page 28

2.5K 194 6
                                    

*💅BAKIN RIJIYA....ba wurin wasan makaho bane*💅

   Love story 2018

Billy galadanchi

*HASKE WRITER'S ASSO.*(home of expert and perfect writers.)
 
Wattpadd@ 68billygaladanchi

*Sadaukarwa gareki qawar alkhairi ummie Aisha*

         28

A babban parlor na gidan hafsat ta had'u da muh'd kallanta yayi sosai ganin ranta duk a b'ace

"Kaddai harkun gama gaisawar?" kallansa itama tayi "Ta dai gama wulakanta ni,Allah bazan qara zuwa wannan part d'in ba" tana gama fadar haka ta banki kofar tayi gaba abunta,binta yayi da kallo da kallo harta kurewa ganinsa,a ranshi yace lallai wannan yarinyar dama wai haka takeda fitina?....zuwa yayi kai tsaye d'akin da zainab take,Kallo daya yayiwa ma aikatan suka saketa suka watse,mutuqe fuskarnan yayi

"Me kikawa hafsat ne?" kallon raini ta masa

"Wacece hafsat kuma?" batare daya ce kala ba ya juya da nufin fita,ya gano raini zata kawo masa "Idan wannan shegiyar fitsararriyar yarinyar kakemun wannan kallon gwara ma ka dena,sanin kanka ne nan d'in gidanane kuma kowa dole ya girmama ni sabida nice babba" cak ya tsaya jin kalamanta sannan a hankali ya juyo ya kalleta

"Gidan tane itama,ai auren mu aka daura bawai yar aiki na kawo miki ba,bakuma wai zama dadiro mukeyi da itaba,sannan da kike zancen girma aini ne me gidan idan baki girmama niba babu wanda ze girma maki wlhy,zaman lafiya nakeso kuyi da juna bawai shirmen kishi ba" miqewa tayi tazo har inda yake

"J.A ni kake kallo kace dani wai kishi? Akanwa zanyi kishin kai? Danake sanka kokuma da aka gaya maka zaman jin dadi nake a gidan naka? Kaga wlhy idan ma mafarki kake ka farka,bazan tab'a kishin kaba sabida kasani sarai ba so araina" murmushi yayi dukda yaji zafin kalamanta sannan yace
"Kamar yanda kikasan ni d'inma hakan take a wurina,nakuma auro matar so idan kin isa kem ki auro mujin so" Kallon mamaki ta masa sabida be taba cewa da ita baya santa ba se yau,qirjin tane ya doka lokaci d'aya taji ranta ya b'aci,kan tasamu bakin magana kuwa yayi gaba abinshi.... Koda ya dawo b'angaren hafsa kuwa a walk way ya sameta tanasham coffee,kallon shi tayi sosai

"Mezaka ci dinner inaso zanyi girki?" kallonta yayi sosai

"Bana cin abinda keda nauyi,so u think of something light"

"Same here" tafad'a had'e da miqewa,sanda zuka parlor ya kalleta "Zan fita akwai wani abu?" matsowa tayi sosai kusa dashi ta hada jikinta da nasa,a kumatu tayi tsalle kadan ta manna masa kiss tace tana murmurshi cikeda rashin damuwa da abinda tayi

"Ina maka fatan alkhairi,Allah ya sanya aje lafiya kuma a dawo lafiya" tana kaiwa nan ta juya abunta zuwa kitchn, yafi 3 mnts tsaye yana tunanin hafsat,tunda yake zeezee bata tab'a gwada yi masa adu'a ba akan wai ze fita ko wani abu daya shafi nasarar sa,wani sanyi yaji yana ratsa shi tamkar ruwan sanyi ayayin daka kwaso rana kake tsananin jin qishirwa, juyawa yayi ya fita amma sam bayan ya fitan seya kasa zama waje,duk motsin dazeyi kuwa zuciyar sa azalzalar sa takeyi akan ya dawo gida haka nan.....

    Shaam kuwa da maryam tun daren jiya suka angwance,ya samu nutsuwa me tsananin yawa a tattare da aurenta,yarinya ga tsananin riqon addini,domin kuwa ganin lokacin sallan asuba yayi shaam na bacci koda ta tasheshi sanda tayita mai wa'azi akan hakan,haleema kuwa batada labarin miyan da ake sha a niger da mujinta lolx.....

    Waffles sandwich ta musu da pizza ,se creamy la bees,sosai gidan ke tashin kanshi,wanka ta tsala tayi sallan ta na isha,daci ado cikin wasu riga da wando qanana pink and white masu matukar kyau,zokaga yanda heeps nata suka kwanta sosai gwanin sha'awa,kunce gashinta tayi ta taje shi zuwa baya yasha gyara se sheqi yakeyi haka ta zuboshi tamkar wata india,light makeup tayi tana fitowa sukaci karo a parlor,sanda ya lumshe ido ganinta kawai yaja numfashi, kamshin dayaji gidan nayi kawai ya wadatar balantana qamshin dayaji na ratsashi sanda ta fito, da sauri taje ta rungumeshi sosai ta kwantar da kanta  a saman faffad'an qirjinsa ta furta a hankali

"Sannu da zuwa yaa muhammad,ina fatan ka dawo lafiya" qamshin sumar kanta ne ya ebe shi besan sanda ya daura hannunsa yashafi gashin kan nata ba,yama kasa magana dama gashi ba ma'aboci son magana ba se kace ba lauya ba,dagowa da kanta tayi jin tayi lamo itama tanaso ta manta da muhammad ne fa,a shagwab'e tace

