*💅BAKIN RIJIYA....ba wurin wasan makaho bane*💅
Love story 2018
Billy galadanchi
*HASKE WRITER'S ASSO.*(home of expert and perfect writers.)
Wattpadd@ 68billygaladanchi*Sadaukarwa gareki qawar alkhairi ummie Aisha*
13
Yaukam rayuwar daddy tayi matuqar b'aci da wulakncin shaam akan hafsat,lallai wannan yaron yazo da salo na raini iri iri,banda haka tayaya ma agaban su kaikoma ba agabansuba zece wai baze auri hafsat ba haryana iqirarin be sota tana da lapiyaba se yanzu data zama nakashashiya,ba abunda zece dashi koya nuna masa zega iya gudun ruwanshi tare da jiran matakin da Haris ze dauka.......Hafsat zaune tanaso taci abuncin dake gabanta amma bata saka cokalin wurin daya kamata,har ranta takejin wani tuquqi,wannan ya sanya ta ajiye cokalin ta laluba ta gincira,duk wannan abun datakeyi khairri na kallonta tana hawayen tsananin tausayinta,zuwa tayi ta zauna kusa da ita ta kamo hannunta tace "Sister ya bakici abuncin da yawa ba kaddai harkin koshi?" Murmushin yake tayi tace " Na qoshi ne wlhy"
"Nasani baki koshiba hafsat,kawai sabida bakya saka spoon din inda ya dace ne,kiyi hakuri na baki kanki saba kuma inshaa Allah zaki warke ai haka doctor yace zakiji sauqi kinji" hawayen da dukkaninsu ke qoqarin tarewa ya silalo musu hafsat tace "Khairiyya haryaufa yaa shaam bezo ya duba niba,da gaske manufarshi kenan ya rabu dani har abada?" kukane ya kwace mata ta toshe bakinta,khairiyya tama rasa me zatace mata "kiyi hakuri hafsat,amma barin kira miki shi awaya" batace komai ba wannan ya sanya khairiyya taje waje tayi kiran shammaz akan dan Allah yazo hafsat ta damu da rashin zuwansa,beyi musu ba yace yana nan zuwa da dare.....
A parlor zaune hafsat take a kujera me mazaunin mutum biyu,se shaam dake zaune a me mazaunin mutum d'aya,dak'yar ya iya bud'e bakinshi yace
"Hafsat ya jikinki"
"Naji sauqi Alhamdulillah"
"Akace kina nemana?" sadda kanta tayi qasa "Yaya dama zancen komawa nane gidanka,dan Allah kayi hakuri abubuwan dasuka faru wlhy ko mutuwan khaleefa ba laifina bane lokacin sa ne yayi" murmushi yayi yace
"Haba hafsat,kewai bakya fahimtar abubuwane? Ban soki nakuma zauna dakeba sanda kike mutum me lapiya,se yanzu dakika zama nakashashiya,na dade da fad'a miki sam bakin rijiya ba wurin wasan makaho bane saura miki yaushe ki gama iddah,idan ma banyi kuskure ba aiba idda a kanki,saboda haka kiyi hakuri ki kalli dahir ni bazan taba dawo dake gidana ba,ina miki ao irinna yan uwantaka matsayinki na kanwata amma bawai zancen aure ba" dukda bata gani amma hakan be hanata duban inda take jiyo sautin muryanshiba tace tana kuka
"Yanzu yaa shaam idan kai dakake dan uwana ka gujeni akan inada matsala waye aduniya ze aureni? Kaine sanadin lalacewar rayuwata,ka b'atamun duk wani abu danake taqama dashi,bani ga karatuna babu labarin future na,banida d'a ko d'aya a duniya da wanne kakeso inji?" murmushi ya kuma yi
"Hafsat wlhy kinji na rantse bazan tab'a iya zaman aure dakeba,ke ni idan ma kinamun wannan maganar haushi kike bani wlhy,kimun magana kanki tsaye indai zaki bani matsayin yayanki to zakiga gata na haduwa,amma zancen aurennan yarabu kenan har abada,idn bakida wani abun fada zan wuce"......sanda ta d'anyi shiru sannan tace
" Nayi dana sanin saninka arayuwa,nayi danasanin kasancewarka d'an uwa na jini agareni,nayi danasanin aurenka,nakuma yi danasanin aurenka,nayi danasanin kasantuwar zuciyata tawa ina ma ace canje aka mun bisa kuskure dana roqa a sauyamun da tawan sabida na kaucewa wannan wahalalliyar soyayyar,daga rana me kama da yau inaso ka nemo biro da takarda kakuma rubuta ka ajiye cewar ni hafsat nakashashiya nafita arayuwarka na har abada,na yanke duk wata alaqa dake tsakanina dakai, harta zamanka d'an uwana,ko a hanya ka ganni karka nuna sanayya tsakanina dake,bana buqatarka arayuwata ka sani ayau d'innan wlhy na tsaneka tsana mafi munin tunani,bazan hana zuciyana haukanta na sanka ba amma zan iya haramtawa rayuwata koda gaisawa dakai koda hakan yana nufin zan rasa ilahirin rayuwata kuwa tunda ai ka gama nak'asani meya ragemun,nice nan yaa shaam zan tabbatar maka da cewar bakin rijiya sam ba wurin wasan makaho bane" Yad'anyi mintuna biyu bece komai ba secan ya nisa yace "Hafsat me kuma ya kawo maganar tsana anan nifa d'an uwankine" miqewa tayi ta soma doddogara sandarta tana neman hanyar waje,kasancrwar tasan tsarin gida. Yasanya tayi amfani da basirar ta ta nufi cikin gidan zuwa dakinsu.....duk wannan zantutuukan nasu akan kunnen abba haris tausayinta me tsananin gaske ya rufe shi,daganan ya qudiri niyyar nemawa hafsat lapiya kota halin qaqa koda kuwa dukkanin abinda ya mallaka ze qare.....
YOU ARE READING
BAKIN RIJIYA...ba Wurin Wasan Makaho Bane
RomanceMeya sanya arayuwa nayi rashin sa'an zuwana duniya gaba d'aya? Mesa zanso mutqaunar mutuwarsa akan Koda k'wayar idonsa ya sauke Akaina?? Mesa nayiwa Kaina wannan rashin adalcin?? Mesa wannan bakar zuciyar tawa bata dasamun San waninkaba yaa shammaz...