*💅BAKIN RIJIYA....ba wurin wasan makaho bane*💅
Love story 2018
Billy galadanchi
*HASKE WRITER'S ASSO.*(home of expert and perfect writers.)
Wattpadd@ 68billygaladanchi*Sadaukarwa gareki qawar alkhairi ummie Aisha*
24
Tunda hafsat ta koma gida take nazarin abubuwan da suka shiga tsakaninta da J.A sam bata ankare da wautar data aikata ba se yanzu,idan ya kasance shi yayi wining na case din fa? Ko kuma ya kasance ba shi bane yayi kisan fa?" wani tsoro ne ya shigeta lokaci d'aya qirjinta ya soma wani irin dokawa,dafe kanta tayi ta shiga rero adu'o i kala kala na tsari.....Brr. J.A kuwa bayan fitar hafsat a fusace shima ya fita,be tsaya ko ina ba se asibitin uduth kai tsaye wurin masu bada katin shiga wurin ya nufa bayan sun gaisa ya nuna musu ID card d'insa sannan yace
"Nazo bincike ne akan wani case na murder da aka samu anan asibitin kwanakin baya,ina matukar buqatar had'in kanku domin tallafawa family d'in wannan babban rashin ba bisa haqqi ba,nima kuma da ake zargi ku taimakamun matsayin na na baban lauya me matsayi ace ana zargina da kisan kai" sosai suka fahimce shi dama mutane da dama sun dad'e da qaryata zancen zargin da ake masa kasancewar mutane da dama sunsan halinsa na nagarta, babban cikinsu yace "Wane taimakao kakeso mu maka yallab'ai?" gyaran zaman madubinsa yayi sannan yace
"Record nakeso na dukkanin motocin dasuka shigo asibitin nan aranar 11/11/2016 tunda shabiyun daren shigar ranar har zuwa shabiyun daren wucewar ranar,na kuma san kunada cctv camera anan so idan ba damuwa ina buqatar video d'in" gyaran zama ogan nasu yayi sannan yace dashi
"Dama plate number ne muke d'auka mubaka card na shiga,se kuma sunan motar da color dinta da model number na motar,cctv kuwa yana daukar shiga da fice na kowa a asibitin nan,sabida haka yallab'ai komai daya dace zamu baka inshaa Allah" godiya ya masa sannan yashiga tattare muhimman informations da aka lokaci daya ya harbo bakin zaren.........
Shammaz kuwa tunda abun yafaru yakejin wani tausayin hafsat,a qasan zuciyarsa kuwa yanajin wani iri tamkar laifin sane komai,zuwa yayi ya samu haj Innah ya sanar mata yafasa auren hafsat baya santa kuma ta janye qudirinta,dama ita tunda taji cewar sabida auren sa da aka ambata hafsat ta gigice harta samu hatsari ta kudurta aranta bazata qara wannan furucinba kuma idan ma hafsat taji sauqi zatace abata zab'inta,shi kenan kuwa ta amince wa shaam akan ya gayawa iyayensu......
*Court*
Hafsat ce a zaune tare da lauyan me kare J.A se wasu lauyoyin guda biyu,acikin babban court dake jihar sokoto,Justice d'inne ya rero bayanin zargin da akewa Brr. J.A tare da baiwa masu qara damar bayyana hujjojinsu daya sanya suke zarkin sa da kashe likitan,batare da bata lokaci ba hafsat ta zayyane komai daya faru agabanta ta qara da cewar
"Furucin sa kad'ai ya isa ya nuna mana cewar shine yayi kisannan" dayan lauya din me kare wanda ake qara ne ya miqe yace
"Objection my load" kallon sa justice din yayi shikuwa yaci gaba
"my load be kamata lauyan wanda suke qara ya riqa alaqanta laifin kisan kai kacokam ga wanda ake zargi ba,tunda ai zargin sa ake bawai an tabbatar ba" justice ya kalli hafsat yace "A kiyaye" ya sake kallon Brr. Khaleed yace
" yallab'ai zamu so akara mana lokaci kadan domin gabatar da shedunmu kuma zasu so a gayyato mana babban Abokin marigayin anan wato Dr. Shuraim" dama aka basu daganan aka d'age zaman sena da sati d'aya.