"Yaa muhammad sekuma ka barni ni kadai,tun yamma fa ka fita" murmushi ya sakar mata me sanyi yama rasa me zece seya tsinci kansa da furta mata "Kiyi hakuri hafsat,wani abune ya tsaidani nima banso hakan ba,amma na kawo miki chocolate" wara ido tayi "Allah yaa muhammad? Thank you so much" ta qara rungumeshi sannan ta sakeshi ta juya,kallon duwawunta yake harta shige da jakar hannunsa da leda data karba,shi yaushe ma yataba samun arziqin a wani riqe masa jaka? Hmm lallai wannan auren yana ganin shine ake kira auren gaske kuwa.....A bed room nashi ma koda yashiga kamshin turaren wutan da aka saka dana freshner gaba daya ya banbanta,be taba kamshin daya kwanta masa araiba irin wannan,kallonshi tayi sosai,zuciyarta na dokawa sabida abinda huda tace tayi ya mata nauyi,haka ta daure sabida yanzu kam ta shirya yin wining wannan,taje kusa dashi botiran shirt nashi ta soma b'alle masa sororo yayi kuwa ita kam se murmushi take "Wanka ne ya dace dakai,a baho na had'a maka ruwan wanka da turaren wanka me tsananin kamshi,bayan kayi wanka se dinner kuma ko?" kallonshi tayi dasanjin amsar tambayarsa "murmushi ya sakar mata ya gyad'a kai  alamar e,haka ta cire masa har wandon cikeda dauriya,ya dawo iya boxers de singlet ne a jikinshi, towel ta miqa masa tace "To zan jira kafito semu tafi tare" harta juya ya riqo hannunta  yace "Sauran kayan fa hafsat? Su bazaki tayani ragewa ba?" murmushi tayi tace bayan ta kawar da kanta gefe  d'aya "Yaa muhammad wannan ma aiya isa,dan Allah ka barni haka?" juyawa yayi zuwa toilet ba tare dayayi magana sarai ya gano nauyin sa takeji,wannan auren yana ganin shine mutu ka raba,shibesan ana wa maza gata ba har haka ai,a gurguje yayi wankan yana mamakin wannan kamshin da ruwan wankan keyi,haka yafito dagashi se towel halittarsa ta faffadan kirji ta kala,gaba daya jikinta ya mace sanda ta lumshe ido tana mafarkin ganin kanta a cikin wannan kirjin nasa,haka ya janyo man shafawa ze shafa,ita ta karb'i karamun towel ta goge masa jikinshi sannan ta shafa masa mai d'in,kayan baccin data ciro masa ta bashi ya karba yana murmushin da sam,yakasa daukewa a fuskarsa,da sauri ta bashi wuri tayi waje,a parlor ya taddata koda yaga pizza kallonta yayi

"Daga ina kikayi ordering pizza,na season 7n kawai nakeci" kallonshi tayi ordering kuma sekace banida kayan had'in pizza d'in? Ni na hadashi ba dadewa fa" kallon mamaki ya mata "A ina kika koyi girki?" ya wurgo mata tambayar "A wurin mama na,kuma a india naje ctring classes yafi a irga,wasu zubin idan muna hutu ban dawo ba senayi joining,i so much like cooking ai" jinjina kanshi yayi yana me jin dadin yanda yake cin girkin matar daya ajiye a matsayin tashi,tunda yake so daya tak zainab ta dafa masa spag ita dinma san beci ba sabida ba taste kowa abincin cook yake ci,a parlor suka zauna kallo bayan sin ida,matashin kai tayi da cinyarsa anan bacci ya dauketa, se wuraren 11 ya dagata cak zuwa bed room nashi, sosai ya rungumeta ya kwanta shima.......

Haleemah kuwa kwana bakwai da auren shaam ta dira niger,kuma a gidansu tafara sauka anan takejin mugin labari,aikam qungiya guda sukayi zuwa gidan amarya domin ciwo kan ubanta danye lolxxxz.

    Yau satin hafsa daya kenan a gidan muhammad sukan ci atare susha atare kuma a haka zasu kwana wuri daya,amma fa sam ba wani mu'amalar aure dake shiga tsakaninsu,sedai kullim kwanan duniya tana qara samun wani babban matsayi a zuciyar muhammad har yakeji baya iya daukar a wanni biyar batre daya ganta ba,yauta shirya zataje gidan shaam da gidan Abba haris,izini yamata akan ta karbo key na motarsa Avensus wurin zeezee sabida duka keys suna bangarenta taje da kanta tunda tace tare dasu momy zasuje gidan shaam din harsu khairii ma,koda ta aika wai bazata badaba,kai tsaye taje da kanta ,a zaune ta tadda ana matsa mata kafafu ta kalle ta sama da kasa tace
."Zainab key na Avensus fara zaki bani zanje unguwa"

"shi me gidan naki be sanar miki cewar ni ce nakeda ikon komai da kowa ba agidannan,kice hajiya kuma ki durqusa ki rokeni key sannan zan baki" wata dariya hafsat tayi ta juya abinta zuwa waje,kallon driver na gidan tayi tace dashi

"A waccen benz da key ke hannunka akwai mai ne?" kallonta yayi ya gyada kai,miqa masa hannu tayi kawai ta karba tayi gaba,tana tashin motar ta saisaita kanta sega zee tafito tana masifa ko kallonta batayi ba,tazo tasha gabanta aikam hafsa tayi cikin ta seda ta fadi sannan ta kauce tayi gaba abunta.......

Topha koya zata kaya,su haleema sunyi qungiyar zuwa gidan shaam gakuma su hafsat zasuje koya zata kaya ohoo

Vote and comment

BAKIN RIJIYA...ba Wurin Wasan Makaho BaneWhere stories live. Discover now