*💅BAKIN RIJIYA....ba wurin wasan makaho bane*💅
Love story 2018
Billy galadanchi
*HASKE WRITER'S ASSO.*(home of expert and perfect writers.)
Wattpadd@ 68billygaladanchi*Sadaukarwa gareki qawar alkhairi ummie Aisha*
20
Zirga zirga abba haris keyi tamkar me ynqurin naquda,sam ya kasa gayawa hafsat meke tafiya gata durqushe a gabansa amma se gumi yake had'awa,kar yarunyar nan tayi tunanin cewar san kai yake mata akan d'ansa,ganin yayi shiru beyi magana ba ya sanya takuma cewa"Abbana gani" jikinsa ne yayi mugun mutuwa jin takirasa da abbanta, yasani hafsat duk gatan da mahaifinta keyi mata gani takeyi tamkar shine ya haifeta kuma yafi santa,hannu ya sanya ya rage zufar data tsatsafo masa a goshi sannan yace,
"jeki ki dakko mayafinki kizo mu je wani wuri" dubanshi tayi haka kurun taji qirjinta na dokawa kuma kanta ya soma sara mata,jiki a mace ta miqe zuwa part nasu ta sako hijab a saman doguwan rigar atamfar dake jikinta tafito......*A parlor daddy*
Tunda hafsat ta ga kowa zaune har yaa shaam jikinta ya mata sanyi,gaba ki d'aya setaji wani iri,zama tayi yaukam ma akasan carpet ta gayar da kowa,kallonta daddy yayi yace
"Hafsat ina fatan kin san cewar mu iyayenki ne kuma mun isa mu sakaki komai a yanda muke so muke kuma ganin ya dace?" kallon su tayi d'aya bayan d'aya sannan ta sauke idanta akan yaa shaam dayake ta faman murmurshi a hankali hawayenda suka taru mata tun farko suka silalo,ta gyad'a mar kai alamar gamsuwa da jawabinsa sannan yaci gaba
"kuma kinsan cewar dukda muke iyaye a wurinku muma muna da iyayen dasuke sakamu abu adole koda bamaso se munyi shi?" nanma d'aga masa kai kurun tayi wannan lokacin kam tana kuka sosai,ganin yaa shaam na murmushi ta gano da babbar matsala,daddy yaci gaba
"Innah ce da kanta tayi mana umarni akan lallai mu d'aura aurenki da shammaz nanda wata d'aya me zuwa,kuma idan d'ayanmu ya sauya wannan maganar ko bayan ranta bata yafe masa ba" qirjinta ya dad'a dokawa fiye da da,ta d'ago cikeda razani ta kalleshi,idonta ya kada yayi jajir yanzu kam tama kasa kukan se quna da zuciyarta keyi,miqewa tayi ranta a b'ace ta qarewa kowa kallo sannan ta kalli Abba haris tace cikin wata murya me d'aci wacce basu santa da ita ba
"Abba na da gaske wai Innanku ne ta fad'a haka ba shiri bane wannan,na tabbatar kai kadaine zaka sanarmun zallar gaskiya" wasu yawu ya had'aya dak'yar masu d'acin gaske sannan yace dak'yar
"Inna ce ta bada umarnin nan jiya hafsat" hijabinta ta gyarawa zama sannan tace " To yayi" Ta juya da gudu zuwa waje batare da tasan me yake damunta ba ko ina zataje ba,daddy da Abba haris ne suka bi bayanta,da gudunta suma haka a haka tafito daga gate d'in gidan tana kawowa kuwa wata motar na dannowa da gudun fanfalaqi atake tayi mata ebar karan mahaukaciya.......dafe kai sukayi dukkansu bame abunyi haka aka cillata acikin drainage dake gefen titin,abbah haris na kuka kamar wani yaro yaje ya fada ya cirota,sam babu alamun numfashi a tattare ita,ta sume mamallakin motar ma daya kasance matashin saurayi dan gayu fitowa yayi ya taya abba haris daukarta suka saka ta mota suka fada atare yaja da karfin gaske sukayi gaba,anan suka bar abba a tsaya ya kasa koda motsi sabida rudu,dakyar ya iya komawa ciki ya kallesu yace
"Bana tunanin hafsat ,
Zata tashi,koda kuwa ta tashin bana tsammanin mata ingantacciyar rayuwa a yanda mota tayi mata wannan eban karan mahaukaciya ta cillata a gota" momy ce ta riga kowa miqewa jin kalamansa ta dage qirji "A ina wannan ya faru Alhj?" kallonta yayi da rinannun idanunsa yace"A kofar gida yanzu data fita da gudu,ina jiye mata idan ba ajali bane ya fitar da ita" zarewa momy tayi tayi waje da gudu shi kuma ya bita, dak'yar ya samu kanta tazo aka dunguma mota bayan sun kira abba ya sanar musu suna asibitin uduth wurin dr. Say.......
Say yana zaune a office abba haris ya shigo masaa birkice,dakyar ya iya sanar masa mota ta kad'e hafsa tana waje,ai banke abban yayi ya fito da gudu,Trauma suka wuce kai tsaye da ita,babban tashin hankalin say be wuce ganin pause nata yayi qasa ba sosai,sannan gashi bata numfashi daidai abu mafi ban tsoro shine jininta dakeyin qasa sosai amaimakon ya hau,yaukam kasa yin komai yayi ya janyewa wasu likitocin suyi,har yamma suna kanta sedai ba sa'a,Dr. Shuraim ne yafito ya sameshi har iffice shida abba haris da daddy,suna ganin ya shigo suka tashi tsaye,kai tsaye wurin sayyed ya nufa ya dafa kafad'arshi,hannun nashi say yafara kallo sannan ya kalleshi da kyau,yace kafin shuraim yace wani abun
"Dr. Shuraim karkace dani abunda nake tsammani?" kallonshi shuraim yayi cikeda tausaya wa,duk sunsan hafsat itace xe aura kuma yana matukar santa yace
"To zaka ja da ikon Allah ne sayyeed?" kafin wani yace wani abun say ya sulale wurin a sume....
Mom Nua'iym
YOU ARE READING
BAKIN RIJIYA...ba Wurin Wasan Makaho Bane
RomanceMeya sanya arayuwa nayi rashin sa'an zuwana duniya gaba d'aya? Mesa zanso mutqaunar mutuwarsa akan Koda k'wayar idonsa ya sauke Akaina?? Mesa nayiwa Kaina wannan rashin adalcin?? Mesa wannan bakar zuciyar tawa bata dasamun San waninkaba yaa shammaz...