*Bayan sati d'aya*
Lauyan wanda ake qara ne yace fara magana kamar haka
"My load wannan gabaki d'aya record ne na motocin dasuka shiga asibitin ranar da abun ya faru,acikin mun samu mota iri daya kirar honda civic kalar ja wacce aranar tashiga asibitin kusan 7 times a wannan ranar cctv camera ta main gate data ward din da akayi kisan duk sun tabbatar mana da shigar mamalakin motar so bakwai a wunin ranar, kuma duk shigar sa kai tsaye ward d'in yake nufa wato inda sin din ya faru kuma mayannin dayayi duka ba face mask a fuskarsa se ziyartarsa ta karshe inda har yayi nasarar hallakar da sayyeed,sannan kuma a binciken da muka gabatar,makashin yaje kashe hafsat ne ita kadai bawai da sayyeed,sabida sayyeed ba asibiti bane gidansa,kuma idan ma kasheshi zeyi sedai yaje gidansa ya kashesa acan,abinda muka sani shine sayyeed taimako yaje a yanda muka gani a camera shine harya fito ya ganshi ya shiga seya bisa a baya,abinda camera ta kasa nuna mana shine menene ya soma faruwa acikin dakin kasancewar babu wadatuwar haske ya sanya se bayan yayi kisan ya juya ze fita haske ya wadata kuma har fuskarsa mun gani,abunda masu qara sukace wanda yaje kisan hafsat itace wacce yafara dosawa pillow a fuska kafin sayyeed ya cece ta,idan ko har hakane furucin da muhammad yayi sam bashida alaqa da wannan kisan na sayyeed" shiru yayi hafsat gaba daya kanta ya daure sabida batayi wannan tunanin ba shi kuwa yaci gaba
"Munyi nasarar cafke wanda yayi kisan,kuma munaso yazo nan da bakin sa yayi bayanin wanda ya sakashi kisan idan har kotu ta bamu damar yin hakan" izini. Aka basu akan su gabatar da mutumin......koda alqali ya tambayi mutumin seya fara bayani kamar haka
"Da farko dai sunana kamilu,kuma ni dan area boy ne ina zamane a unguwar iraqi dake cikin garin sokoto,ina zama wani likita me suna shuraim yazo ya sameni akan yanaso in masa aiki akan wata mara lapiya me suna hafsat,ni kuwa dama ba ruwana aiki ko wane irine indai na kudine to kuwa zan yishi yabani details na komai da komai na dakin datake da time da babu yawaitar mutane awurin yakuma ce na danneta da pillow sabida gudun zargi ganin zan samu kudi ya sanya na amsa tayinsa naje nagama monitoring na wurin da komai,nashirya rana daya naje,shine qaddara ya fadowa wanda yazo tare fadan na kasheshi da wuqa ta,shine wayannan suka bi ta hanyar kotar danake hawa suka kamoni" jinjina kai kowa keyi yayinda hafsat ta rikice tabbas wannan shine mutumin data gani kuwa,dama sun buqaci ganin shuraim shi kuwa be karaji daga wurin wannan mutuminba so bezata hakan zata faru ba,koda aka buqaci yazo beyi gaddama yazo a rude ,tambayar sa akayi dalilin san kashe hafsat baiwar Allah yafara magana kamar haka
"Na kasance ina matukar san yarinyar tun tana secondry schoool amma ta wulakantani,har kuka nake mata amma bata damu dani ba,ganin nayi nayi taqi kulani yasanya nashiga malamai na sanya duk wani namiji idan ya kalleta zeji yana matukar tsanarta idan kuwa me riqon addinine yafara santa semu saka masa mafarkai na tsoro akan zamu kashe duka su biyun harse yagaji ya kyaleta,kwatsam mukazo asirinmu damuke mata ya dena tasiri bincike ya nuna mata an mata magani kuma turarukan datake using ba wani aljanin daze iya rab'ar inda take ma, da wannan naji zuciyata tanamun zafi a yanda nakesan hafsat lallai na qudurta araina idan har ban sameta ba to kuwa bazan taba bari ta mori wata rayuwa da wani namiji ba,a wannan karon kuwa naga bazan iya kashe abokina ba kuma asirin yaqi cinsu shine nayi amfani da damar kwanciyar ta asibiti na aikata hakan,amma wlhy nayi nadama musamman rashi aminina na sosai sosai" shiru aka danyi kan mutane su fara mamakin dan wannan guntun laifin ze saka tsabar rashin imani ka kashe mace har lahira,hukuncin daya dace dashi aka yanka mai aka tarwatse karar aka kuma gargadi muhammad akan furucinsa daya janyo masa cin zarafi.......
*Washe gari*
Tsaf J.A ya shirya yaje gidan su hafsat a parlor akai masa masauki,sannan akaje kiran hafsat,jiki a mace ta sakko yana ganin ta ya miqe tsaye yazo suna fuskantar juna yace
"Bakin rijiya poor barrister,the youngest one,nazone in sanar miki ki gayawa iyayen ki one week kawai na saka d'aurin auren mu,lokaci yakusa zuwa dazaki san waye muhammad,menene kuma matsayin wanda ya tozartar dashi yakuma bata masa suna a idan duniya" wasu miyau ta hadiya masu dacin gaske ta runtse idonta sosai ta bude su a hankali sannan tace
"Kayi hakuri muhammad" bece komai ba ya miko mata waya kirar iphone 6 yace zan miki waya,idan buqatar hakan ya taso,yana gama fadar hakan ya juya a nan ta durqushe ta saka kuka me tsuma zuciya.....
Mom nuaiym
YOU ARE READING
BAKIN RIJIYA...ba Wurin Wasan Makaho Bane
RomanceMeya sanya arayuwa nayi rashin sa'an zuwana duniya gaba d'aya? Mesa zanso mutqaunar mutuwarsa akan Koda k'wayar idonsa ya sauke Akaina?? Mesa nayiwa Kaina wannan rashin adalcin?? Mesa wannan bakar zuciyar tawa bata dasamun San waninkaba yaa shammaz...