali.

Allah Ya taimakeshi, duk abunda yasa gaba to da ikon Allah sai ya bunkasa.
Ya samu cigaba na ban mamaki cikin yan shekaru kadan, ta hanyar noma, kiwo da kasuwanci.
Haka kuma Allah Ya yi mashi jama'a masu kaunar shi, saboda mutunne Mai son jama'a, sakin fuska da son wasa da dariya ga kowa. Duk wanda zai kawo kukanshi wajen shi, to da yaddar Allah zai share mashi hawaye ya dara.

Wannan yasa mutane suka yi mashi lakani da Alhaji Mai jama'a, daga duk in da kake, kaje garin Dutsinmar jihar Katsina kace kana neman Mai jama'a to bazaka bata ba, Za'a kaika har gidanshi.
Danginshi duka ya rike, yayansu da jikoki, ya hada kan kowa.

Ganin jama'ar da Allah ya bashi, yan siyasa kowa so yake yayi hurda dashi, dan haka ya zamo dan siyasa da karfi da yaji. Kuma duk wanda ya tsaya mawa, to da ikon Allah zai samu nasara, dan jama'a zasu goya mashi baya, sanin cewa Mai jama'a ba zai kawo masu jabu ba.

Ba a cewa hamshakin mai kudine, amma shine komai a dangi da makota da abokan arziki, daga kudin tara, har jamia.
Kayan auren dangi shine, Macca duk danginshi da wanda Allah Ya cida daga makota da abokan arziki sunje sun sauke farilla.

Duk wanda Ya Bude baki tsakaninshi da Maijama'a sai addu'a da neman shiriyar Allah ga iyalinshi.
Mahaifiyarsa, watau Kaka kenan takance "Mai jama'a a riqa tanadi dan kanada zuria'a da yawa."
Ansarshi a koda yaushe itace "Kuyi ta yi mana addu'a, dan dai abinda nake ma mutane bazai sa na rasa ba, haka zuri'ata, kullun fatana, Allah Ya rufa ma kowa asiri har ya taimaki wasu."
Haka dai rayuwarshi take, in baya wajen hidimarshi to yana gida cikin zuri'arshi, ayi ta hira ana wasa da dariya, hakan na birge duk wani da ke hurda da yan gidan. Ba ruwanshi dattijon, baban Zainab kenan.
Matanshi hudu, Hajiya Babba, Hajiya Mairo, Hajiya Ma'u, sai Hajiya Amarya wadda Ya auro bayan rasuwar mamar Zainabu, wadda Zainabu ke kira da Hajiyarta dan ita ya damqa ma amanar Zainab bayan zuwanta.

Yayan gidan, cikin talatin kadan ke babu, na karshe-karshen sune su Zainab, yara uku ko hudu zuwa biyar ake taso wa kai daya cikin gidan. Ko da yaushe gidan cike yake da mutane.
Tukanen dafa abinci na gidan kansu abun kallone, kamar na makarantar kwana (boarding house) dan girma.
Cikin ikon Allah hudubar da Baban nasu ke yawan yi masu a koda yaushe tayi tasiri a kansu, dan dukkansu 'yan gadannan kan su a hade yake, suna son junansu, da wuya ka tantance yan daki daya. Kuma duk da babansu suke kama, duk da dai duk iyayensu mata kyawawa ne shima Ya hadu guy din dan kuwa ba daga baya ba wajen kyau.

ZAINABU ABU (COMPLETED)Où les histoires vivent. Découvrez maintenant