page 1

10.4K 455 5
                                    

      *💅BAKIN RIJIYA....ba wurin wasan makaho bane*💅

   Love story 2018

Billy galadanchi

  Sadaukarwa gareki qawar alkhairi ummie Aisha.

      *Wannan shafin nakine 'Yar uwata Hafsat Elham, Allah yabar mana zumuncinmu, Yakuma albarkaci rayuwarki Ameen*

                         01
Hafsat!!  Malamin nasu ya daka mata tsawa,d'aukacin yaran class d'in sun tsorata da wannan tsawar amma Hafsat ko'a jikinta a zahiri ma ko d'ago kanta batayi ta Kalli malamin ba, zuwa yayi cikin azama ya daki teburin da take Kai yace cikin fusata "How dare you! Are u stupid? " a hankali ta miqe daga zaman datake sannan cikin ko inkula tace "No sir I'm not" cikin qaraji yace "what!!  Repeat what u just said now" cikeda kwanciyar hankali ba alamun tsoro tattare da ita tace " I just say I'm not sir" murmushin mugunta yayi dama yana jiranta a cike yake da ita fam

"Hafsat look into my eyes and repeat after me OK? "batayi magana ba ya kuma cewa

"oya say that you,you are stupid " wani shu'umin murmushi tayi sannan tace "You! You are stupid!!!! " zaro idonshi yayi sabida ba haka yake tsammanin zatace ba yace

" How dare you, are u in ur senses? " ita d'inma cikeda raini tace tana Zare ido  Kamar yanda yayi tace  " How dare you? Are you in ur senses?? " cikin azama ya sanya qaton hannunshi irinna yarbawa ya zabga mata lafiyayyan Mari seda taga jiri dafe wurin tayi ta saka kuka aikam malamin se wani cicika yakeyi irin ya hasala, hanyar fita waje tayi Kai tsaye office na principal nasu ta nufa Tanata uban kuka irinna shagwab'abb'un yarannan marasa ta ido, PC na ganinta ya miqe tsaye ya sani idan ba'ayi sa'a ba lokacin korar wani malamin ne yazo

"Hafsat lapiya me kikewa kuka haka?  Meya  sameki?" tana kukan ta kwashe qarya da gaskiya ta sanar masa, a haka aka tarar wa malamin sanda ya bata haquri sannan tace ta yadda bazata fad'awa daddyn tab'a, domin kuwa mahaifin nata shine mamallakin makarantar kuma itadin yar gatace gaba da baya ba Wanda ya isa ya taba Hafsat Poojah ya zauna lapiya mahaifinta be had'a kowa da itaba kasancewar ita k'adaice 'ya d'aya  tilo da Allah ya bashi se kuwa yayan ta shammaz......

   
Class dinsu ta koma,dashigarta mazan class d'in suka dauki ihu,pooja!pooja!pooja!....wani Yaro dan masu ji da naira nalura yana dai daga cikin taqadarun students d'in makarantar yace,
   Poojah babe ina fatan kinsa an lallasa wannan malamin?,
Abokinsa Wanda duk halinsu d'aya yace, Ni bama Sonai takaishi Kara ba,
  Sonayi itama ta kifa masa Mari ya za'ayi tana yar me makaranta ya Mareta?,

Haushi taji yadda yanuna rashin gamsuwarsa da abinda tayi, wato ma bata burgeshi ba harara ta kwadamai kafin tace,

Banga damar ramawa bane,kaima kasan inkifa masa Marin yana dai daga cikin kananun ayyukana kamar yadda Kaima baka wuce in zabga MA Marin ba mtswww,

Baki asake yake kallonta se Abokinsa wizkid Yasoma ihun kiran sunanta,poojah!poojah!kina burgeni wallahi,

Cikin halinta na basarwa tace,
   Dalla kuyi mana shiru ninagaji da wannan banzan hayaniyar naku,

Sum sum mata da mazan dake a tsaye  suka Nemi mazaunin su batareda sunyi magana ba, 

Wannan shine kadai aikin hafsat a makaranta taga damar submitting  plane sheet lokacin exam kuma duk teacher Dinda yai failing  dinta ze rasaa aikinsa ne bakuma Dan wai batasan mezata rubutaba sedan kawai ta nuna isa da tantagaryar shagwab ganin makarantar  ta mahaifinta ne kuma baya ganin laifin ta aduk shirmen dazatayi, 

1:50pm aka Tashe su tun daga sama ta leqo bata hango motar driver dinta ba, tafiya take bata kallon gabanta hartagama saukowa daga stairs d'in be k'araso ba,tafiya take Tana tunanin hukuncin dazatayi wa Ayuba yau,tana isa gate segashi yazo dasauri yazo ya Karbijakarta ya sa bayan motar itama yabude mata tashiga Se cin magani take, 

BAKIN RIJIYA...ba Wurin Wasan Makaho BaneWhere stories live. Discover now